Sashe 10
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuka tana tafiya har ta iya shigewa akinta. Kayan jikinta ta cire kasancewar duk sun lalace ta fito ta nufi randar ruwa ta bu e ta debi ruwa cikin bokiti ta nufi hanyar ban aki dan yin wanka. Bayan ta fito ne ta saka kayan da zata saka doguwar riga ce ta atamafar roba sai hijabinta da ta saka. "Wai dan uwarki ba zaki fito ki auki tallar doyar bane? Ko so kike tayi kwantai 'yar ba in ciki kawai." Tafiya take inda ta kalli afarta inda ya one da wuta ya girma ya ari ruwa, sai kuma gefen cikinta da take ji yana mata zafi sosai sai guiwar afarta da ke mata ciwo inda Inna ta buga mata itace. Fitowa tayi tana fitowa ta watsa mata harara tare da cewa "Ki kama jiki bakwai ki dinga tafiya kamar kazar da wai ya fashe mata a ciki." Lokacin da ta fito har Inna Habi ta kammala zuba mata doya a farin bokiti irin wanda ake ganin duk abinda ke cikin robar , sannan ta ajiye mata garin yaaji da soyayyen man gya Bayan ta fito daga cikin akin take tafiya a hankali sai ta ji muryar Inna tana cewa. "Dalla kama jiki kina tafiya kamar wacce bata da kaka a jikinta." Bayan ta araso ne ta auki bokitin doyar tare da aukar soyayyen mai da ya ji ta nufi hanyar fita.sai ta ji muryar Inna Habi ta ce, "Doyar nan ta dubu biyu ce ko naira biyar tayi ciwon kai wallahi sai jikinki ya fa a maku." Haka ta fita tana tafiya tana yangyashi afsrta na ciwo dai-dai guiwar afar damanta wajen duka, kuma gashi tallar doyar yawo zata dingayi ba zama ba ballantana a ce zata huta. Haka ya wuni kwance wayoyinsa ma a kashe, gaba aya ya rasa sukunin da walwala, ya aurawa kansa alhakin abinda ya samu 'yan matan nan a kansa. Gani haka shine sanadiyyar komai da ya faru dan haka garin da abubuwan nan suka faru ma ya masa zafi, ji yake gaba aya ya tsani garin da zamansa, gara ya canza gari ko zai rage damuwa, ya yanke shawara koda ya koma wane gari bazai ta a bari wata 'ya mace ta shiga rayuwarsa ba ballantana wata masifa ta same ta sanadiyarsa Sau yamma sannan Baba Ashiru anin mahaifinsa ya zo Lokacin jama'a suka sun watse, Umma ce tayi masa Jagora har zuwa akinsa, Bayan sun gaisa ne ya kalli Umma ya kalli Adamsy ya ce, "Nifa wannan al'amari ya fara isa na, a ce mata ai har guda biyar kuma kowace na ta kalar masifar daban, lamarin nan fa abin dubawa ne, wannan ta rasu wannan ta haukace waccan ta makance kowa da irin tata masifar." Ajiyar zuciya Adamsy yayi tare da cewa "Na yanke wata shawara Allah yasa zaku amince... *Kuyi ha uri da Wannan* *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman arin bayani* 09065327995 Love you oll *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://chat.whatsapp.com/IdLjpWceclh5VR8G5W9SFY . INA MASU BUKATAR KAYA AKAN FARA SHIN SARI KU SARA KU SIYAR KU SAMU NAKU AKAN FARASHI KALILAN MUNA DA KAYA KALA KALA KAMAR SU HIJABAI KAYAN KITCHEN ATAMFA LACE KAYAN YARA MOTHER CARE KAYAN SHAN ISKA NA ABBA MATERIAL DINKAKKE DA YADIN BEDSHEETS HULUNA DA SAURAN SU MUNA TURA KAYA DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI UBANGIJI *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Page1 Nan ya yanke wata shawara Allah yasa zaku amince..." Umma ce ta kalle shi tare da cewa. "Wata shawara ka yanke?" "Ina son zan koma garin Kaduna dan na cigaba da tafiyar da kamfaninmu da ke gari, dan wallahi zaman garin nan ya ishe ni na gwammaci nayi nisa da garin nan ko zan iya mancewa da muanan abubuwan da suka faru a rayuwa ta." Umma ce ta kalle shi ta ce, "Mancewa da abubuwan da suka faru a rayuwarka ba abu bane mai sau i, a tunani na mancewa da su wani abu ne mai kamar wahalal." Gajeren murmushi yayi Wanda ya tsaya iya fatar bakinsa bai kai zuci ba, sannan ya ora da cewa "Ummana koda ban mance komai ba amma zan rage wasu damuwar tunda bana ganin unguwanni kowa cikinsu." Baba Ashiru ne ka kalli Adamsy ya ce, Ta wani angaren maso komawa da zaka yi, dan kamfanin mahaifin naka da ke can an banzatar da shi ba kulawa ba komai, kuma ga gidajenku da ke can maihaifinka da ke can. Maida dubansa yayi zuwa ga Umma sannan ya ce, "Maganar matsalarsa da yaron nan yake fuskanta ne abun dubawa, ba haka kawai abubuwan nan suke faruwa ba dole akwai ummul'aba'isin faruwar komai. Walau mutum ko aljan." Shiru Umma tayi kamar mai nazari sannan ta ora da cewa "To yanzu me kake so ayi ne?" "Mu tafi wajen Shatima ya bincika mana wannan lamarin dan ya gano komai, indai Shatima ne wannan abun shan ruwa ya fi shi wahala a wajensa, tun daga farko har arshe zai sanar da mu komai ko sanya hannun an Adam ko kuma sharrin jini wata aljana ce ta aure da duk zai gani." Umma ce ta kalle shi tare da cewa "Shatima ai boka ne." "Kinga ba wani boka kawai..." Adamsy ne ya katse masa hanzsrinsa ta hanyar cewa "Baba Ashiru ni dai duk wannan zancen a barshi kawai, na fawwalawa lamarina, komai ya faru da ni hala Allah yaso da ni." "Kai da matarka zaka koma Kadunar ne ko yaya?" Umma ce tayi masa wannan tambayar. "Zan fara komawa ni ka ai amma idan naga yanayin wajen yayi mani sai na dawo na auke ta mu koma can." Baba Ashiru ne ya kalle shi tare da cewa "Ni kuma bazan so ka tafi da matarka can ba, dan idan ka tafi da ita sai mun da e kafin mu ganka, amma idan yakasance tana nan tare da mu to ganinka bazai mana wahala b. Nasan zai dinga dawowa week koda bayan sati biyi ne ko idan ya auki hutu ya zo wajen mu gansa. Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Kada ka damu duk inda nake kuna cikin raina, ai ba zan ta aukan tsawon lokaci ba tare da na zo naga Ummata ba kuma tunda mahaifina ya rasu kai nake gani a matsayinsa kasancewarsa aninsa, kallonsa nake maka." Turo ofar akayi aka shigo tare da sallama, Sadik ne ya shigo bakinsa auke da sallama. "Assalamu alaikum" Gaba aya suka amsa masa da "Wa'alaika salam" Gaida Umma yayi da Baba Ashiru sannan ya maida dubansa ga Adamsy dake masa kallon mamaki. "Ya aka yi kasan ina nan?" "Ya bazan sani ba, bayan na kira ka baka sanar da ni inda kake ba illa kawai ka ce an fasa aurin aure, na je gidanka matarka ta fa a mani baka nan shiyasa nasan cewa baka da inda zaka je da ya wuce nan." Kama hannunsa yayi tare da cewa "Tashi mu tafi." "Mu tafi ina kuma?" "Wajen wani malami dan wannan lamarin naka zuwa yanzu ya fara bani tsoro sosai, abun naka dole sai an danganta shi da malamai na kira shi na sanar da shi halin da kake ciki sh ne yake sanar da ni cewa rayuwarka tana cikin hatsari mu zo tare da kai yana don ganinka." Fisge hannunsa yayi daga ri on da Sadik yayi masa tare da cewa "Kai dalla rabu da ni, waye ya fa a maka rayuwa ta tana cikin hatsari shi yasan gaibu ne? Ai sanin gaibu sai Allah ba inda zan tafi da zaku je ku raba ni da imanina." "Daga taimako?" "Bana bu atar taimakon ballantana..." Baba Ashiru ne ya katse sa ta hanyar cewa "Mai sunan Babana nima fa lamarin nan naka ya bani tsoro, da zaka bi ta shawara ta da ka bishi kun tafi." "Baba na fawwalawa wa Allah lamarina , duk abinda ya faru da ni haka Allah yaso da ni." "Shikenan ai tunda ka dage kuma na lura kai da Umman taka a idarku iri aya ne Allah yayi mana magani ya iya mana kada ya barmu da iyawarmu." Umma ne da Baba Ashiru suka fita suka bar Adamsy tare da Sadik suma tattunawa. Bayan Baba Ashiru ya tafi gidansa ne Umma ta nemi Direbanta da ya kaita gidan Admsy. Bayan Direbanta ya yi parking ne ta fito tare da bashi umarnin ya jira ta ta fito. Amina ita da wasu awayenta biyu ne a falo, suka gaida Umma. "Ina wuni Umma?" "Lafiya lau ya kuke?" Suka amsa mata da lafiya lau. Kallon Amina tayi tare da cewa "Magana zamu yi da ke mu shiga ciki sauri nake yi. ewa Amina tayi ta bi bayan Umma zuwa akinta. Kallonta Umma tayi tare da cewa "Ki saurare ni da kyau dan duk abinda nake yi dan ke nake yi, kowa rai yama da i bai kai mai shi ba." Jinjina kai Amina tayi tare da cewa "Ina saurarenki Umma." "Adamsy zai bar garin nan da zama zai koma Kaduna zai cigaba da kula da kamfanin mahaifinsa da ke can garin Kaduna. Kuma komawarsu Kaduna ba karamar barazana ba ce a gare mu." Ta ina hakan zai zama barazana a gare mu Umma? Mata nawa ne mazajensu suna can wani gari suna aiki amma matayensu basa tare da su, sai dai idan sun samu sarari su zo suga iyalinsu su koma wajen aikinsu, ni a gani na wannan ba matsala bace." Tsawa Umma ta daka mata tare da cewa. "Dalla rufe mani baki sha sha sha kawai da bata san ciwon kanta ba, to bari kiji matu ar Adamsy ya auri wata matar to daga ni har ke zamu tashi a tutan babu, kuma bazan ta a bari hakan ta faru ba." Kallon mamaki Amina ta dinga yi wa Umma sannan ta ora da cewa "Umma kada dai a ce duk abinda ke faruwa da mijina ke ce sila? Kada a ce ke ce kike raba shi da matan da yake shirin aure da wa anda yake aure?" Jinjina kai Umma tayi tare da cewa warai kuwa ni ce nake shirya komai." "Ta ya ya hakan ta faru ne ye dalilinki?" Wani shu'umin murmushi Umma tayi tare da cewa.