← Book details Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 88

Sashe 51

Ameenatouh Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Same lodge siddeeq ya sauka Kuma daren ya gama binciken komai gameda rayuwar AM jden da ranar datai graduation harma da duka iyalan gidan Omar din sedai Kuma abinda Bai saniba shine Sabon babyn da familyn suke dashi wanda tsaban bincike saida ya samo hotonsa inda yake da Omar jden din su kadai Suna dariya a gurin wasan Yara wanda duka kaf jdens Babu wanda ya taba yadawa ko Saka hoton Arfat a ko Ina sbd tsaro da tsananin son da kakansa yake masa ya hana a ringa sakin hotonsa Dan hakanne ma Babu wanda yasan yanada jikanda 'yarsa ta Haifa masa.

Yana turawa Jamaal komai ya tashi Dan wanka da Shirin bacci sbd dare ne sosai.

A nata bangaren kuwa wanka tayi ta Saka short kaya marasa nauyi bayan tayi sallah,
Ta zauna taci abincin da aka kawo Mata tareda hot milk me kyau tukuna ta zauna tafara kiran su Babbah ta jima tana magana dasu kafin tayi da Arfat Yana tambayar uncle Buddy dinsa tukuna sukai sallama.

Dad dinta ta kira har lokacin Suna tareda Jamaal Suna magana wanda a Cikin zancen Jamaal ya tabbtarda da gasken Bata Tina komai ba ta manta duk rayuwar da suka gudanar a asibiti harma shaquwanta dashi da Ashley dinta hakama da gasken gasken su Dad Omar basusan da aurensa akanta,basusan da auren daya daura da ita ba kenan harshi har su Babbah,

Duk halinda suka shiga na bayan rabuwarsu da komai dad ya sanar masa Banda Abu daya shine an mata fyade ta haihu harma tanada baby sbd bazai taba fadawa kowa wannan rigar mutuncin nasa Dana yarsa da aka yaga ba da Kuma yanda zaa Kalli Arfat dinsu Dan haka alkwarinsa ne bazai taba fadawa kowa ba harda Jamaal din kuwa duk da Babu abinda yake boye masa Amma wannan dai zai zama sirrin familynsu ne da babu me sani inshallah.

Jamaal Bai da dogon kuzari ko dadin zuciya Sam Amma bazaka taba Gani ba ko gane hakan musamman gaban Dad din dayake zaune a natse Cikin kamewansa da Dad din ya Sansa da ita harma da wadda ta qaru Suna magana yai Nisa sosai a tinanin a wane matsayin yanzu zai bayyanarwa da Dad aurensa dayake kanta da yanda ita kanta zata Kalli auren sbd bayajin zai tilasta kowa karban wannan auren kaman yanda dole ne da rashin mafita ne a lokacin ya sakasa aurenta din,

A yanda ya sani Haroon takeso shi kadaine a ranta Kuma shi kadaine abinda Bata manta ba a hauka hakama a lafiya,
A Haroon take kallansa, a Haroon ta yadda dashi fiyeda kowa, a Haroon tai matsa tsananin so duk a asibiti Dan haka a yanzu datake Cikin cikakkiyar hankalinta bazai taba sake amsa sunan Dan uwansa ba sai dai ya amsa sunansa Jamaal a matsayin mijin da igiyoyin auren dayake rataye akanta suke hannunsa yakeda cikakkiyar ikonsu Amma a yanzu zai gama bincikensa akanta kafin yagama karantar yanayin rayuwanta sbd baisan komai gameda asalin waye ita din ba kaman yanda itama kwata kwata batasan waye shi din ba Dan haka bazaiyi gaggawa sbd Baya buqatan hayaniya da tashin hankali yanzu zai bawa komai time Dan haka ya dakatar da Siddeeq daga sanar da ita komai ya kula da komai nata kawai.

Kiranta Yana shigowa wayar Dad dinta Dake gefensa ajiye Idanuwansa akan sunanta ya sauka kallo daya yayiwa sunan ya dauke Idanuwansa Yana daukan cup din gabansa na ruwan dumi yakai bakinsa yasha Yana Dan sauke numfashi yanajin sautin muryanta na sauka cikin kunnuwansa.

*****Washe gari 9 ta fito a shirye Cikin skinny jeans da Riga da jacket mota ta dauketa zuwa inda zasuyi program din.

Basu dawo ba acan ta wuni zai kusan yamma a gajiye take Dan haka koina Bata fita ba wanka da sallah tayi taci abinci sama sama tayi waya da kowa ta kwanta bacci yayi gaba da ita.

Hakama washe gari ta faru sbd program ne na Wani tsadaddiyar business class da dad di ya sakata wanda ya hada Yayan Manya harma da manyan wanda kanayinsa ka zama cikakken dan Business da zai iya hulda da kowanne irin yare ko qasa ko mutane.

1 month class ne Dan haka ta zama busy sosai ga uban kewan Arfat da iyayenta datake dawainiya da ita kaman me Hafiz da Dad sunzo sun dubata Amma Sam baa kawo Mata sanyin idaniyarta ba ta gansa Shima acan rigima Babu kalar wanda bayayi akan rashin mommnsa Dan har Ciwo yayi Amma hakanan akaita kulawa dashi kaman kowa zai cire ciwon daga jikinta ya dawo dashi nasa har aka samu ya warke.

Kaman yanda Dan cika burin Dad dinta na zama cikakkiyar independent woman Mai lafiyayyan ilimi da sanin business ya sakata dagewa a karatunta data gama ba ji ba Gani hakama wannan ta Maida hankali sosai takai Saida ta Dena communicating da kowa sbd cimma manufa har suka gama sai gashi Cikin Tarin turawan qasashe daban daban itace ta zama gwarzuwa Akai programs din da zaayi na kammalawansu aka gama ta dawo da mamakin wanda Idanuwanta suka ganar mata a gurin program din Amma Kuma tasan hakan bamai taba yiyuwa bane ganin Haroon gareta Amma Kuma tinawa da kamannin Jamaal ya sakata Tinanin yanzu akwai  wanda yake da komai n kamannin Haroon dinta.

A daren a matiqar gajiye take Dan haka hutawa tayi tsawon kwana biyu kafin tayi Shirin tafiya gida ta Siya ticket din France Kai tsaye.

Da daddare jirginta zai tashi Dan haka  ta fita ta Dan yiwa Arfat dinta shopping sama sama sbd Babu m abinda yake buqata sbd Babu ranar da Kila Hafiz baya Siya masa abubuwa harda na shirme.

Kayan Yara ta Siya sosai tana dawowa sallah tayi ta sake wanka ta shirya tana gamawa Ariana na isowa lodge din da mota ta dauketa sai airport.

Ko awa daya bataiba a airport jirginta ya tashi tabar Madrid.

Ko data isa France safiya tayi Hafiz ne yazo daukanta tareda Arfat wanda Yana hango mommansa da Wani irin gudun gaske ya kwace daga Hafiz ya nufeta yana ambatar sunanta farin cikinsa Mai tsananin gaske Yana bayyanuwa sbd Bai taba dadewa haka batareda mommnsa ba.

Itama ware hannuwanta tayi Cikin tsananin farin Cikin da take Idanuwanta suka ciko da hawaye tana cewa

"My blue eyed champ,mommas love, honey I missed you like crazy,ohh my love......."

Daukansa tayi tayi sama dashi duk da nauyinsa tana dariya Shima dariyan yakeyi.

Hafiz daya iso gurinsu Cikin farin Cikin ganinta Shima barka da sauka yayi mata Yana kallan yar ramar datai Amma ta qara haske sosai yace

"Yau akwai turancin France a bakin babbah da Dad jden idan yaga yar budurwansa ta rame haka"

Dariya tayi Suna yin gaba tana cewa

"Allah sarki babbahna duk kun rikita masa yar budurwansa"

Dariya yayi Shima Suna isa mota ya Bude aka Saka komai nata ya Bude mata ta shige ya karbi Arfat dinsa ya Bude masa baya ya sakasa tareda Saka masa seatbelt ya rufe kofan kafin ya zagaya ya shiga lafiyayyan motar ya tayar suka bar airport din aguje.

Idan akwai abinda yafi hawan jini to siddeeq Yana cikinsa sbd mutuwan tsaye yayi na ganin babyn a tsakiyar Hafiz da AM Kuma Yana kiranta mommah idan kunnuwansa sunji masa daidai kenan.

Innalillahi wainna ilaihi rajiun""

Wannan babyn waye ne ya haifesa a kaf familyn jden shine abinda yake tsananin son sani kafin isawar da Jamaal wannan sakon da zai iya tarwatse komai,
Tukuna ma Ina aka samu jinin bature a fmlyn??
Kodai Cikin familyn asalin jdens dinne Omar jden ya dauko...

Numfashi ya sauke daqyar dole Yana buqatan sanin komai kafin barinsu AM din kasar kaman yanda JAMAAL yafa masa.

Su kuwa Kai tsaye gida suka nufa Suna isa Aunt Didi ce tafara farin Cikin ganinta sbd zata fita ne tana bakin motarta suka shigo.

Rungumeta tayi tana mata sannu da zuwa itama Cikin farin Cikin ta rungumeta tana Dan bayyanarda shagwabanta.

Wata lafiyayyan Ferrari ta Gani a harabar gidan Amma Bata damu da tambayar ba sbd tinanin ko Dad dinta ne ya siyo sabuwan motan kokuma ta Hafiz ce.

Ciki sukayo Arfat har lokacin Yana maqale da ita a hannunta babbah bayanan shi da dadah Dan haka Kai tsaye palon Dad dinta ta nufa da Arfat a hannunta Hafiz na gefenta suka shigo palon.

Dad dagowa yayi fuskansa cikeda farin Ciki ya kalleta Yana ware mata hannuwansa ta taho har Arfat din suka shige jininsa sai alokacin ta lura d JAMAAL SEELAH dayake zaune tareda Dad din batareda y dago ya kalletaba waya yake amsawa a Cikin wata irin nutsuwa da kamewan data sakata dauke nata Idanuwan daga kansa
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[29/05, 10:08 pm] Zainabdawaki: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
107

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************
Da daddare gurin Dad dinta da Mum Nur tayi dinner tareda su sbd haka take rabawa Dad dinta da su babbah kanta kowa tana tsananin sonsa tana kokarin basa time dinta da kulawanta yanda ya kamata sbd dukkaninsu ta rasa wanda ya fi sonta tsakanin Dad dinta da babbah.
Chapter 51 · 0% Book details