← Book details Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MAGANA A KEYI TA GLOIN SKIN (GYARAN JIKI SHINE MECE) DUK MACEN DABATA GYARA TO MUNA MATACE BAKAI AKIRATA MACEBA HADDA MAZANMA Hajiya shin kina bu atar jikinki yayi kyau fatarki Takoma anya shakaf tamkar ta jarirai ??? Kikoma tamkar zarah acikin taurari acikin mata yan uwanki domin fa hasken zarah dabanne shin kina bu atar fatarki Takoma tamkar ta jaruman Kaneewood kona novel?? Humm kinsan cewar dafata ne matan waje kekar e mana mazaje?? To idan baku saniba ayau kusani, yalli fata shine keru ar mazajenmu dakuma samari kai harmada ammata idan kinshirya gyara jikinki Hajiya kigarzayo domin samun ingatattun ha in daze wanke Miki fatarki tass kikoma tamkar bala rabiya sabida yalli da kyau babu kwailin balle abata miki fata, se ha in zallar gargajiya na an itatuwa masu inganta lafiyar fatarki, *SABULUN WANKA, MAN SHAFAWA GA AMSHI GA DA i, SEKUMA DILKAH WADDA ZAKIYIWA KANKI A CIKIN MINCI* dukkansu afarashi aya za'a ha a Miki duka ukkun wlh wlh wlh summa tallahi acikin mako aya (one week) Zaki banbata fatarki data sauran mutane domin ingatattun kayane kuma inada granty akansu, duk wadda tayi anfani dasu mako aya bataga canjiba tazo wlh Allah zan bata ku inta domin ko haufi banayi akansu gaduk me bu atar wannan ha in ze iya tuntu ar wannan nomber 07037092176 munada maganin mata kala kala namatsi na da i danakomai ma munada harmada na maza wanda suke fama da matsala, gadukkan me bukatar kayanmu ga nomber nan ansaka ze iya nemanmu ako ina yake afa in duniya zamu kaimishi insha Allah sayen nagari meda ku i gida me kyau bayada tsada Ako ina mungode. *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM* Page2 Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar, ya cigaba da driving nashi. Kai tsaye gidan Ummansa ya nufa, bayan yayi horn mai gadin ya bu e masa gate ya shiga ya yi parking. Gaisawa ya yi da mai gadin da sauran ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan. Tsaye ta ke sai kai da kawo da ta ke yi kamar mai safa da marwa. Sallama ya yi ya tura ofar . "Assalamu alaikum" Dakatawa tayi tana kallonsa ta ce, "Wa'alaika salam" Kallonta ya ke da alamar tambaya ya ce, "Umma lafiya kuwa, na ga sai kai da komo kike da alamar akwai damuwa." Murmushi ta alo tare da cewa "Bakomai Baba na kada ka damu." usawa ya yi gaishe da ita cikin girmamawa, ta amsa masa cikin walwala, amma da ka kalle ta kasan hankalinta ba kwance ya ke ba. "Umma idan akwai wata matsala ne ki sanar da ni , ba abunda zaki iya oye mani, haka zalika nima bazan iya oye maki halin da na ke ciki ba." Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Kada ka damu kanka da akwai damuwa kaima kasan bazan oye maka ba." "To shikenan tunda haka ki ka ce." Daga nan ba wanda ya sake magana har tsawon mintuna biyu, daga bisani ya kalle ta ya ce, "Umma gobe zan tafi Kaduna na zo na yi maki sallama ne." Sai da ta ji gabanta ya fa i rass cikin dakiya ta ce, "Ni dai bana son ka yi nisa da mu Baba na, na fi son ya kasance kana tare da mu, muna ganinka kana ganinmu." Kada ki damu Umma zan dinga yawan zuwa insha Allahu, na za i na yi nesa da garin nan ne saboda abubuwan da suka faru a rayuwata, wata kila idan na nisanci garin zan samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata, domin zan samu canjin rayuwa." Idan na fito na bi hanyar da ya kasance hanya ce na unguwar aya daga cikin matayen da na aura ko nayi niyya sai na ji abun ya dawo mani sabo, gara na nisanci garin nan da abubuwa marasa da i suka faru da ni a cikinsa." "To shikenan tunda ka matsa bazan hana ka ba, sai dai in tambaye ka shin zaka tafi da matarka ne?" "A'a Umma ni ka ai zan tafi sai dai zan dinga zuwa weekend." "Amma yakamata ka tafi da ita gaskiya tunda kana da gida a can , ko dai ya ya kana tare da iyalinka ai ya fi." "Haka ne, zan tafi da ita amma da farko ina so na je na ga yanayin wajen idan ya so daga baya zansa Direba ya auko ta." Ba haka ta so ba sai dai ba yadda zata yi tunda baice bazai tafi da ita ba, dan haka ta masa fatan alkhairi." "To Umma ga wannan." i ya ajiye mata kimanin naira dubu ari biyu. "Sannan kuma idan akwai wani abu da kike bu ata ko kuma ya are sai ki kira waya na xansa aka wo har gida." "Kada ka damu ai abincin da suke store da naman da suke fridge duk zasu kai mana wata aya ma basu are ba." "To idan dai da wani abu sai a sanar da ni ko ta waya ne." "To Allah ya yi maka albarka." "Ameen Ummata." Fira suka an ta a daga bisani suka yi sallama ya tafi. Bayan tafiyarsa ne ta kira Amina a waya ta ara zuga ta tare da mata mummunan hu uba, akan ta dage sai ta bi Adamsy Kaduna. Gidansu Sadik abokinsa ya nufa, nan ma ya yi masa sallamar bankwana sannan ya nufi gidansa. Kasancewar lokacin sallar la'asar ta yi ne yasa ya tsaya a wani masallaci ya ya sallah kafin ya nufi gidansa. Koda ya isa gida kai tsaye akin Amina ya nufa, tura kofar ya yi sa sallama. "Assalamu alaikum" "Wa'alaikumus salam." Kallonta ya yi ta sauke akwati tana ta koda kaya a cikin akwatunan guda uku. "Kayan me kike ha awa haka kamar wacce ta ke shirin barin gari.?" "To ba garin zan bari ba?" "Ina zaki je?" "Kaduna mana ai afa ta afarka." "Wai ba na fa a maki cewa wannan tafiyar ni ka ai zan fara yinta ba? Sai daga baya ne zan sa ki zo ba?" "Nifa bazan yarda ba." "Amina yaushe muka fara jayayya da ke ne? Bana son gardama kiyi abinda na ce maki kawai idan ba so kike mu samu matsala da ke ba." Daga nan ya fita ya barta a aki. angaren Humaira kuwa tunda ta shiga aki bayan Inna Habi da Salma sun cinye mata indomie da ta yi wahalar dafawa ga yunwa ta ya cinye ta, tana kwance tana riskar kuka tana ri e cikinta da ke mata ula har barcin wahala ya yi awon gaba da ita. Koda Mallam Musa ya dai daga masallaci ya tarar da Inna Habi da Salma zaune, lokacin har sun kammala cin indomie. Kallonsu ya yi tare da cewa "Ina Haumaira ta ke?" Salma ce ta yi saurin cewa "Yanzu ta kammala cin indomie ta shiga aki wai zata huta." Kai tsaye Mallam Musa ya nufi akin da Humaira ta ke ganinta kwance ya juya baya da alama barci ta ke yi, dan haka ya juya ya koma wajen Inna Habi ya ciro ku i Naira dubu uku ya bata. Washe baki ta yi tare da cewa "Mallam ina ka samu kudi haka?" Wani mutum ne ya ba ni su akan uban gidansa zai dawo nan garin da zama, to ni ne wanda zan dinga masa gadi, shine ya bani kyautar dubu biyar, gobe zan da sassafe zan fara aiki." "Yanzu shi wanda uban gidansa ne zai dawo nan shine ya baka dubu biyar? Ina ga shi mai gidansa da zaka yi aiki a gidansa? Ka ce kakarmu ya yanke sa Shi dai shiru yayi yana sauraronta inda tacigba da cewa "To ina sauran dubu biyun? Naga nan dubu uku ka bani." "Na siyawa Humaira indomie kuma za ri e wasu ku i a hannunsa." "To can zaka dinga kwana ne kuma nawa zasu dinga biya ka?" "Can zan dinga kwana kuma ko nawa zasu biya ni ban sani ba, sai mai gidan ya iso." "To gaskiya sai dai ka bani sauran canjin da suka rage, saboda tsawon lokaci baka bada ku in cefene a gidan nan, ni ce nake aukar awainiyar komai a gidan nan, baki da ku in da zaka biyan dan haka duka dubu biyar zaka bani idan ya so na Indomie da Humaira ta ci na yafe mata." Haka ta dinga zuba masa rashin mutunci har ya mika mata sauran kud'in dan masifarta. Da misalin karfe goma na dare, ya fito daga bathroom sanye da white bathrobe a jikinsa, yana goge kansa da farin towel. Lotion insa mai amshi ya shafa da body spray sannan ya haura saman gadon yana jiran shigowar Amina. Har arfe goma sha aya da rabi na dare yana jiran Amina amma bata zo turaka ba gashi kuma yan bu tarta. Wayarsa ya auka tare da lalubo wayarsa ya tura mata da o kamar haka. "Ina jiranki" Bayan ya tura mata sa on ne sai ya ajiye wayar. Ita kuma tana kwance a akinta sai juyi ta ke yi ta rasa hanyar da zata bi akan tafiyarsa in nan, arar shigowar messages ne ya shigo a wayarta, dubawa ta yi ta karanta, ajiye wayar ta yi bayan ta karanta sau on ta yi tsuki tare da cewa "Ba inda zan zo, tunda har kasa zanyi kwanan ba in ciki to kaima sai dai ka yi kwanan ba in ciki dan ba zaka ata mani rai a banza ba sannan na biya maka bukatarka ba." Jin shiru har arfe goma sha biyu bata zo ba ne yasa ya kira wayarta, ringing ya yi bata aga ba har ya tsinke. Jin kiran ya tsinke ne ya sa shi yin tunanin ko barci ta ke yi, dan haka ya mi e tsaye tare da nufar akinta, dan shi a bu ace ya ke da matarsa a wannan lokacin. Tura kofar ya yi ya shiga tare da sallama duk da a tunaninsa ta yi barci ne, wutar akin a kashe ya ke sai ya kunna, a can arshen gado ya hange ta kwance a tunaninsa barci ta ke yi, kashe hasken ya yi kai tsaye ya nufi kan gadon ya haura, shiga cikin bargon ya yi tare da janyota jikinsa,
Chapter 14 · 0% Book details