← Book details Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 47

Sashe 24

Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wayar ya duba inda ya ga Abdallah ne ke kiransa, agawa yayi tare da karawa a kunnensa. Kafin ya yi magana ne ya ji muryar Abdallah na cewa *Adams kun tashi lafiya?" "Lafiya lau" "Ya jikin Humaira?" "Da sau "Kana tare da ita ne?" "Tana akinta nima ina akina. Amma shigowa ta kenan daga akinta, dan na ga sai tsorona ta ke yi bata ma yarda na je kusa da ita." Dariya Abdallah ya yi tare da cewa "Ai dole ta ji tsoronka mutum kamar doki, har ka ana mata amshin mutuwa..." Bai jira ya kai arshen zancensa ba ya kashe wayar,dan bazai iya jiran tsiyar da zai masa ba. Lambar wayar Amina ya lalubo ya danna mata kira, sau biyu yana kira bata daga ba sai a na uku sannan ta aga. Tana kwance a saman gadonta lullu e a cikin bargo, dai tsuki ta ke yi dan ta san waye ya kira ta a daidai wannan lokaci. Tura baki ta yi tare da cewa "Hello" Murmushin takaici ya yi tare da cewa "Ki tashi ki yi sallah" "To na ji" "Ba to kin ji ba ta shi na ce ki yi." Kashe wayar ta yi tare da yin cilli da shi gefe. "Mutum sai damuwa kabar garin ma ba zaka bar mutun ya huta ba sai ka ce kai zan wa sallar." Juyawa ta yi sannan ta gyara kwanciyarta. Bayan kamar mintuna biyar ya sake kiran wayar. Ta shi ta yi tana cewa "Aifa idan ba tashi na yi ba bazai ta a bari na huta ba." Jin bata aga bane ya sa shi sanin cewa ta tashi yin sallah . Dan dama inda sabo ya saba da halinta, a'ida sai ya tayar da ita wata rana idan ta farka ta ga lokacin sallar ta yi ne sai ta tashi da kanta ta yi. Dan ta san cewa ko bata ta shi ba a'ida sai ya tayar da ita. Bayan ta fito daga wanka ne, sai ta ji jikinta ya mata an sau i ba laifi sakamakon gada jikinta da ruwan zafi da ta yi. Dagowar riga na material ta saka, sannan ta saka hijabi ta hau kan sallaya ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar ne tana azkar din safiya kamar yadda ta saba. Bayan ta gama ne sai ta an kwanta a saman darduma kewar mahaifinta kawai ta ke yi, ba abunda ta ke muradi illah ta saka shi a idanunta. Ta shi ta yi a hankali ta fara tafiya zuwa jikin window da ke akin, a hankali ta bu e glas in window ta hango mahaifinta zaune a barandar akinsa yana sanye da rigar sanyi mai ha e da hula, kasancewar garin sanyin damina ne musamman da aka kwana ana ruwan sama sai wajen asuba sannan ruwan saman ya tsaya. Karatun Alqur'ani ya ke yi. Zuba masa idanu tayi tana kallonsa har Adamsy ya shigo akin bata sani ba, a hankali ya araso wajen da ta ke tssye bata ma sani ba, hannunsa ya sa a saman kafa arta ta juyo a firgice tana kallonsa. Matsawa ta sake yi ta shige jikin bango tare da janyo labulen windon ta oye kanta a ciki. "Me ki ke yi a nan?" Shiru ya yi ba tare da ta ce komai ba irjinta na dukan uku-uku, dan tsoron ya zo kusa da ita ta ke yi. "Ki daina jin tsorona haka nan kinji, bazan cutar da ke." Tura baki ta yi tare da cewa "Nidai wajen Abbana zan koma." "Abbanki ya kawo ki nan ne dan ki zauna zama na har abada, mutuwa ce ka ai zata raba ni da ke." Kuka ne ya ta fashe da shi tare da cewa "Wallahi bazan iya zama da kai ba sai dai na koma cikin uncin da na fito ya fiye mani..." "Dakata kiji, nan fa gidan aure ne kuma aure ibada ne, zaman raya sunnah kike fa." "Nasan aure ibada ne amma idan da cuta barinsa halak ne." "Ta wace hanya na cutar da ke?" Sunkuyar da kanta asa ta yi duk da tana cikin labule baya ganin fuskarta, tura baki kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Murmushi kawai ya yi dan ya tuna abinda ya faru jiya daddare ne ya sa ta jin tsoron zama da shi. "Shekarunki nawa?" "Shekaruna goma sha shida, dai ranar babban sallah zan cika sha bakwai." Shiru ya yi yana nazari kalli aramar yarinya ce, amma idan ka kalle ta ba zaka ta a tunanin cewa iya shekarunta kenan ba, musamman yadda komai na jikinta ya amsa sunansa, zaka yi tunanin 'yar shekaru ashirin ce. Dan duk suffarta sun cika ga irjinta a cike fam ga hips inta ya fito kasancewar tana da ira mai kyau. Mamaki kawai ya ke yanzu aramar yarinya ce ta saka shi fita hayyacinsa duk ya bi ya gigice baima san me ke faruwa ba sai da ya samu biyan bu atarsa, jinjina kai ya yi kalli Humaira ta dabance a cikin mata. "To yanzu me kike so na maku?" "Nidai kawai zan koma wajen Abbana ne." "Kinga abunda ya faru tsakanin ni da ke jiya fa ba wani abu bane kowace mace sai da taji abinda kika ji, kuma dan na farko ne shi ya sa, amma idan muka sake ba zak..." "Sautin kukanta ta ara, da sauri ya yaye labulen tare da cewa "A'a ki kwantar da hankalinki ba abunda zan sake yi." yar ya rarrashe ta ta yi shiru ta daina kukan. "Muje ki yi breafast." Hannunta ya ri e cikin nasa, ta na arin zame hannunta daga ri on da ya mata, yayi saurin matse hannunta cikin nasa yadda ba zata iya zamewa ba. A haka suka fara tafiya a hankali saboda yanayin yadda ta ke tafiya,ganin haka ya sa ya auke ta cak ya nufi dinning area da ita, arin sauka ta ke yi ne sai ya yi ki bata damar da zata sauka,a haka har suka arasa ya dire ta a hankali saman daya daga cikin kujerin dake wajen. Zama ya yi shima yana fuskantarta. "Me zaki ci?" Tana maganar yana bu e duk abinda ke wajen tana gani. Shayi da bread ne sai soyayyar wai da dankalin turawa da plantain. Gefe guda kuma ga farfesun kaji nan da farfesun kayan ciki kallon dayan flask in ta yi ta ga indomie ne da ya ji kayan ha Sunkuyar da kanta ta yi tana tuna rayuwar gidansu, ga koko tana tallansa amma ba za'a bata ta sha ba, sai dai ta ci sauran tuwon jiya, Idan aka ba Salma koko tana sha sai ta ji dama ita aka bawa itama. Yau ita ce a cikin wannan daula, ga abinci nan na kalaci kala-kala sai wanda ranta ya so zata ci, ta yi nisa cikin zurfin tanani da ta ke yi ne ta ji ya ta a mata afa, agowa ta yi tana kallonsa tare da cewa "Na'am" "Tunanin me kike yi ne?" Girgiza masa kai ta yi alamar ba komai. "Me zan zuba Mali?" A hankali ta ce "Ni koko da uli uli na ke so?" Zuba mata idanu ya yi tare da cewa "Koko kuma da uli?" Jinjina masa kai ta yi alamar eh. Shiru ya yi yana nazari sannan ya kalle ta ya ce, "Me ya sa duk abinda ke nan baki so sai abinda babu shi?" "Kullun addu'a ta Allah ya kawo mani ranar da nima zan zama irin Salma na dinga shan koko da uli kamar yadda ta ke ci." Bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba. Sai da yayi dariya har ya ishe sa zuba masa idanu ta yi tana kallonsa duk takaici ya ishe ta, na dariyar da ya ke mata dai da ya ga yadda fuskarta ya canza kamar zata yi kuka sannan ya dakatar da dariyar tare da cewa "Am sorry" Maida wallar da ke shirin zubo mata ta yi tare da kauda kanta gefe. "Kada ki damu duk abunda kuke so shi zan maki, nidai bansan yadda zan samo maki koko ba, dan dama yau kuku da zai dinga mani girki zai iso, kuma restaurant da ake kawo mani abunci basu siyar da kokon, bansan inda zan samu ba." "Ni na sani." "Ina kenan" "A unguwarmu farkon layin shigowa anan akwai." "Shikenan bari na kira Direba ya kaimu sai ki nuna masa hanya tunda ke kika san wajen." Wayarsa ya auka ya kira layin Direbansa ya sanar da shi inda zasu tafi. Kasancewar hijabi ne a jikinta sai ta mi a hannu ta auki wani jug da ke gafenta ta nufi hanyar fita, shi dai ido kawai yake binta da shi. Ga tafiyarta ya sauya dan ma hijabinta har asa ya ke ja mata, sai ta ke dan tafiya a hankali yadda ba kowa zai gane yadda ta ke tafiyar ba. arasawa ta yi wajen maigaifinta inda ta ganshi zaune yana sauraren rediyo, shima an ajiye masa abincinsa. usawa tayi har asa tare da gaishe da mahaifinta, ya amsa mata cikin jin da i da farin ciki. Dai-dai lokacin da Adamsy ya araso wajen , kasancewar dama tunda ya dawo daga masallaci sun riga sun gaisa da Mallam Musa, sai ya ke jin nauyin Mallam Musa da kuma kunyarsa, a zuciyarsa yana tunanin abunda zai masa da zai daina masa gadi, dan bazai yiwu ba a ce ya dauki 'yarsa ya basa sannan ya cigaba da masu gadi ba. Sake gaida Mallam Musa ya yi sannan ya nufi wajen motarsa, already Direbansa na cikin motar yana jiran arasowarsu. Bayan ya shiga bayan motar ne yana jiran isowar Haumaira. Humaira kuwa ta kalli Mallam Musa ta ce, "Abba zamu je siyan koko?" Take fara'ar da ke kan fusakarsa ya sauya, dan ya san Humaira ce da wannan aikin, da ta sa mijinta da Direbansa fita nemam koko. "Haba Humaira ke wace irin yarinya ce, kawai sai kisa mutan fita cikin sanyin nan dan kawai zai sha koko? Me ya sa ba zaki ci abunda kea gidan ba idan ma kokon kike so kisa a siyo maki gero kiyi d kanki, wannan ba girman yalla ai bane da zai fita nemam koko." Nam dai ya yi mata fa a sosai tare da mata garga in kada ya sake jin
Chapter 24 · 0% Book details