← Book details Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 47

Sashe 7

Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakan sosai, daga arshe sai ya nemi ta turo masa address na gidansu, take ta tura masa zuciyarta fal da farin ciki. Bayan ta gama ne ta fito falon inda tabar Mum inta da kannenta, kalli aya Mum inta tayi mata taga yadda take cikin farin ciki, dan haka ta ce, "Me kika samu ne haka na farin ciki?" "Mum dole ki ganni cikin farin ciki, mutumin da kullun nake kiransa sai yaga dama yake auka duk na shiga damuwa akansa, kwatsam yau rana ta farko ya kira ni, sannan ya nemi da na bashi address na gidanmu gobe zaizo." Cike da takaicinta Mun inta tayi tsuki "A matsayinki na 'ya mace ke ce zaki dinga bibiyar a namiji ba shi zai dinga bibiyarki ba? Ina abinki naki yake mace da aka sani da alkunya gaskiya kin bani takaici wane irin namiji ne shi haka?" Mum wallahi tausayinsa nake shine fa wanda ranar da za'a aura aurensa da Fauziyya ta ce, bata sonsa." "Yanzu tsohon mijin aawarki kike so kenan, dama can kina sonsa ko?" "To dama tun farkon gani na da shi ya burge ni, amma ban ta a tunanin wani abu game da shi ba da naga awata ta wula nata shi a ranar da zasuyi aure, kuma kanta tayiwa dan wallahi ya ha u Mun baki ganshi bane fari ne dogo kuna kyakkyawan arshe, ga lafiyayyen sake da yayiwa fusakarsa awanya da kin ganshi kin..." Mum in ta ce ta katse ta hanyar cewa "Dalla rufe mani baki, kamar ni ina Mahaifiyarka sai ki zauna kina zayyane mani siffar irin na namijin da kike so? Saboda baki da kunya ko?" Sunkuyar da kamata tayi tana dariya ta ce, "Mum ke fa kika tambaye ni..." "Ni ban tambaye ki fiffofinsa ba, sannan kibi a hankali, ba kyawun siffa ko kyawun ira ake so ba a'a kyawun hali ake bu ata " "Eh har kyawun hali yana da shi." "Kin zauna da shi ne?" Girgiza kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba. Washe gari kuwa kamar yadda Adamsy yayiwa Hauwa'u al awarin zuwa gidansu kuwa sai gashi ya zo, murna a wajen Hauwa'u ba'a magana kamar ta zuba ruwa asa ta sha take ji sun ta a hira inda yake bata labarin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwar sa na dangane da aure-auren da yayi ne, har zuwa yau ba abunda ya oye mata ya nuna cewa idan zata soshi a haka ba matsaka shikenan. A cikin wata aya aka gama komai na dangane da auren Adamsy da Hauwa'u, inda biki ya rage saura kwana bakwai ana ta shiyrye- shirye daga kowane angare. Ana gobe aurin aurensu ne da misalin arfe biyu na dare sai ga awayen amarya sun fito a guje daga akin amarya, saurin rufe ofar sukayi ta wace yayin da sai kwaramniya da sautin fashewa abubuwa da ake tarwatsewa. Kai tsaye bedroom in Mum suka nufa, cikin tashin hankali suke bubbuga ofar suna kuka. Cikin barci Mum in Hauwa'u da annen mahaifinta da ke kwance a akim Mum suma sunzo daga Abuja, jin arar ofar na tashin hankali yasa suka farka a firgice da sauri Mum in ta ta tashi suma suka biyo bayanta, bu ofar tayi tare da cewa "Ku lafiya daddaran nan me ke faruwa ina asar taki." aya daga cikin awayen amaryar ne ta fara kuka sosai tana cewa "Mun Hauwa'u ta haukace." "Ke wai ni sa'arki ce da zaki ce mani 'yata tilo ta haukace? Ina take ne?" aya daga cikinsu ta aura da cewa "Wallahi ta haukace tuburan tana ta fashe-fashe har da dukanmu wallahi da yar muka sha a hannunta, shiyasa muka zo fa a maki gata can mun rufe ta a aki." *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM* Page9 Wallahi ta haukace tuburan tana ta fashe-fashe har da dukanmu wallahi da yar muka sha a hannunta, shiyasa muka zo fa a maki gata can mun rufe ta a aki. Cikin tashin hankali Mum inta ta nufi akin Hauwa'u, ta tura kofar wayam bata ga kowa ba,sai ta ji motsi a bayan ofar ta waiga da sauri taga Hauwa'u kanta a warwatse ga kayan jikinta duk ta yayyage su hatta pant inta ana gani. Mum inta ta fashe da kuka tare da rungume ta a jikinta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hauwa kece haka na shiga uku na..." Kasa arasa maganar da tayi niyyar yi tayi sakamakon wani ra in azaba da ta ji, lokacin da Hauwa'u ta gantsara mata wani masifaffen cizo a damtsen hannunta iya arfinta, ara Mun inta ta saki wanda ya janyo hankalin gaba aya ilahirin jama'ar da ke cikin gidan. Cikin hanzari kowa ya nufi cikin akin, da yar aka are bakin Hauwa'u daga damtsen hannun Mum inta, sai jini ke tsiyaya daga hannunta, ga shaidar cizon nan sunyi zurfi sosai lokacin da aka are bakin daga hannun Mum inta sai da kowa dake wajen yayi mamakin irin wannan cizon. Hajiya Talatu awar Mum ce ta kalli wata mata dake gefenta ta ce, "Maman Fahad dan Allah kuje ki duba ta kiyi mata duk abinda ya dace." Maman Fahad wata awar Mum ce da take aiki a asibiti , ta ja hannun Mum suka fita tare ta nufi akin Mum da ita. Abun a da uwa, ita kuma Mum ba ta cizon da Hauwa'u tayi mata bane ke damunta a'a halin hauka da 'yarta ke ciki ne ya fi daga mata hankali matu Bayan fitar su Mum ne sai kawai Hauwa'u ta janyo hannun wata awarta tayi tare da kai mata duka ta ko ina, da yar aka wace ta dan yanzu wani arfi ne na ban mamaki Hauwa'u ke da shi, kamar na arfinta ba, mutane kusan su biyar amma ta rinjaye su da yar suka iya dakatar da ita daga dukan awarta da take . Fita suka yi suka barta ita ka ai a akin suka rufe ta ta waje. Kasancewar dare ne a lokacin kusan arfe uku saura kwata ne a gidan ba wanda ya iya yin barci daga masu kuka sai masu alhini. Mum kuwa kwana tayi tana kuka duk yadda aka dinga rarrashinta abu ya ci tura gaba aya ta kasa daina kukan haka suka yale ta. "Ya kuke so na yi idan banyi kuka ba, yarinyar nan bata da mahaifi ni nake kula da su da ranta da lafiyarta lokaci aya ranar jajibirin aurenta ace ta haukace lokaci guda ni fa da kaina na shiga akin da na ji hayaniyarsu tayi yawa na ce arfe goma sha biyu tayi su kwanta suyi barci, har tana ce mani sai da safe sun daina fitar a cikin awa biyu da rabuwa ta da ita ta haukace tuburan har da dukan mutane." arasa maganar cikin kuka mai cike da cin rai, nan aka dinga rarrashinta inda Hajiya Talatu ta cigaba da cewa "Kinga addu'a zaki yi mata Allah ya yaye mata, sannan wannan auren da za'a aura gobe a dakatar da shi har sai ta samu lafiya, a kaita asibitin da ake kula da masu lalurar walwa ayi mata magani, idan Allah yasa komai ya dai daita sai a daura auren." Jinjina kai Mum tayi tare da cewa "Shikenan hakan za'ayi yadda kika ce." Washe gari da safe ne awayen Amarya suka watse kowa tayi hanyar gidansu, wacce Hauwa'u tayi wa duka kuwa jikinata yayi kumburi musamman fuskarta, gefen idanunta ma aya a kumbure bata gani da idanun sosai. An ha a Breakfast masu aikin gidan ba wanda ya nufi dinning area ballantana yayi breakfast. Umma ce ta dauki kofin shayi dan zuwa ta kaiwa Hauwa'u ko zata sha, tunda tasan ko tana jin yunwa ba zata iya magana ba, dan haka ta nufi akin Hauwa'u da kofin shayi a hannunta. Tura kofar tayi zata shiga sai taji muryar Hajjo anwar Baban Hauwa'u ta ce, "Nifa ina tsoron ki shiga akin nan bansan kuma abinda zata aikata maki ba." Murmushin takaici tayi tare da cewa "Wata uwa ce zata guji 'yarta a duk halin da 'yar ta tsinci kanta?" Daga nan bata sake magana ba ta kutsa kai cikin akin, ta same ta tana ta safa da marwa a dakin, a hankali Mum inta ta tari gabanta tare da sakar mata murmushi ta ce, "Hauwa'u?" Dakatawa tayi tana kallon Mum kamar taga sabon halittar da nata ta a ganin mai kama da ita ba, mi a mata kofin tayi da niyyar kaiwa a bakinta sai ta buge kofin ya fa i ya tarwatse asa, sai ta du a zata auki fasassaun kofin Mum tayi saurin ri e mata hannu nan suka dinga kokawa da ita har Mun ta fa asa dai-dai lokacin da Hajiya Talatu suka shigo tare da wasu mata guda biyu, tayar da Mum sukayi inda Allah ya taimaka na bata yi muguwar fa uwa ba. Ganin yadda take daga ita sai bra da pant ne yasa Hajiya Talatu nufar drawar kayan Hauwa'u, ta auki nata wani riga doguwar ta abaya tare da dogon wando da zasu sanya mata a ciki. Ganin yadda ta tu e kayan jikinta ya saura daga ita sai bra da pant bayan aya daga cikinsu ta kwashe kofin da Hauwa'u bata fasa ta gyara wajen. Sai da suka nemi taimakon wajen mata biyu suka zama su biyar tukun sannan suka fara saka mata kaya, da yar ta bari suka saka mata kayan jikinta amma sai kawai suka ga tana arin yaga kayan ne suka ri e mata hannu ta kasa cire kayan jikinta Nam aka dinga kokawa da ita dukkansu mutum biyar in nan sai da ita ka ai ta kwaci kanta daga hannunsu hakan yasa suka fita tare da janyo mata dakin suka rufe suka zare key suka tafi da shi. Mum intac ta auki wayar tare tare da kiran wayar
Chapter 7 · 0% Book details