Sashe 4
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baban Fauziyya ya koma gida ya tambaye ta sai ta nuna ita bata sonsa, dan haka Baabanta da Mamanta sunyi masa fa a sosai kamar ta ha ura amma a zuciyarta ba haka ba. *KADUNA* Wasu matasan 'yan mata wa anda ba zasu wuce shekaru goma sha biyar, aya tana wanke kwanika aya kuma tana sanye da kayan makarantar boko tana shan koko. Wacce take sanye da kayan makarantar bokon ce ta kalli mai wanke kwanika ta ce, "Ke Humaira ki yi sauri ki arasa wanke-wanke nan kizo na aike ki?" Maihaifinsu da ke fitowa daga akinsa ne ya kalli wacce ke sanye da kayan makarnata ya ce, "Salma me yasa kike wa yarinyar nan haka ne? Tana aiki kina mata ihu ta gama ta zo ki aike ta? Ke aikin me kike yi da ba zaki tafi aiken da kanki ba?" Tura baki tayi tare da cewa "Nifa makaranta zani Baba." "To ita ba zata tafi makarantar bame? " Kallon Humaira yayi tare da cewa "Me yasa ke baki shirya zuwa makarantar ba?" "Baba Inna ce ta hana ni zuwa makaranta wai ta cire ki daga makarantar." Kallon mamaki yake mata tare da cewa "Akan me ta cire ki?" "Wai idan na tafi makaranta ba wacce zata dinga mata aiyukan gidan da kuma aike da ibar ruwa." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un," Ya juya ya kalli oafar akin Inna tare da cewa "Habi! Habi!! Habi!!!" Inna da ke cikin aki tana jin duk maganar da suke ne ta fito tare da cewa "Lafiya Mallam kake wala mani kira da sassafe haka?" "Akan wane dalili ne yasa zaki hana Humaira zuwa makaranta? Bayan ga 'yarki nan baki hana ta ba sai ita?" Cikin nuna isa da gadara ta ce, "Saboda ni ba baiwarta bace kuma ba baiwar uwarta bace, idan ta tafi makaranta nine zan dinga aiyukan gidan ko yaya?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Bazai yiwu ba wallahi, lokacin da uwarta ke da rai duk ranar girkin uwarta uwarta ce take aiyukan gidan sai idan 'yarta ta taya ta nima duk ranar girkina ni nake aiyukan gidan sai idan 'ya ta ce ta taya ni, don haka bazaiyiwu ace uwarta ta mutu ba sannan ni na dinga mata aiyukan gidan, bazaiyiwu ba." "Yanzu Habi kina kishi da uwar yarinyar nan, sannan bayan ranta ma sai kinyi kishi da 'yar da ta haifa." e baki tayi tare da cewa "Dama na sani haka abin yake, lokacin da uwar ke da rai ita ce matar so yanzu bata da rai 'yar ta kuma ita ce 'yar so." Kallon Humaira da ke zubda walla tayi tare da cewa "Ki sani na kashe katatunki matukar kika fita a gidan nan da sunan zuwa makaranta kika dawo sai na kusan kashe ki, sannan kuma wanke-wanke da shara da wankin kayana da na Salma suna kanki, ibar ruwa da uku kece dakan garin kunu ko na tura duk kece ki rubuta ki ajiye karatu kam ba zaki same shi ba." Kuka Humaira ta fashe da shi na ba in ciki, yayin da kuma Salma ke farin ciki da hukuncin da uwarta ta yanke, dan dama Humaira tafi ta arin kowane lokaci ita ke zuwa na aya a makaranta hakan na ona mata rai,dan ita ce kusan ta arshe. Cikin acin rai Mallam Musa ya kalli Habi ya ce, "Baki isa ba ni zan yanke hukunci da gida na ba ke ba, dan ni ne mai gidan." Dariya ta sheke da shi "Mallam Musa da ne kake mai gida lokacin da kake da abunyi ba yanzun da baka da aikin yi ko sana'ar yi ba, tunda ni nake san'a nake aukar nauyin gidan nan kuwa ai nine mai gidan ba kowa ba, dan haka talla ma zata fara zuwa." Da sauri ya kalle ta tare da cewa "Tallah?" Jinjina kai tayi cikin isa ta ce, "Cif". Rana bata arya sai dai uwar aya ta ji kunya, yaune za'ayi aurin auren Adamsy da Fauziyya. Jama'a sun taru a ofar gidansu Fauziyya dangin Amarya da dangin Ango da 'yan uwa da abokan arziki kowa ya hallara ango da abokansa ma duk suna nan, an fara gabatar da aurin aure ga waliyin ango da na amarya inda waliyin ango ya fara magana ya ke cewa waliyin amarya. "Ni Alhaji Kabiru ina nemawa ana Adam auren Fau..." "Ku dakatar da wannan aurin auren!" Muryar mace suka ji kowa ya fara kalle-kalle dan sanin wace ce take maganar, me zai kawo mace wajen aurin aure? Nan fa aka fara kallon kallo. *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman arin bayani* 09065327995 Love you oll Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANRWA* Wannan irerren labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba. Arashi ne mai kashe auren wawa. Page 5 & 6 Muryar mace suka ji kowa ya fara kalle-kalle dan sanin wace ce take maganar, me zai kawo mace wajen aurin aure? Nan aka fara kallon-kallo. Fauziyya ce tsaye a wajen hajaran majaran tamkar wata zautacciya, zubewa tayi ta dur usa akan gwuiwar afarta tare da fashewa da wani matsancin kuka, kallon maihaifinsu tayi tare da cewa "Dan Allah kada a aura auren nan, wallahi bana son auren nan idan aka aura shi zan iya mutuwa." arasa maganar tana mai fashewa da wani sabon kuka,mi ewa tsaye tayi zata nufo inda mahaifinta yake zaune, ganin haka yasa ya mike tare da nufarta yana arasawa gabanta ya wanke ta da tagwayen maruka akan fusakarta, sake aga hannu yayi da niyyar kai mata mari sai Adamsy yayi saurin shiga a tsakaninsu tare da cewa "Dan Allah Baba kayi ha uri, a dakatar da wannan aurin auren ni na janye Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu." Cikin tsananin acin rai mahaifinta ya ce, "Fauziyya irin tarbiyyar da na baki kenan? Ni zaki kunyata a gaban jama'ar da na tara?" Cikin kuka ta ce, "Dan Allah Baba kayi ha uri wallahi zauciya ta bata sonsa." "Da can baki san da baki sonsa ba lokacin da kika kawo shi a matsayin mijin da zaki aura? To baki isa ba ko kukan jini zakiyi ke ko mutuwa zaki yi sai dai ki mutu amma wannan auren ba makawa sai an aura shi." "Kayi ha uri Baba ka gafarce ni amma tunda har ankai ga haka, ta fito da kanta ta ce bata so na bata son auren nan to na ha ura da Fauziyya har abada." Baba ya bar wajen cikin tsananin acin rai yana huci. Adamsy kallon Fauziyya yayi tare da cewa. "Me yasa baki so na?" Nayi maku laifi ne? Da can ne baki so na ko sai yanzu?" "Dan Allah kayi ha uri wallahi bana son aurenka ka taimaka kada ka bari Baba na ya ha a wannan auren ka tausayawa rayuwa ta." Murmushi wanda yafi kuka ciwo yayi tare da cewa "Baza'a aura ba tunda baki son auren nan, nima bazan ta a auren macen da bata so na ba, tashi ki tafi gida." Jikinta na rawa tayi masa godiya ta bar wajen, komawa yayi wajen nahaifin Fauziyya tare da basa hakuri yana tausansa, dan ganin cewa ya samu nutsuwa, yayin da shima kansa Adamsy arfin hali kawai yake yi, zuciyarsa tafarfasa take masa da zugi." Abokansa ne suka ja shi suka nufi mota, Sadik na mazaunin direba yayin da shi kuma Adamsy yana zaune a gefensa. Sai abokansa su uku da ke a bayan motar, Babawo Aminu sai Umar . Lokacin da suka hau titi ne Salisu ya juya ya kalli Adamsy ya ce, "Abokina ni fa wannan al'amari ya fara bani tsoro? Sai hu u fa kenan, kana yin urin aure ko bayan auren sai zama bazai yiwu ba. Da farko dai ya auri Atika itama hala ranar aurin aure aka fasa, sannan ka fara neman Basma ita kuma bayan an aura auren ta i yarda ta shiga gidan auren ma, duk yadda akayi ta ce ba zata yarda ta zauna da kai ba aka dinga fama arshe dai haka aka hakura ka sake ta. Sannan ga Husnah bayan ankaita gidanka zama ya i da i sai gudunka take, itama ka rabu da ita yanzu ga Fauziyya ranar aurin aure abun baiyuwu ba, yakamata fa ka duba magana ta mata har hu u kuna soyayya da su da anzo kan aure sai abu ya lalace gaskiya ba banza ba." Babawo ya aura da cewa "Nifa ina ganin kamar aljanna ce ta aure shi, shiyasa take raba shi da duk wata macen da ya so ya aura." Girgiza kai Umar yayi tare da cewa "Bana tunanin cewa aljannah ce ta aure shi, dan idan aljana ce ta aure shi ne yasa tabarshi tare da Amina? Ai da har da Amina ma sai ta raba su kamar yadda take raba sauran matansa." "To ka sani ko Aminar tafi arfin aljanarce shiyasa ta barta? Dan ba yadda zata yi da ita." Haka dai suka dinga magana kowa na tofa albarkacin bakinsa, shi dai Adamsy bai ce komai ba sune suke ta zantuttukansu kowa da abinda yake cewa. Har suka isa ofar gidansa baice da su komai ba, gaba aya ji yake duniyar ta masa zafi. Kallon Sadik yayi tare da cewa "Ba sai ka shiga cikin ba, ka tsayar da motar anan waje, zan shiga ka tafi da motar zuwa gobe ko anjima idan ka samu lokaci sai ka dawo mani da motar." Bai jira cewarsu ba ya saka kai ya shiga cikin gidan. Da sallama ya shiga cikin gidan a falo ya tarar da Amina da awayenta sai kuma 'yan uwanta fa suka zo bikin, amsa masa sallamar suka yi inda anwar Amina mai suna Zahriyya ta kalle shi tare da cewa "Ango kasha amshi." Sauran jama'ar da ke falin ne