Sashe 17
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rungume juna suna dariya fuskar kowannensu auke da farin ciki. Bayan sun zaune ne Abdallah ya ce, "Na yi farin ciki sosai da dawowarka nan. Fatan dai komai lafliya ya Umma da madam?" "Duk suna lafliya." "Ai na auka tare da Madam kuke." Kai ya girgiza tare da cewa "Ni ka ai ne." "Amma da ka zo da ita, ta ya ya mai mata zai koma gwauro?" "Abdallah ina da damuwa ne, kuma ina bukatar na ga na ka aice ni ka ai ba tare da kowa ba." "To kuwa ka aici ba abunda zai haifar maka face yawan tunani da damuwa." Ajiyar zuciya kawai kawai Adamsy ya sauke inda Abdallah ya cigaba da cewa "Wai yanzu matayenka guda nawa ne?" Harara ya gallawa Abdallah sannan ya ce, "Ban sani ba." "Sorry friend ka san na je dai aurin aurenka sau uku, bayan su ban sake zuwa ba, kuma ko wanda ban je ba na san zasu kai uku. Yanzu duk kana nufin ba ko aya a gidanka?" "Wai me ya haka Abdallah akwai sanin kanka ne cewa ba abinda na oye maka, duka matayen nan da ka sani ba wacce mu ka yi zaman aure da ita, wasu a ranar aurin auren ake fasawa guda biyu ne aka kawo su gidan suma zamana mintuna uku banyi da su a aki aya ba." Tsuki ya ja tare da cewa "Dan Allah Abdallah ka daina dawo mani da abinda ya wuce, shi ya sa na dawo garin nan dan bana son na dinga tuna baya." Shiru ya yi tare da cewa "Ka yi hakuri Adams, na san yadda kake ji ace ka auri mata sama da guda biyar ba wacce ta zauna da kai? Gaskiya wannan abun ba banza ba akwai wata a asa. Dan duka auren soyayya kuma yi da su ballantana a ce ko dan basu sanka ne , kuma akasarinsu sune suka fara neman soyayyarka kaga kuwa karshen so kenan, tunda har mace zata iya cire kunya da bayyana maka irin son da ta ke maka, rabuwa da mai ba abu bane mai sau in a gare ta. Dan haka ka bincike lamarin nan amma ruwa baya tsami banza." "Koma dai me ne ne ya zo arshe bani ba sake auren jinsi wata 'ya mace." Abdallah zai yi magana kenan sai Adams ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Kana fama mani tabon da ke zuciyata ne,dan Allah wannan maganar ka auke shi ka yi jira da shi baya kada ka sake waiwayarta." Jinjina kai Abdallah ya yi tare da cewa "Shikenan tunda haka ka ce." "Ina madam da kuma yara?" "Duk suna lafiya suna gaishe ka." "Masha Allah Ina amsawa." Daga nan fira suka cigaba da ta a wa inda har Abdallah ke cewa "Ina ka samo wannan mai gadin ne, yana da hankali da kamala." "Manaja ne ya sa aka kawo shi, nima dawowa ta na tarar da shi. Daura na sa a nema mani mai wankin motoci da bawa fulawa ruwa." "Wannan kam ba matsala ba ne a yau aka nema za'a samu." "Ga abinci nan fa ka ci ga abun sha " Girgiza kai Abdallah ya yi "Am okay." Adamsy ya kalle shi ya ce, "Bari na mi awa mai gadin nan abinci." aukar leda aya ya yi na takeaway da robar ruwa da na lemu ya kai wa Mallam Musa. Malama Musa ya ji dad'in hakan sosai. Humaira na komawa gida kuwa ta tarar da Inna Habi sai zazzaga mata masifa ta ke yi. "Wato ke da uwarki daga kan kije ki wa ubanki rakiya shine kika je kika shantake ko?" "Kiyi hakuri Inna unguwar ce da nisa." Dariya ta yi tare da cewa "Albishirinki, daga yau zaki fara tallan tuwon dare." "Tuwon dare kuma Inna?" warai kuwa dama na san ubanki bazai bari bane shi ya sa ban yi ba, amma yanzu tunda baya nan, yau zamu fara." Kallon Inna Habi ta ke baki sake wato ita dai bata da lokacin hutu, da asuba ta je ibar ruwa da safe tallan koko, da rana tallan doya sannan ga dare kuma tallan tuwo. Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, ganin haka ya sa Inna Habi ta ce "Au kuka kike yi?." Gadan-gadan ta nufi inda Humaira ke tsaye ta daga hannu ta sauke mata tagwayen maruka biyu, sannan ta cigaba da jibgarta tana ihu tana neman taimako, ba mai taimaka mata. Sai da ta mata lilis da duka sannan ta barta. "Ki ta shi ga wanke-wanke can ki wanke su tun azu suke jiranki." ayar ta iya tashi ta nufi wajen da aka jibga kwanikan wanke-wanke sannan ta bu e randa da niyyar ibar ruwa da za ta yi wanke-wanke da su ta ji an daka mata tsawa. "Ke!" Da sauri ta juya tana kallon Inna Habi wacce ta saka mata tsawar. "Kada ki kuskura ki ebi ruwan gidan nan, sai dai ki je can rijiyar ofar gidan Barumi ki abo ruwa." A hankali ta ke tafiya dan jikinta ciwo ya ke mata, ga wurin da ta one da wuta ranar da Inna Habi ke dukanta da itacen wuta, ta kone ta a gafen ciki kuma har yau tana jin zafin wurin. A haka ta fita ta yi tafiya mai an tsayi sannan ta arasa rijiyar. Guga ta auka ta zura cikin rijiyar, zata jawo kenan sai taga an janyo mata, aga kai ta yi dan ganin waye. Salman ta gani tsaye yana kallonta yana murmushi. "Je ki zauna ko huta zan ebe maki ruwan." Jan gugan ta yi tare da cewa "A'a ka barshi zan iba da kaina." srasa maganar tana tsuke fuska, dan ta lura da takensa yana yawan shiga lamarinta. Haka suka dinga jayayya da shi, da ta ga alamar ba zai barta ba, kuma zai ata mata lokaci ta sake shan wani duka, hakan ya sa ta sake masa gugar ya dinga janyo ruwan yana zuba mata har bokitin ya cika. auka tana shirin orawa a kanta ya yi saurin auka ya ri e a hannunsa. Sanin cewa ba bata zai yi ba yasa ta bin bayansa, yana ri e da bokitin a hannunsa. Haka ta cigaba da rayuwa cikin unci da ba in ciki. Kullun arfe hu u na asuba zata tashi, idan bata Inna Habi ta kwara mata ruwa, dole ta farka. Ta tafi aban ruwa bayan ta dawo ta yi sallah zata fara sharan gida da wanke-wanke idan kayan Salma da Habi sun taru ita zata wanke ta masu. Sannan ta dama koko ta tafi talla, idan ta siyar ta dawo ta wanke kayan da ta dasu robobin da ludaya. Sannan zata fere doyar da zata tallah da rana, bayan ta dafa ne ta yi wanka zata tafi talla. Kuma ko ta dafa doyar Inna Habi shi zata ci da rana, Salma ma shi zata ci amma ita ko yanka aya na doyar ba za'a bata ba, hala za'a lissafa mata idan kuwa ku aya ya ace sai ta sha duka kamar za'a kashe ta. Idan ta dawo tallar doyar ba abinci wata rana Inna zata ce mata wai ta bari sai an gama abincin dare sannan ta ci, wata rana a ce ta a ce ta siyo gari ba sugar ta sha. Sannan ta fara shirin zuwa tallar tuwo bayan sallar magrib. Tunda Mallam Musa ya bar gidan shikenan komai ya sake tsanani ga Haumaira, Salma kam ta sai iko da mulki ta ke nuna wa Haumaira, dan sai abinda ta ce da ita. Kuma duk aikin da ta saka ta bata dole sai ta yi mata shi. Mallam Musa ma yana samun alkhairi a wajen Adamsy dan sosai ya ke bashi kyaututtukan ku e, ba wai sai albashi ba. Wata rana Humaira ta dauki tallar doya ta fita, tana tsaka da tafiya kafin ta kai bakin titi tsautsayi wasu samari su biyu a saman mashin sun gudu suke zaubawa, jin sautin mashin in yasa Humaira ta waiga, tana waigawa kafin ta ankare sun ka e ta da mashin in ta fa i a wajen robar doyar ta farfashe. Wanda aka goya a bayan ne ya cewa na gaba "Kayi sauri mu gudu" Dan haka suka gudu suka barta kwance a wajen. Wata mata ce da zuwa ta hange sanda suke wucewa da gudu ta araso ashe ma ta san Humaira. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Humaira zaki iya tashi kuwa?" Hakan ya sa ta yun ura da taimakon matar ta tashi. Ganin yadda robar doyar ya ragargaje ne matar ta ce tabar shi tunda ga doyan duk sun watse a asa. yar ta ke tafiya har suka arasa gidan, da sallama suka shiga, Inna Habi har ta bu e baki zata amsa ganin yadda aka shigo da Humaira ba doya sai ta sura wata irin ashariya. Jin haka ya sa Humaira ta ame matar tana kuka, ganin haka ya sa matar ta dinga ba wa Inna Habi ha uri. Murmushin ya e Inna Habi ta yi ta nunawa matar ba komai, har matar ta yi godiya ta tafi. Bayan fitar matar ne Humiara ta korawa Inna Habi bayanin abinda ya faru ta kuma bata ha uri tana kuka. Kukan kura Inna Habi ta yi tare da yowa cikin Humiara a yarda ita asa ta haye saman cikinta ta fara dukanta. Humaira na ihu sosai tana bata ha iri amma ina, bata saurare ta ba, ma ota suna ji amma ba halin su shigo, dan ko sun shigo ma Inna Habi cin mutuncinsu ta ke da zagi, dan haka kowa ya fita harkarta. arshe sai da Humaira ta suma a hannun Inna Habi, da ta ga bata motsi ne ta aya d'aga ta. Ruwa ta ebo ta yayyafa mata a jiki sannan ta farfa o.kuka ta ke sai har idanunta sun kumbura saboda naushi da ta sha a idanunta bakinta ma ya fashe. "Tashi ki je ki nemo ku i ki biyani ku in doya na." "Inna Ina zan samu Kudi wallahi ban dan inda zan samo ba." "Na fa a maki yadda za ki samu?" Kai ta gya a mata alamar eh. Dan haka sai ta ce mata "Ki je ki yi karuwanci ki kawo mani ku ina." Da sauri ta kalli Inna Habi ta ce, "Karuwanci?" "Eh haka na fa a ko ke