← Book details Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 47

Sashe 11

Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta yadda akayi hakan ta faru ba yanzu zan fa a maki ba sai dai zan fa a maki dalilina yanzu." Kamar yadda kika sani dai suna na Hanne na taso da son abun duniya da kwa ayin ku i. Sau uku ina aure yana mutuwa kasancewa ta bani da ha uri musamman da talauci bani da ha urin talauci dan haka idan naga bana samun inda zan huta sai na kashe auren. Wata rana ina zawarci bayan na haife ki da kwana arba'in na fita ziyara gidan awata kasancewar da cikinki na fito gidan tsohon mijina to da na yi kwana arba'in sai na je ziyarar akan hanya ta dawowa gida hadari mai arfi ya taso lokaci guda, sauri-sauri gudu-gudu na ke yi a kan hanya sai ga ruwa ya alle mai karfi ina cikin wannan halin sai na ga wata tsadaddiyar mota ta tsaya a gaba ba, kasa motsawa na yi illa kawai na zubawa mamallakin motar idanu domin kuwa idanunsa kasa daina kallonsa yayi sai na mance da ruwan da ke duka na sai da na ji muryarsa yana cewa wai bana jin ruwa ne na shigo ya rage mani hanya. Hakan yasa na shiga tare da masa kwatancen unguwarmu, na saki jiki muka dinga fira sai da ya ji kukan jaririya da na goya ne ya ce wai ni matar aure ce na ce A'a sai yayi da dariya tare da cewa ashe Masha Allah yana fatan ni budurwa ce sai na ce bazawara ce ni, ganin ya canza fuska ne kamar baiji da i ba na ce masa ni budurwa ce. Daga ranar muka kulla soyayya yana gudun kada ya gane ni matar aure ce yasa na auke ki kina jaririya ranar da kika cika kwanaki arba'in da biyar na cire ki daga nono na kaiki wajen yayata Karima na nuna mata cewa na samu wanda zan aura kuma na fahimci budurwa yake so don haka ta cigaba da ri e ki a hannunta tana shayar da ke madara da aka bawa jariran da suka rasa nonon uwa. Kasancewar daga ni sai maihaifiyata ce a gida yaya Karima tana gidan mijinta tana kula da ke har aka saka ranar aure na da Alh. Muhammad Adam yana da mata aya sunanta Zainab suna da a guda aya sunansa Adamsy, wato mijinki kenan.Har aka saka ranar aure na da da shi na dinga arin gyara dan kada ya gane cewa ni bazawara ce har na haihu, har inki nayi da maganin budurci dan gudun zargi. aura aure na da shi an kaini gidansa inda na same shi da matarsa aya da yaronsu Adamsy wanda lokacin shekarunsa biyu da watanni. Ganin irin soyayyar da Alh. Muhammad ke nunawa ansa Adamsy yayi yawa hatta gidaje da filaye kawai sai ya siye da sunan Adamsy ya mi awa mahaifiyarsa, duk da cewar Zainab mahaifiyar Adamsy bata da matsala tana nuna mani auna bata auke ni kishiya ba sai 'yar uwa kullun da alkhairi take bina yayin da ni kuma nake da wata ulalliya akanta sai dai idan har ina son burina ya cika sai na da taimakon Adamsy dan haka na jashi a jikina arshe ya koma akina da kwana kayansa sawarsa kayan wasansa komai nasa yana wuya na, har mahaifiyarsa da mahaifinsa suke kira na da Umman Adamsy har aka saka sa makaranta ni nake masa komai da uwa ke wa ansa. Hatta dangin Alh. Sai kira na suke da Umman Adamsy ganin yadda na maida shi tamkar an da na haifa a cikina, har lokacin ba wanda yasan na ra a aure a danginsa da gidansa.Yaya Karima da ke ri e da ke mijinta ya samu canjin wurin aiki zuwa Bauchi dan haka hankalina ya fi kwanciya sosai.Haka rayuwa tayi ta tafiya Adamsy ya fara wayau har yakai shekaru goma baisan cewa ba ni ce mahaifiyarsa ba kuma har lokacin ban samu ciki da Alh. ba ga shi arzikinsa sai bun asa ya ke yi ka tarin kadarori kuma duk rabin dukiyarsa ya mallakawa Adamsy. Wata rana Alh.yayi tafiya zuwa Abuja akan hanyarsa ta dawowa yayi hatsarin mota Allah ya masa rasuwa, bayan mun kammala takaba ne naji danginsa suna maganar rabon gadonsa, kasancewar Adamsy ne ka ansa da ya haifa ne shi zai gaje duk dukiyarsa nikam sai dai su bani tumunin takaba shikenan tunda ban haihu da shi ba, duk da cewar kowa na kallon kamar ni ce na haifi Adamsy mahaifiyarsa da danginsa ne kawai suka san cewa ba ni na haife shi ba. Hankalinsa ya tashi ganin cewa Adamsy ne kawai zai gaje dukiyar mahaifinsa kuma mahaifiyarsa za'aba kasonsa dan haka na yanke shawarar kawar da ita daga doron asa dan ita ce zata mani shamaki da dukiyarsa. Dan haka na kar i magani wajen boka domin na kawar da ita ya zama daga ni sai shi, ba wacce zata gaji dukiyarsa sai ni, hakan kuwa aka yi bayan ta mutu ya zama ba wacce zata mani shamaki da dukiyarsa dan dama saboda dukiyar na shigo gidan. Nayi ta kukan mutuwarta har da sumar arya na fita hayyacina kowa sai da ya tausaya mani na cigaba da ri on Admsy da dukiyarsa yana da shekaru ashirin a duniya dangin mahaifinsa suka mallaka masa dukiyar komai da komai wanda banso hakan ba na so a ce ni ce suka dam awa komai kafin yayi wayau, amma duk da haka baisan cewa ba ni bace na haife shi kuma ba wanda ya fa a masa yana kyautatawa a gare ni da mani biyayya baya tsallake magana ta lokacin da ya kammala karatu ne ya fara gudanar da kamfanonin mahaifinsa a lokacin ne kuma ya tsiro da zancen aure yana da shekaru ashirin da ashirin da tara, inda hankalina ya tashi idan ya auri wata mace ta samu ciki ta haihu to duk abinda ya mallaka zai zama mallaki matarsa da ansa, dan haka sai na yanke shawarar tunda ina da 'ya wacce na haifa ai ita zanyi amfani da ita nasa shi ya aure ta dan mu mallake dukiyar ni da ita. Daga nan ne na kara yaya Karima ta sa aka kawo ki na nuna masa cewa ke 'yar yayata ce na bashi umarnin ya aure ki, kasancewar yana mani biyayya baya etere zance na yasa ya aure ki, sai dai kash ke baki haihuwa kuma shi ya kasa kwantar da hankalinsa sai neman wacce zata haihu masa yake yi, shi ya sa duk wacce ya shirya aure sai na raba su da taimakon boka na." Gaba aya Amina mutuwa tsaye ta yi da jin zancen Umma hankalinta ya tashi kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi jin munanan abubuwa da Umma ta aikata. "Umma dama ba ke ce kika haifi Adamsy ba? Ba Mummy Karima ta haife ni ba duk shirinki ne ke ce kika hana Adamsy aure kike saka shi cikin halin da yake ciki?" afafuwanta kasa aukarta suka yi ta zube a wajen tana kuka tana cewa "Ke kika dur usa kika haife ni? Abun akwai ba in ni dai wallahi banyi sa'ar uwa ba." Umma bata saurare ta ba sai da ta kai bakin ofa ta juyo ta ce, "Duk yadda za'ayi ki tabbatar Admsy bai bar garin nan shi ka ai ba, ki tabbatar afarki afarsa barin Adamsy shi ka ai da zaki yi sh ine babban kuskure da zaki tafka a rayuwarku." *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://chat.whatsapp.com/IdLjpWceclh5VR8G5W9SFY . INA MASU BUKATAR KAYA AKAN FARA SHIN SARI KU SARA KU SIYAR KU SAMU NAKU AKAN FARASHI KALILAN MUNA DA KAYA KALA KALA KAMAR SU HIJABAI KAYAN KITCHEN ATAMFA LACE KAYAN YARA MOTHER CARE KAYAN SHAN ISKA NA ABBA MATERIAL DINKAKKE DA YADIN BEDSHEETS HULUNA DA SAURAN SU MUNA TURA KAYA DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI UBANGIJI *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Page1 "Duk yadda za'ayi ki tabbatar Adamsy bai bar garin nan shi ka ai ba, ki tabbatar afarki afarsa barin Adamsy shi ka ai da zaki yi shine babban kuskure da zaki tafka a rayuwarki." Haka Amina ta zauna ta dinga kuka ita ka ai tana cewa. "Dama ba Umma ta haifi Adamsy ba? Shi kansa baisan cewa ba ita ta haife shi ba,nima bansan cewa ita ce ta haife ni ba duk akan abin duniya " Kuke ta ke sosai kamar ranta zai fita, jin sautin kukanta ne yasa awayenta suka shigo cikin akin tare da tambayarta lafiya, hakan ya sa ta tsagaita kukan tare da ce masu ba abunda ke damunta, haka suka yi ta fama da ita akan ta fa a masa me ke damunta amma sam ta i fa a, hakan yasa ta ce ta sallame su kowa ta tafi gidanta tana bukatar ka aicewa ita ka ai a yanzu, dan haka suka bar mata gidanta kamar yadda ta bu ata. Lokacin da Direban Umma ya bar gidan Adamsy dai-dai lokacin da ya fito daga kwanar gidan Adamsy ya hau titi dai-dai nan sai ga motar Adamsy ta shigo kwanar, Sadik ne ke tu a motar nasa shi kuma yana zaune a gefensa idanunsa na kan motar tabbas motar Umma ce ba shakka.kallon Sadik ya yi tare da cewa "Ko mai ya kawo Umma gudana kuma?" Sadik ya kalle shi tare da cewa "Ina motar Umman ta ke?" "Yanzu suka bar nan, kuma na tabbatar daga gudana ta ke." Ba wanda ya sake magana sai da suka iso oafar gidan ne Adamsy ya kalli Sadk tare da cewa "Mu shiga ciki mana." Girgiza kai Sadk ya yi tare da cewa "Na kawo ka har kofar gida ne sakamakon ganinka da na yi baka cikin nutsuwarka,dan haka ka shiga guda kuma na kama gaba na." "Okay ba danuwa tunda haka ka ce, yanzu dai tunda baka auko motarka ba tana can gidan Umma to ka tafi da wannan motar tawa idan ka dauka ta ka sai ka ajiye wannan a can gudan." Daga nan ya mi a masa hannu suka yi musabaha sannan ya fita. Sadik ya ja motar ya bar wajen kai tsaye ya nufi gidan Umma. Koda ya shiga
Chapter 11 · 0% Book details