Sashe 26
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya yi dan auro alwala tunda dama masallaci za tafi. Da misalin karfe takwas da rabi na dare tana kwance saman sallaya bayan ta idar da sallar isha'i. Turo ofar ya yi ya shigo bakinsa auke da sallama. "Assalamu alaikum" Shigowa ya yi cikin akin inda ya hange ta kwance bisa sallaya, dur usawa ya yi ya janye hijabin da ya lullu e mata fuska, wanda hakan ya sa ta farka. A hankali ta tashi zaune tana kallonsa, ganin yadda shima ya zuba mata idanu ne ya sa ta an fara ja da baya, dan har yanzu akwai sauran tsoronsa a cikin zuciyarta, musamman ganin yadda ya zuba mata idanu wanda idan ta kalli idanunsa dai ta ji ya mata kwarjini da yawa . "Barci kika fara tun yanzu?" Sunkuyar da idanunta asa ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Tashi mu je ki ci abinci." "Na oshi" "Bana son gardama" Tashi ta yi tsaye ya zare mata hijabin ya ajiye, hannunta ya ri o cikin nasa wanda jin hakan ya sa ta fara arin zame hannunta daga nasa, amma bai bata damar hakan ba sai ma kare ri e hannun nata da ya yi. Falo suka nufa inda ta hangi wani matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da biyar, yana zaune a saman Centre carpet. Ido ya zuba masu yana kallonsa zuciyarsa cike da tambaya, shi dai ya san Amina ce ka ai matar Adamsy wanna kuma fa, ko dai za man dadiro suke yi ne da wannan yarinyar. Kamar Adamsy ya san zancen da Mustapha ke yi a zuciyarsa, kamar daga sama Mustapha ya ji muryar Adamsy na cewa "Matata ce." Sunkuyar da kai kawai Mustapha ya yi cikin jin kunya dan ya auka Adamsy ya ji zancensa ne. Har suka araso suka zauna akan kujera bai daga kai ba, sai da ya ji muryar Adamsy na cewa "Mustapha ina son ka saurare ni." A hankali ya ago kansa tare da cewa "To yalla "Wannan ita ce matata kasan dai aikinka ba sai na fa a maka ba, kasan yadda kake komai ba sai na fa a maka ba, abu guda ne zan sanar da kai cewa wannan ita ce matar gidan, wajibi ne ka yi biyayya a gare ta ta hanyar bin ra'ayinta,duk abinda ta bada umarnin a girka shi zaka yi indai ba ita ce ta baka za i ba." Jinjina kai ya yi tare da cewa "In sha Allah." Maida dubansa zuwa ga Humaira ya yi tare da cewa "Duk abunda kike bu ata shi zaki sanarwa ya girka maki, aikinsa ne ba kuma ba wani nau'in girki da bai iya ba tun daga na gargajiya har na zamani, bama iya na asarmu Nigeria ba harda na asashen waje ya iya." Ita dai Humaira mamaki ne ya kamata,wai namiji ne ya iya girki haka, har Adamsy ya gama bayanin da zaiyi sannan ta ce "To badamuwa." arasa maganar tana hamma alamar bacci ta ke ji, Adamsy ya kalli Mustapha ya ce "Zaka iya tafiya idan Allah ya kaimu gobe da safe zaka fara aiki." Sallama ya masu ya tafi. Adamsy ya kalli Humaira da ke ta yamma cak ya aya d'aga ta ya nufi dinning area da ita. Cewa ta yi ba zata ci abinci ba sai da ya lalla a ta ta an ci ka Tashi ta yi ta nufi hanyar akinta, dai-dai lokacin da kiran abokinsa Sadik ya shigo wayar. agawa ya yi tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaikumus salam" "Wato ka ji da in Kaduna ka mance da mutane ko?" "Wane ni ai ba'a mance mutanen swarai irinku." "Haba Mallam kwana biyu ba slm waya shiru mai mutanen Kaduna suka baka ne ka mance da mu kake cikin farin ciki?" "Ba komai" "Ina wallahi akwai komai, nafa sanka farin sani, idan kana cikin farin ciki a maganarka na ke ganewa, haka ma idan akasin haka ne, ka fa a mani me ya saka farin ciki ne ye sirrin?" "Ba wani sirri kawai na za i kullum na kasance cikin farin ciki da walwala ne dan ina arin mance abubuwan da suka faru dan..." Dariyar Sadik ne ya katse masa maganar da ya ke yi, sai da ya yi dariya mai isarsa kafin ya ce, "Daga jin maganarka ba gaskiya ka fa a ba, dan baka iya karya ba da zaran kayi ta sai an gane, dan ba abi'arka bace. Kuma iya sanina ba abinda kake oye mani yanzu zaka fara." "Ba wani abu da nake oye maka ka yarda da ni." "Shikenan tunda haka ka ce, dama na mance ban sanar da kai ba, ranar Asabar aurin auren Jamil." "Yanzu har auren ya zo nan da kwanaki hu u sannan ka ke sanar da ni?" "Afuwan wallahi na sha'afa ne abubuwa sun yi mani yawa." "Ba damuwa zan shigo Katsina aurin auren ko kwanaki biyu na yi na dawo." Fira suka dinga yi har tsawon mintuna talatin daga bisani suka yi sallama ya katse kiran wayar. Bayan ya gama shirinsa na kwanciya barci ne ya ji bazai iya kwanciya ba tare da ita ba, dan haka kai tsaye ya nufi akinta. Koda ya shiga akin har ta yi barci amma bata kashe hasken akin ba. Kai tsaye ya nufi gadon hannu ya kashe hasken akin, janyota ya ya mata masauki da faffa irjinsa, wanda hakan ya sa ta farka, tana ganinsa ta saka masa kuka, cikin tashin hankali ya ce, "Me ya faru?" "Bakomai dan Allah ka yi hakuri wallahi akwai zafi har yanzu ban daina jin zafi ba ciwo ya ke Mani." Daina kuka ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki, aya sai kuka ta ke dan tsoronsa ne ya dawo mata, gani ya ke kamar abinda ya kawo shi kenan, ganin bata da niyyar daina kuka balle ta fahimce shi ya sa magana da an karfi. "Ko ki mani shiru ki daina wanna kuka ko kuma na maimaita abinda baki so na ga mai hanani, ko kukan jini zaki yi idan na yi niyya sai nayi dan haka idan har kina son na yale ki gara ma ki yi shiru ki kwnata na yale ki, idan kuma kika i jin magana ta kika cigaba da kuka sai nasa ki yi mai dalili." Ganin ba wasa a fuskarsa ya sa ta yi shiru ta daina kukan, dan ta san tabbas yanzu kukan nata ba dalili kada ya sa ta mai dalili kamar yadda ya fa Janyota ya yi ya kwnatar a jikinsa ya tofa masa addu'ar kwnaciya danna ya ja masu bargo ya yin da ya mata filo da irjinsa. Gabanta bai daina fa uwa ba amma bai ce da ita komai ba dan ya lura a tsorace ta ke, ba jimawa barci ya auke shi yayin da ita kuma ta kasa barci, zuciyarta cike da fargaba saboda sabon al'amari ne wanna a gare ta na kwanciya jikin mutum. Ta jima kafin barci ya auke ta. Da asuba ya ya tashi ya nufi bathroom ya yo wanka tare da auro alwala, gefen fuskarta ya shafa ta bad'e idanunta a hanakali. Murmushi ya sakar mata tare da cewa "Ta shi lokacin sallah ya yi sarauniyar tsoro." Masallaci ya wuce yayin da ta tashi ta nufi bathroom. Ba shi ya dawo ba sai arfe bakwai saura kwata. Ganin tana barci ya sa ya koma akinsa . Da misalin karfe tara na safe ta yi wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa, mai da powder kawai ta shafa ko an kwali bata aura ba ta fito zuwa falo, yana zaune a kan kujera yana danne-danne a computer amshin turarenta ne ya sa ya dago ya kalle ta, sunkuyar da kanta ta yi dan kwarjinin da ya ke mata, harta arasa kusa da shi ta dur usa tare da cewa "Ina kwana ." "Barka da tashi kin fito sarauniyar tsoro." arasa maganar yana jan hannunta ya zaunar da ita kusa da shi, kuma yana sarrafa computer da ayan hannunsa. Wayarsa ce ta soma ruri, ya duba ya ga Ummana ne sunan da ya bayyana. agawa ya yi tare da cewa "Barka da safiya Umana." Daga can angaren ta ce "Yauwa Banana kq tashi lafiya?" "Alhamdulillah . Na ji matarka ta ce wai aka zo ranar juma'a nan da kwana uku kenan ko?" "Eh Umma Jamil an yayan Baban abokaina zai yi aure, zan zo daurin auren." "Wani abokinka Sadik ko wa?" "Eh Umma shi, idan na zo juma'a zan koma ranar Lahadi." "Kwana biyu kenan zaka yi" "Eh Umma" "Kwana biyu ai ya yi ka an yaushe aka gana biki ka zauna tare da matarka da kwanaki bata saka ka a idanu ba." Gaban Humaira ne ya fa i ta kalle shi da sauri, jin yana da wata matar, ta ke sai ta ji ba da i, ta rasa dalilin hakan. "Umma ai monday ina da aiki shi ya sa zan yi kwana biyu." "Ai kaine shugaba a wajen aikin ba matsala amma kam dole ka yi ko da sati guda ne ko kwanaki goma." Bazai iya jayayya da ita ba dan haka ya yi shuru, yana kallon Humaira wanda itama tana jin *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ne, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowa ce siga ba tare da izinina ba. GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi