Sashe 8
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adamsy yana ta ringing amma bai aga dan haka ta ce kila bai kusa ne anjima ka an zata gwada kiransa, dan kada ya zo baisan da zancen cewa an fasa aurin auren ba yazo da jama'a alhalin ba'a fa a masa ba, dan haka ta ajiye abin duniya duk ya ishe ta. Sautin Sallama ta ji a cikin kunnenta. "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki salam" Hajiya Saratu ce ta shigo wato awar Mum ce ita ganin yadda idanun Mun suka kumbura suka yi jazir yasa ta cikin tashin hankali ta dafa kafa arta tare da cewa "Lafiya kuwa me yake damunki haka? Yau ranar bikin 'yarmu ranat farin ciki ne a gare mu ." Girgiza kai tayi tare da cewa "Nikan wannan ba farar rana bace a gare ni, ba in rana ce ranar da bazan ta a mancewa da ita ba a tar ihin rayuwa ta." Idanun Hajiya Saratu ya sauka akan wani jaka na kwali mai auke da hoton Amarya da ango wato Adamsy da Hauwa'u. Zaro ido Hajiya Saratu tayi cike da mamaki ta ce, "Kada dai a ce Adamsy ne mijin da Hauwa'u zata aura?" Cikin mamaki ta ce, "Eh Admsy sunansa kin san shi ne?" Kai kawai Hajiya Saratu ke girgizar tare da cewa "Babu alkhairi a tattare da Adamsy mata guda biyar yake aure sannan kiga wata masifa ta samu kowace a cikinsu ." Cikin tashin hankali Mum ta ce, "Dan Allah kiyi mani bayani nasan inda zancenki ya dosa ba." "Bari kiji duk matar da ta aure Adamsy sai wata nakasar ta same ta, a takaice dai wallahi mata biyar kenan idan aka ha a da 'yarki shida kenan, ciki. Matan nan biyar wata ta mutu wata ta haukace wata wata ta makance ta zama makauniya ta cikin su biyar ba wacce ta tayi rayuwa salin alin." ora hannu aka Mum tayi tare cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Adamsy ka cuce ni baka sanar da ni cewa kana da matsala ba gashi yanzu ka haukata mani yarinya." Da mamaki Hajiya Saratu ta ce, "Kina nufin yanzu har 'yar ta mu ta haukace ?" Kai ta jinjina mata tare da cewa warai kuwa" Adamsy ne ya kira lambar Mum dan kamar ba zata aga ba sai kuma ta canza shawara ta dauka, jin muryarsa tayi yana cewa "Assalamu alaikum " "Wa'alaika salam,kana ina ne Adamsy?" "Ina gida Mum." "Kazo yanzu ina son ganinka" Bata tsaya jiran ko ne zai ce ta katse kiran wayar, shima yayi mamakin kiran haka ya mi e jiki a mace ya nufi ofar fita dai-,dai lokacin da Amina ta fito daga akinta, ta kalle shi tare da cewa "Ango har ka fito ne?" Ba tare da ya kalle ta na ya ce, "Mahaifiyar Amarya ce tayi mani kiran gaggawa." Jim tayi tare da cewa "Allah ya sa Lafiya." Daga nan ya amsa da Ameen ya fice. Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, inda ya bu aya daga cikinsa sannan ya shiga ya tayar, horn yayi mai gadin gidan ya bu e masa gate ya fice. Kai tsaye ya dauki hanyar gidansu Hauwa'u. A falo ya same su su dinga da wa anda ya sani da wa anda bai sani ba, Sallama yayi wanda hakan dai-dai da arasowar Mum a falo, bayan sun bashi izinin shigowa ne ya kalle su tare da dur usawa asa yayi ya gaishe su, ba wacce ta amsa a cikinsu. Tunani ya shiga yi kodai ya ara gaishe su ne sai ya ji muryar Mum tama cewa "Shikenan Adamsy dama abinda kake so kenan hankalinka ya kwanta burinka ya cika, wai me yasa kake wahalar da rayuwar bayin Allah? Me suka yi maka? Tukunna ma kai wane irin mutum ne haka da duk wacce ta aure ka sai masifa ya fa a mata? Wane irin mutum ne kai mai ba addara har sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari meye ribarka akan hakan kayi aya biyu uku kaga yadda rayuwarsu suka kare me yasa kai ba zaka ha ura ba saboda sin zuciyarka shine ka cigaba da auren wasu kana dad'a jefa rayiwasu cikin gararin rayuwa." Wata mata daga cikin mata ta ce, "Waya sani ko yana cikin ungiyar nan ta matsafa ne yasa..." Kafin ta kai arshen zancenta ne ta ji kusryarsa ya ce "A'uzubillahi minashshai anir rajim." Nan dai suka cigaba da fa a masa maganganu marasa da i, anan yake sanin cewa Hauwa'u ta haukace tuburan. Jin muryar Mum yayi tana cewa "Abinda kayi muna sai Allah ya isar mana, sai kaga karshenka mugu mai ba ar aniyar, kuma bari ka ji koda ace yarinya ta ta warke ta dawo dai-dai to wallahi ba kai ba ita Allah ya tsare sauran 'yan matan daga sharrin ka." Nuna masa hanyar fita tayi tare da cewa "Tashi ka fita ka bar mana gida bana bu atar sake gani. Ko mai kama da kaine ne a rayuwa ta, zanyi jinyar 'yata har Allah ya bata lafiya, idan kuma itama ta rasu kamar yadda na ji ance awarta Fauziyya ta rasu bayan fasa aurenku da kwana aya to Allah ya ji ansu amma Alhakin mutuwarsu ya rataya a wuyanka. Tashi yayi ya nufi hanyar fita idansa duk sun janza launi zuwa ja, wato bayan fasa aurensu da kwana aya, gashi yanzu Hauwa'u dake nuna masa tsamin so ta haukace banda sauran mata hu u da yayi yunkurin aure da wadda ya aura? Me ke faruwa da rayuwa ta ne? Tambayar da yake yiwa kansa kenan. Motarsa ya shiga ya tayar tare da aukar hanyar komawa gida. Yana driving yana kuka yana magana shi ka "Me ke faruwa da ni ne? Anyi na biyar mata biyar kenan Fauziyya kin rasu? Allah Sarki Hauwa'u kin nuna mani auna tun bana kula ki ina share ki bakiyi zuciya kin rabu da ni ba haka kika cigaba da hakuri har ranar da na amshi tayin soyayyarki, gashi yanzu ke ce a hauka ta dalilina?." Maganar mahaifiyar Hauwa'u ya tuna inda take cewa. "Sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari?meye ribarka akan hakan?" Kuka kawai yake yi yayi nisa cikin duniyar tunani abunda dake faruwa a rayuwarsa, yana cikin driving hankalinsa ya gushe bai ankare ba sai yaji motarsa ta bada sautin garar... *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman karin bayani* 09065327995 Love you oll Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM* Page1 Kuka wai yake yi,yayi nisa cikin duniyar tunani abinda ke faruwa a rayuwarsa, yana cikin driving hankalinsa ya gushe bai ankare ba sai ya ji motarsa ta bada sautin garar... Ashe ya daki motar da ke gabansa ne ba tare da saninsa ba, sai a lokacin ya dawo daga hayyacinsa dade goshinsa yayi tare da fa "Ya Salam!" Mai motar da ya daka ne ya fito cikin fa a da tijara ya nufi motar Adamsy yana cewa. "Wannan wane irin banzar tu i kake yi ne ko ka san irin arnar da kayi mani? To wallahi sai ka biya ni yadda ka aki motata har da fasa mani Danja ka..." Kasa arasa maganar yayi sakamakon ku in da Adamsy ya fito da su yana mi a masa, bandir in dubu ari ne guda biyu wato dubu ari biyu kenan, amsa yayi tare da cewa. "Yanzu na ji magana irinki ake so da ko kunyi arna zaku biya har da roba bawai masu bada hakuri ba." Horn da ake danna masu daga baya ne yasa Adamsy yayi masa nuni da hannunsa wato ya tafi ya ja motarsa sun tare na bayansu. Tafiya yayi yana cewa "Allah sarki ahe ma kurma ne shi baya magana." Shi duk a tunaninsa Admsy baya magana ne, tunda koda yayi taasifarsa bai yi magana ba ku i ya bashi, yanzu kuma gashi yayi masa nuni da hannu. Bayan ya shiga motarsa ya ja ne sai sai Adamsy yana nasa ya cigaba da tafiya. Kai tsaye gidan Ummansa ya nufa, inda ya samu jama'a sun an taru ba laifi, dan ya ga aikun mutane a harabar gidan. Ajiyar zuciya ya sauke tare da maganar zuci yana cewa "Allah sarki Ummana baki gajiya da tara jama'a a gidan nan, ko wane lokaci sai kinyi taro kuma auren baya yiwuwa, idan wani ya tashi kuma sai kinyi sake yi to anzo na karshe insha Allahu." Yana fitowa daga motarsa kai tsaye ya nufi wata aramar ofa wanda ada kafin yayi aure nan ne akinsa na samartaka, kuma Ummansa na sanya mai aikinta tana gyara akin bata bari yayi ura, yana shiga ya maida kofar ya rufe kai tsaye ya nufi bedroom insa ya fa a akan akan gadon tare da kifa cikinsa idanunsa duk sun riki e zuwa ja Kuka kawai yake kamar aramin yaro yana tuna abubuwan da suka faru a rayuwarsa, ga maganar Mum in Hauwa'u inda take cewa. "Mutum ne kai mai addara har sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari meye ribarka akan hakan kayi aya biyu uku..." Kuka ne ya ci arfinsa a hankali ya ke furta kalaman Mum in Hauwa'u, haka ya dinga kuka tamkar wani aramin yaro. Turo afar aka yi aka shigo Ummansa ce tsaye tana kallonsa bata san kuka yake ba sai lokacin da ta ji sautin kulansa cikin hanzari ta arasa jikin gadon tare da furta cewa "Babana kana lafiya kuwa? Me ya same ka ne la kwanta kake ta kuka haka tamkar wani aramin yaro?" "Haba na sanka fa da jarumtaka ban sanka da kuka ba kai jarumine?" Cikin kuka ya ce, "Umma Fauziyya ta rasu washe garin ranar da za's aura aurenku aka fasa, sannan ga shi Hauwa'u ta haukace ya in nan Ummanta ta kira ni take sanar da ni, Umma wai me ke faruwa ne da rayuwata, Umma wai ashe ba addara ce da ni?" Duk matar da na so