Sashe 31
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, sabida iya inganta soyayyar dake tsakanin mata da miji" "Amma yanzu matan zamani ga ilmin, amma saidai da yawansu basu iya kula da miji ba, saidai tarin kishi mai yawa, dalilin hakan sai kaga mace-macen aure ya yawaita a wannan zamanin" Haka ya cigaba da mata nasiha sosai, kuma jikinta ya yi sanyi sosai. Daga nan suka an ta a fira ganin magrib na gabatowa ne ya umarce ta da ta tashi ta koma cikin gida. Da misalin karfe goma na dare yana zaune a falo yana kallon t.v sai Amina ta fito daga akinta. Sanye ta ke da rigar barci wacce ita da babu marabarsu ka an ne, dan rigar iya rabin cinyarta ta ke mai shara-shara komai na jikinta a bayyane ya ke. Ta fito tana taku aya bayan aya sai amshin turare ta ke yi, wanda amshin ne ya saka Adamsy agowa ya kalle ta. Kallo aya ya mata ya auke idanunsa daga kallonta ya maida kan t.v. Har ta gifta ta gabansa ta nufi fridge bai sake kallonta ba. e fridge ta yi ta ciro youghurt da kofi ta zo ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, ta zuba a kofi ta fara sha tana satan kallonsa. Ta ga ko kallonta bai sake yi ba, mamaki ne ya kama ta shi da idan ya ganta haka hankalinsa ke ta shi ta ke ya ke janyota jikinsa arshe sai ya biya bu atarsa da ta tado masa amma yanzu ko gezau kamar wani dutse. Sanin da ta masa sam bata iya hakuri da ita baya iya yale ta indai ya ganta a haka amma wai yau shi ne ya kauda idonsa kamar ba Adamsy da ta sani ba. Kuma ko da ya bar garin nan da sha'awarta ya tafi saboda ya bukaci kwanciyar aure da ita ta bijire masa ya tafi da acin ran abunda ta masa. Sannan yanzu ya dawo bata gabansa ma ya share ta, tambayar kanta ta fara yi ko dai ya fara bin matan banza ne? Ga shi girman kai ya hana ta bashi ha uri idan ma fushi ya ke da ita. Ganin ko kallo bata ishe sa ba ya sa ta tashi ta nufi akinsa dan ta san tabbas idan bata bishi sun kwana a dakinsa ba dole zai kira ta zuwa akinsa. Har arfe goma sha aya da rabi bata ga ya kira ta ba kuma ita bata jin zata iya binsa akinsa sai ya biyo ta ko ya kira ta. Shi ma share ta ya yi dan baya son abunda zai kara mata masa rai, dan ya san idan ta faranta masa na awa aya daga ta bata masa rai na awanni biyar. Kuma idan ta faranta masa na sati aya sai ta bata masa rai na wata aya. Ta shi ya yi ya nufi akinsa tare da fa awa kan gadon yana jinsa ba walwala da kuzari tamakar ya rasa wani sashe na jikinsa. Komawa ya yi yana ta tunane-tunane, daga arshe ganin Amina bata shigo bane ya sa ya fara tunanin kiranta a waya, dan gani ya ke idan ya share ta kamar bai kyuta mata ba. Wayarsa ta lalubo ya tura mata text message kamar haka :_UWAR GIDA RAN GIDA, AN SHANYA NI AI SAI A ZO A BAZA NI HAKA NAN KO_ tura mata ya yi tare da kishin gi a yana tunanin halinta, ita ce ta masa laifi amma shi ke rarrashinta, dan kullun sai Umma ya tunasar da shi cewa Amina amana ce bata yarda ya ata mata ba, sau tari albarkacin Umma ta ke ci ya ke yale ta idan ta masa laifi. Tana kwance ta ji shigowar messages a wayarta, san shi ne kamar ba zata duba ba sai kuma ta duba ta karanta tare da cewa "Sai yanzu da bu atarka ta tashi ka san da ni, to ba inda zan je sai na ja aji." Gyara kwanciyarta ta yi tare da yin tsuki. Jin shiru ne ya sa shi aga waya ya danna mata kira, sai ya ga an katse kiran. Sake kira ya yi ya ji wayar a kashe. Kamar ya share ta amma ba zai iya ba, duk da ba laifinsa bane amma gani ya ke kamar bai mata adalci ba. Tashi ya yi ya nufi akinta yana tura ofar sai ya ji ta a datse. Knocking ya yi tana jinsa sai ta yi kamar bata ji ba, shima ya san da gan-gan ta yi, tunda ya kira ta sai ta katse. Juyawa ya yi tare da komawa akunan, wayar Humaira ya kira suka fara fira. Sai da ya ji alamar tana jin barci sannan ya yi mata sallama ya katse kiran Haka suka cigaba da zama har Adamsy ya kwashe kwanaki uku a garin Katsina, ranar da aka aura auren ne bayan ya dawo daga wajen dinner ne ya samu Amina a falo, tana waya amma daga ganinsa sai ta yi saurin katse kiran wayar alamar rashin gaskiya. Kallo aya ya mata ya gane bata da gaskiya. Bai kula ta ba duk da cewar sallamarsa ma bata amsa ba, akinsa ya nufa dan dama a gajiye ya ke. Allah ya sa dai yau an gama hidimar biki. Bathroom ya wuce dan watsa ruwa. Na jimawa ya fito sanye da white bathrobe, wani barci ya ke jin yana zuwa masa, a haka ya nufi gadon ya kwanta. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi. Ko Humaira da suke firar dare ka fin ya yi barci, ba su samu damar yi ba. Washe gari da safe sai ga Umma ta zo gidan. Yana barci ya ji arar wayarsa, a hankali ya bu e idanunsa tare da aukar wayar. Ganin Umma ce ya sa ya aga tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaika salam" "Barka da safiya Umma." "Yauwa barka dai, ina falonka." Daga nan ta katse kiran wayar. Ta shi ya yi ya auki jallabiyarsa ya saka. A falo ta sa me su tana zaune akan kujera Amina na zaune a saman carpet. usawa ya yi cikin girmamawa ya gaida Umma, ta amsa masa ba yabo ba fallasa. "Dama na zo ne akan maganar da matarka ta mani na cewa akwai wani mai magani a asar Niger. Wai ya kware akan irin matsalar matarka, mutane da yawa sun je kuma sun dace. Shi ya sa koda ta sanar da ni na ga yakamata ta je, tunda an yi na asibiti har an gaji ba'a dace ba har asar waje an fita da ita amma shiru. Jinjina kai ya yi tare da tuna wane irin hali ne da Amina, suna kwana gida guda amma ba zata iya fa a masa bu atar da ta ke da shi ba har sai mahaifiyarsa ta shiga ciki. "To wai ance mata masu irin matsalarta miliyan biyu ya ke aiki, kuma wai ana dacewa." Kai ya jinjina tare da cewa "Ba komai ita da wa zasu tafi Niger in?" "Wai awarta da ta ta a zuwa Niger in wajen mutumin." "Ba matsala zan bada." Kallon Amina ta yi tare da cewa "Shikenan ko akwai wani abu.?" "Eh akwai" "Ina jinki." "Dama za'ayi bikin awata ce shi ne na ke so na canza sar ina da an kunne da su warwaro da zobe duk ina son a siya mani da gudunmawa da zan bata. Idan aka ha a jimilar ku in da na zuwa wajen magani Niger da hidimar bikin duka-duka jimilar ku in Naira miliyan biyar." Adamsy ya kalle ta da mamaki tare da cewa "Miliyan biyar da kika ce? Haba Amina wane..." "Babana ai bazai gagare ka ba, miliyan biyar ai ba komai bane a wajenka, kuma haihuwar nan ai kaina kana sonta, kuma a wajen bikin awarta zata so ace tayi bajinta, idan baka da halin ni daina cika mata Naira..." "A'a Umma ki barshi kawai zan bata." Nan ta dinga masa addu'a tana washe baki, dan yanzu shima lamarin Umman ya fara basa mamaki, da duk abunda Amina ta fa a mata ta zauna, bata ma bin ra'ayinsa Kallon Amina ya yi tare da cewa "Ki shiga dakina ki auko mani wannan akwatin silver colour." Cikin rawar jiki ta tashi dan ta san akwatin ku i ne ya ce ta auki. A can kuwa Kaduna Humaira duk ta damu da rashin waya da basu yi Adamsy ba. Kasancewar jiya da ya dawo biki a gajiye ya ke bata samu damar yin wayar ba, ballantana ta ji muryarsa. Dan haka karo na farko kenan da ta lalubo lambarsa ta danna. masa kira. Dai-dai lokacin da Kiran Humaira ya shigo wayar, Amina na jin karar wayar. Bayan ta auko akwatin ta ji wayar na sake ruri, arasawa ta yi kan gadon ta auko wayar tana duba mai kira. Zaro idanu ta yi cikin tsoro tare cewa "What?" Sunan da ta gani ne ya yi masifar aya daga mata hankali *my Happiness* cikin ta shi hankali ta saki wayar ta ke sai ta fa asa, har zuwa lokacin wayar bata daina ruri ba . Afusace ta nufi wayar . *_Masu cewa na dinga ara maku yawan pages, k yi ha uri abubuwa sai a hankali* *Daga la alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll Comments & share *ADAMSY* ~New blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai