← Book details Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 47

Sashe 6

Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da masifa. "Idan bata je ta yi tallar kokon ba ya kake so nayi? Ko kashe ka za'ayi baka da ku in da zaka bayar ayi cefene a gidan nan." Bayan Humaira ta hasa wutar ne ta auka tukunyar da zata ora ruwan koko. Kwanikan wanke-wanke ta fito dasu ta ha a a tsakar gidan inda suke yin wanke-wanke. Bayan ta kammala wanke-wanke ne sai ta share tsakar gida, Inna ta dama koko. Kallon Humaira tayi tare da cewa "Ki tafi akin Salma ki tayar da ita tayi shirin zuwa makaranta." akin Salma ta nufa ta tarar da ita tana ta sharar barci, da alama ko sallar asuba bata yi ba. "Salma Salma." Bugun afarta tayi a hankali, sai ta motsa tana yamutse fuska ta ce, "Ke ni sa'arki ce da zaki dinga kira na da Salma?" "To ai naga ba wani girma ya kikayi ba, wata aya kika bani." Inna dake tsakar gida ta jiyo muryarsu ta ce, "To rasa kunya ko kwana aya ne ai ta girme ki, dan haka idan na sake jin kin kira ta da Salma sai na fasa maki baki." Humaira dai fitowa tayi inda Inna ta ce, "Salma ki fito ke da zaki makaranta kada ki biyewa wannan da ba inda zata je sai zaman kashe zani." Humaira ce ta araso wajen tare da cewa "Inna dan Allah na dan ebi ruwan zafin nayi wanka da shi sanyi nake ji." Sanyin ya kashe ki wannan ruwan zafi na mai zuwa makaranta ne Salma ce zatayi wanka da shi, dan haka ki ebi ruwan randa kiyi da shi, sannan kizo ki auki koko ki fitar mani da shi." *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman arin bayani* 09065327995 Love you oll Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7 "Sanyin ya kashe ki, wannan ruwan zafi na mai zuwa makaranta ne Salma ce zata yi wanka da shi, dan haka ki ebi ruwan randa kiyi da shi, sannan ki zo ki auki koko ki fitar mani da shi." Haka ta ebe ruwan da ta ebo da asuba tayi wanka da shi, bayan ta fito ne ta shige aki da sauri-sauri saboda yanayin sanyin da ake ciki ga iskar da ke ka awa ga wanka da ruwa mai sanyi hakan yasa take jin sanyin. Bayan ta shafa mai ne dai powder ta sanya wata riga da zani ta atamfa, duk da cewar ta ko e amma a wanke suke tas ba alamar datti. Hijabinta ta auka tare da sakawa ta fito zuwa tsakar gidan dai-dai lokacin da Salma ta fito daga aki tana yamutse fuska da yin mi a kamar wacce tayi aiki ta gaji. Kallon Humaira tayi tare da cewa. "Ke ebi ruwan zafin ki shirka shi ki kai mani aki nayi wanka." Bata isa ta ce ba zatayi ba ko ta musa, dan haka ya bu e tukunyar ta zuba mata ruwan zafin ta kai mata ban aki. Bayan ta fito ne ta auki bokitin kunun kokon ta fita da shi zuwa ofar gida. Bayan ta ajiye ta dawo ne, ta auki wani bokiti da ruwa a ciki wanda zata dinga wanke robobin kunu idan wani ya shanye, ta auki robobin da ludayi kafin ta fita. Koda ta fita ta tarar da masu siyen kunun har sun fara zuwa suna jiranta, nan da nan ta fara saida masu kokon. Haka ya tashi da safe ba walwala a tattare da shi, ko Breakfast ma bai tsaya yayi ba ya nufi hanyar fita daga falon. Amina da ke zaune tana jiran fitowarsa dan suyi Breakfast ne taga zai fita, da sauri tasha gabansa tare da cewa "Ina kuma zaka je da sassafen nan haka?" "Fita zanyi." "Naga yau lahadi ba aiki ballantana ka ce kana sauri zaka fita zuwa wajen aiki." "Bana jin yinwa ne, kuma ina son na tafi gaida Umma." "Na ji zaka tafi gaida Umma, amma ka tsaya ko shayi ne ka an sha mana." Girgiza kawai yayi tare da cewa. "Bazan iya saka komai a baki na ba, dan bana sha'awar komai." Duk yadda ta kai ga lalla a Adamsy akan ya tsaya yayi Breakfast amma sam ya i amincewa, dan haka sai ta barshi ya fita ba don ranta naso ba. Kai tsaye gidan mahaifiyarsa ya nufa, inda ya same ta zaune a dinning room tana Breakfast, bayan yayi sallama ta amsa masa ne ta kalleshi ta tare da cewa. "Baba na kaine da sassafe haka?" ara sawa yayi saman kujera ya zauna tare da jinginar da bayanshi da jikin kujera ya lumshe idanunsa kamar mai yin barci, ganin haka yasa hankalin Ummansa tashi, dan tasan cewa idan ta ganshi haka to yana cikin damuwa ne. ara sawa tayi kusa da shi tare da tare da dafa kafa arsa, jinta a kusa da shi ne yasa shi kwantar da kansa saman cinyarta, har lokacin baiyi magana ba. "Baba na kayi ha uri ka rungumi addararka duk abinda kaga ya samu bawa to daga Allah ne, dan haka kayi imani da addararka ta alkhairi ko ta sharri, ba wanda ya isa ya canza abinda Allah addara faruwarsa, hakazalika ba wanda ya isa ya hana abinda Allah ya addara faruwarsa sai dai idan Allah ne baisa hakan zata faru." aarsa maganar tana mai shafa kansa, ta aura da cewa "Idan har ka yarda da abinda na fa a maka to yakamata ka cire damuwar da ke cikin zuciyarka, ka mi a lamuranka wurin Allah." Jinjina kai yayi tare da cewa. "To Ummana na ha ura ai." "Shine kake cikin damuwa?" "Damuwa ya zama dole Ummana na mata hu u fa ina aure kowace da irin tata matsalar ba wacce mukayi zaman mata da miji ko na kwana aya a tsakaninsu." Jinjina kai tayi tare da cewa "Na sani su dama can ba abokan rayuwarka bane, haka Allah yaso da kai, insha Allahu zaka samu abokiyar rayuwarka." Girgiza kai yayi tare da cewa "Umma ni hakura da zancen arin auren nan, wata kila ba rabin zan samu ganin gudan jini na ne." "Kada ka fa i haka kuma kada ka fitar da kanka da ragamar uban giji." "Umma na aukarwa kaina al awarin cewa idan har Allah yayi duniya dan Manzonsa to babu wacce 'ya mace da zan gani na neme ta da sunan aure." "Kayi gaggawar canza furucinka Baba na." Wayarsa ce tayi ringing zaro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba ganin ba uwar number ce yasa ya ajiye wayar bai aga ba. Har sai da aka kira sau uku sannan ya aga tare da cewa. "Hello wai wake damu na ne ka kira ba'a daga ba ai sai ka hakura haka nan ko?" Muryar mace ya ki ya daki dodon kunnensa, a hankali ta ce, "N kasa hakura ne shiyasa na nace sai ka auka ina fatan dai ban takura maka ba." "Gaskiya kin takura mani Wallahi." "To baka ma tambaye Ni wace ce ni ba ko?" "Dan Allah kiyi maganar da zakiyi mallama bana son takura." Murmushi tayi tare da cewa "Hauwa'u ce awar Fauziyya." Cikin mamaki ya ce, "Hauwa'u dai awar Fauziyya wacce aka fasa aure na da ita jiya?" warai kuwa nasan ka Sanni, dan munsha ha awa da kai a ofar gidansu Fauziyya mu gaisa." "Eh na gane ki to me yasa kika kira Ni?" "Abinda yasa na kira ka saboda na baka ha uri akan butulcin da Fauziyya tayi maka, dan na tausaya maka idan har zaka amince zan zame maka madadin Fauziyya." Da mamaki ya ce, "Ban gane zaki zame mani madadin Fauziyya ba." "Ina nufin zaka aure ni na zame maka mata kai kuma ka zama miji a gare ni." "Nagode da nuna mani auna, amma ki sani bana da sha'awar sake wani auren kuma." Murmushi tayi tare da cewa "Zan baka lokaci dai kayi shawar nan da kwanaki biyu zan kira ka naji shawarar da ka yanke, na barka lafiya." Daga nan ta katse kiran, Ummansa dake zauna ya ora afarsa akan cinyarta ne tayi murmushi tare da cewa "Babana da ka bata dama, tunda har ta nuna tana aunarka, a matsayinta na 'ya mace mai kima ta iya furta maka tana sonka to tabbas tana matu aunarka, kayi nazari akai, amma da zaka bi shawara ta Kawai ka amince mata ka aure ta." Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Umma kenan, amma tunda kin nuna kina so bazan i ta taki ba." Murmushi tayi tare da cewa "Allah yayi maka albarka ." Ta amsa da Ameen Kullun sai Hauwa'u ta kira Adamsy akan maganar soyayyarsu amma sai yayi biris da ita, har ta kai yau dai ya yanke shawarar zuwa gidansu. Tana zaune a falonsa ita da Mum inta da kannenta maza biyu, suna fira wayarta tayi ara a hankali ta juya ta kalli wayar sai taga Adamsy ne ke kiran wayar ta, ara zare idanu tayi cikin mamaki tana kallon mai kiran wayar, dan Adamsy bai ta a kiranta a waya ba sai yau, sai dai ita ta kira shi idan tava dama ya aga idan kuwa baiga dama ba bazai aga ba ko sau nawa zata kira shi, idanunta suka gaskata mata cewa lallai Adamsy ke kiranta wani tsallen murna tayi tare da yin ihu wanda ya janyo hankalin gaba aya jama'ar da ke falon, kallon mamaki suke mata tare da furta lafiya? akinta ta nufa da sauri ta turo afar. Amsa wayar tayi tare da fa awa kan gado ta ce, "Hellow, kaine ke kira na ko mafarki nake yi Murmushi yayi tare da cewa "Wane irin mafarki kuma?" "Na da e ina addu'ar Allah ya nuna mani ranar da zaka kira ni, hakan ya nuna cewa ka fara amsa tayin soyayya da nayi maka ne." "Kada fa ki za e dayawa" Bai ta a sakewa da ita sukayi fira ba sai yau, kuma taji da in
Chapter 6 · 0% Book details