Sashe 42
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
arni ya ke mata. Foodflask na uku ya bud'e jollop din taliya ce da ta ji kayan lambu, nan ma ta toshe hanci wai bata son warin abuncin. Foodflask na hud'u ya bu e farfesun anyen kifi da ya ji kayan amshi ne, tana jin amshin farfesun ta fara kakarin amai a guje da wuce falo tare da zubawa akan dogon kujera. Bin bayanta ya yi cikin hanzari tare da tamabayarta "Me ya sa me ki? Dama baki da lafiya ne?" "Lafiya lau na ke , ba abunda ke mani ciwo, kawai gajiyar hanya ce." "Yanzu gajiya ce zaisa ki kasa cin abinci? Sai dai idan baki da lafiya." "Wallahu ba abunda ke mani ciwo gajiya ne, nasan zuwa anjima zan wartsake." "Gara ki wartsake kam kafin zuwa dare na ara maki wata gajiyar." Tura baki ta yi dan dama ta san wannan ba fashi. "Me zaki ci?" "Fruits kwai nake so" Wayarsa ya auka tare da kiran lamabar Mustapha ya basa Umarnin cewa ya kawo mata Fruits. Bayan wasu mintuna sai ga Mustapha ya yi sallama, hannunsa auke da faranti da aka yayyanka Fruits. Ajiye masu ya yi tare da gaishe su, Adamsy ya amsa masa. Tashi ya yi ya basu wuri. Jiki na rawa ta auki farantin tare da fara cin apple da kankana bayan ta gama da su ne ta fara shan lemo da abarba. Haka duka ta shanye Fruits in yana kallonta mamaki ma ta bashi yadda ta shanye su tas. Jingina bayanta ya yi da jikin kujera tare da lumshe idanunta, janyo ta ya yi ya mata fillo da cinyarsa. Cikin ankanin lokaci barci ya auke ta, a hankali ya gyara mata kwanciya tare da nufar dinning room din dan shima yunwa ya ke ji. Yana kammalawa ne ya auki key in motarsa ya fice daga falon. Direbansa na ganin fitowarsa ya araso wajensa, key in motar ya amsa daga hannunsa tare da nufar aya daga cikin motocin. Bayan ya fito da motar ne ya araso inda Adamsy ke jiransa, fitowa ya yi ya bu e masa bayan motar ya shiga kafin ya rufe ya zagaaya mazaunin Direban ya zauna. Suka fice daga gidan bayan mai gadin gidan ya bu e masu gate suka fice. Kasuwa suka nufa shagon Mallam Musa, inda ya kama hayar shago da ku in da Adamsy ya ba shi ne ya bu e shagon siyar da provision. Komai akwai shinkafa, wake, masara dauro, alkama. ayan angaren kuma ga su taliya, macaroni, indomie, maggi, Madara, milo omo sabulai da dai sauran kayan provision da ake siyarwa. Koda suka arasa shagon ma hankalinsa na kan customers masu siyan kayan provision, sai wani matasahin saurayi da ya ke taya shi siyar da kaya, yana angaren kayan awo. Murmushi Adamsy ya yi tare da rungume hannunsa, yana kallon yadda jama'a ke ta siyayya a shagon, hakan ya masa da Har ya kai mintuna biyar a tsaye Mallam Musa bai san ya yana nan ba. Sai da wannan saurayi da ke taya Mallam Musa sai da kaya ya kalli Adamsy ya ce, "Allaji me za'a kawo maka?" Sai a lokacin Mallam Musa ya lura da cewa Adamsy ne tsaye a wajen. Murmushi Mallam Musa ya yi tare da cewa "Yalla ai kai ne a nan? Bisimillah shigo daka ciki." arasa maganar yana janyo kujerar roba,tare da ajiye masa dan ya zauna. usawa ya yi tare da gaida Mallam Musa cikin girmamawa, ya amsa cikin farin ciki da jin da Zama ya yi a kujera Mallam Musa na murmushi ya ce, "To yalla ai sai dai zafi zai dame ka kasancewar ranka ce ba Ac ba." Murmushi ya yi tare da cewa "Na ga wuri Abba, ma sha Allah wuri ya yi kyau Allah ya sa albarka ya sa ka fara a sa'a." "Amin ya Allah, yau kuka dawo ne?" "Yau in nan." "Yau amma shi ne ka iya zuwa yau baka zauna ka huta ba." Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce, komai ba, a ransa ya ji da in yadda ya ga shagon kuma kasuwa na tafiya sosai. Kuma ya udiri niyyar cewa zai karawa Mallam Musa jari." Direbansa ne ya karasa shigowa nan ma ya gaida Mallam Musa, ya kuma yi masa addu'ar sanya albarka. Kasancewar ga mutane na ta shigowa ne ya sa Adamsy ta shi tare da yi wa Mallam Musa sallama suka tafi. Sai da ya yi sallar isha'i sannan ya koma gida, nan ma haka ya yi ta fama da da Humaira akan ya ce abinci amma ta i ci, har dai ya ha ura ya barta sai dai fruita da ta sha kawai ta ce ta oshi. Ya tamabaye ta ko bata da lafiya ta ce lafiyarta lau. Kwanciya ta yi, sai ya auke ta zuwa bedroom inta ya kwantar da ita. akinsa ya koma ya koma ya gama shirinsa na kwanciya barci sannan ya dawo akinta. Tana kwance har ta fara barci can cikin barcinta ta ji hannayensa na yawo a sassan jikinta, ga yunwa tana ji ga kasala sannan ga jarabarsa. Tana ji ya zare mata rigar barcin da ke jikinta, ya fara shafar jikinta, sai ya ji jikin nata da umi. "Baby jikinki fa ya yi zafi me ke damunki?" "Nima ban sani ba." "Yakamata mu tafi asibiti kiga likita ya duba ki." Gabanta ne ya fa i dan ta san cewa zancen allura ko magani ne idan aka tafi asibiti, dan haka sai ta yi saurin cewa "Ni fa ba abunda ke damuna kawai ina ga tafiya da muka yi ne ya sa na ke jin gajiya a jikina sosai, amma nasan cewa zuwa gobe zai bar jikina." Tana maganar tana lumshe idanu, alamar barci ne a idanunta. "To amma ai gajiya bazai saka jikinki ya yi umi ba, sai dai idan baki da lafiya." "To ni yana saka ni." "To bari na kawo maki magani ki sha." "Ni dai a'a ka barshi kawai ba zan sha ba " Duk yadda ya so lalla a ta akan ta sha magani in amincewa tayi, sai ya ha ura ya barta dan bai san ya takura mata aka abinda bata so. Rungume ta yi dan dole baida wani za i bayan yale ta, dan ya ji jikinta da zafi. A haka har barci ya auke ta kafin shi ma barci ya auke shi bayan ya jima barci bai dake shi ba. arfe hu u da rabi na asuba ne ya farka, rigar jinkinta da ya cire mata ne ya mayar mata sannan ya guda mata kwanciya . Bathroom inta ya mufa ya yi wanka tare da auro alwala, sallar nafila ya gabatar sannan ya zauna tana karatun Alkur'ani. Da aka kira sallar assalatu ne ya tayar da Humaira dan ta yi sallar asuba. Bayan ta tashi ne ya fita zuwa masallaci. Ita kuma ga gabatar da sallarta a gida. Tana idar da sallar asuba ta yi addu'a ko azkar bata tsaya yi ba kamar yadda ta saba yi. Daga nan samar sallayar ta yi barci. Koda ya ya dai daga sallar asuba lokacin arfe bakwai na safiya ne, kai tsaye akinsa ya nufa, inda ya shiga bathroom ya yi wanka, nan da nan ya shirya cikin shigar suits blue riga da wando sai ta ciki fara. akin Humaira ta nufa inda ya sa me ta kwance a saman sallaya tana barci. Shafa gefen fuskarta ya yi inda ya ji jikin nomal yanzu ba umi. Tashi zaune ta yi tare da cewa "Ina kwana ?" "Lafiya lau ya jikinki." "Ni dama lafiyata alu." "Zan fita da wuri yau zuwa office, saboda ina da meeting da safen nan, kuma aiki ya mani yawa." "To Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya." "Amin, na san ba zaki ci komai ba idan na tafi aiki, dan haka tashi muje dinning area." Marairaice fuska ta yi tare da cewa "Ni Fruits kawai na ke so." Bai ce komai ba dan ya san ba ci zata yi ba. Fita ya yi daga akin ba tare da ya sake wata magana ba. Bayan kamar mintuna goma sai ga shi ya dawo hannunsa auke da madaidaicin bowl Wanda ke auke da fruits da aka yanka su gutsi-gutsi, sai peck milk da ya juye mata gawangwani aya a ciki. arasawa ya yi a gabanta ya ce, "Ki tashi ki sha." Haka ta tashi ta auki bowl in da cokali ta fara sha, sai da ta oshi sannan ya fita zuwa office. Da misalin karfe biyu na rana tana kwance a falo, ta ji arar mota maigadi ya bu e gate. Haka kawai ta ji gabanta ya tsananta fa uwa, dafe irjinta ta yi tare da mi ewa tsaye ta nufi window ta bu e glass in window dan ganin motar da ta shigo, dan jikinta ya bata cewa ba Adamsy bane . Ganin wa anda suka zo ne ta zuba masu ido tana kallonsu, dan bata san daga ina suke ba. A zuciyarta ta ce, annan matan kuma daga ina?' Yana tsaka da driving a tsakiyar titi, ga ababen hawa suna ta kai da kawo, wayarsa ce ta soma ruri bai yi niyyar aukan kuran ba amma ganin Ummansa ce ta sa ya d'aga yana rike da haya da ayar hannunsa ayan hannun kuma yana driving da shi. "Assalamu alaikum, Umma ina kan hanya ne bari na arasa gida zan kira ki." "Ina jiran ka dan nima gani nan a cikin gidanka na Kaduna." Bai ankare ba sai ya ji sautin Gafff! *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaW2Ygg9xVJlgSoy2Q2V *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA ta zo muku