Sashe 25
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
makamancin haka. Tashi ta yi ta nufi wajen motar da suke jiranta, shi kansa Direba ya ji mamakin yadda uban gidansa wai zai je siyan koko a bakin hanya. "Yalla ai ka bari kawai nake na nemo da kaina." "A'a ka bari muje ta nuna wanda ta ke so." Baya iya musu da shi dan haka ya yi shiru suka tsaya jiran karasowarta. Amma a zuciyarsa yana mamakin yausheuban gidan nasa ya sauya haka ne. Tana arasowa suka kama hanyar fita bayan Mallam ya bu e masu gate. Basu tsaya ko ina ba sai unguwar su Humaira, tana zaune a bayan mota ita da Adamsy. Tsayawa suka yi wajen da ake siyar da kokon, kasancewar nisa da gidansu Humiara ne,da kanta ta fito bayan direba ya bu e mata murfin mota. Shikansa Adamsy yadda yaga yanayin unguwar da jama'ar da mutanen da suke wajen kokon bazai iya shansa sai hayaniya ake Adamsy ma ya fito yana kallonsu. Zubawa galleliyar motar idanu suka yi suna kallo, kamar wasu auyawa, kallon Humaira suka yi kamar wacce suka sani mai siyar da koko, amma sai suka ce ba ita bace,waccan ina ita ina shiga wannan motar. Bayan an zuba mata kokon ari biyu cikin jug da ta auka sai uli shina ta dauki na ari biyu, Direban Adamsy ne ya biya ku in ya mi a dubu aya, mai kokon ta mi a masa canjin dari shida, kai ya girgiza alamar ta bar canjin. Washe baki ta yi tare da godiya, bayan Sun juya zasu shiga motar ne kamar daga sama suka ji an ce "Hamaira!" A firgice ta juyo dan jin murayar mai kiranta sai da gabanta ya fa *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman karin bayani* 09065327995 Love you oll *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page3 A firgice ta juyo dan jin murayar mai kiranta, sai da gabanta ya fa Ba kowa bane illa Salma tana auke da bokitin ruwa akanta. Kau da kanta ta yi ta shige cikin mota, Direba ya ja motar suka bar wajen. Salma ta saki baki tana kallon motar har ta acewa ganinta. Gani ta yi ba zata iya gudu da ruwa ba, dan haka ta watsar da ruwan nan wajen ta ruga a guje dan zuwa kaiwa Inna Habi labarin Humaira. A cikin motar kuwa Humaira har sai da idanunta suka cika da walla,Adamsy ne ya kalle ta tare da cewa "Wace ce waccan da ta kira ki?" Girgiza masa kai ta yi tare da cewa "Ba kowa bace." "Ya aka yi ta san sunanki? Kuma me ya sa kika tsorata da ganinta?" Bata ce komai ba illah maida wallarta da ta, ganin bata da niyyar a shi amsa ne ya sa ya yi shiru. Wayarsa ce ta soma ruri,sabawa ya yi tare da sakin murmushi sannan ya aga wayar tare da cewa. "Barka da safiya Ummana." "Yauwa Barka dai Babana fatan ka tashi kafiya." "Lafiya lau Ummana, fatan kema haka." "Nima haka shalelena yau har ka ta shi barci da wuri? Kai da na san idan na kira ka irin wannan lokacin sai dai na ji kana barci. Fatan dai lafiya ko?" Tunawa ya yi da zancen Sadik na cewa wanann auren ya kasance auren sirri ne, kada ya sanar da kowa ciki kuwa har da mahaifiyarsa, duk da tunda ya ke da ita baya mata arya, gaskiya ya ke fa a akan koma Menene. Amma yau karo na farko a rayuwarsa da Ummansa ya tambaye shi abu da zai mata arya . "Lafiya lau Ummana wata fita ce ta gaggawa ta kamani." "Akan me kenan?" an jim ya yi tare da cewa " Dama na fito ne na nemi abin breakfas" "Kai da ake kawo maka abinci kuma sai ka fita ka nema?" "Am dama na ji sha'awar shan koko ne da uli shine..." Dariyar da ya ji Umma ta yi ne ya sa shi dakatar da maganar da ya ke yi. "Babana yaushe ka fara mani arya ne?" "Umma arya kuma?" "Ba abi'arka bace arya, kuma a duk lokacin da ka fa e ta sai an gane, dan baka iya ta ba." Shiru ya yi ya kasa sake magana, inda ta cigaba da cewa "Ina ji a jikina cewa akwai wani abu da ke faruwa a gidanka da kake oye mani." "Ba abunda na ke oye maki Ummana, kema kinsan d'anki bazai oye maki komai ba." "Shikenan tunda haka ka fa a, to ya aikin?" "Alhamdulillah" Fira suka an ta a daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar. A guje ta shiga cikin gida ko sallama ba ta yi ba, dama ba ta saba sallamar ba. "Inna! Inna!! Inna!!!" Da sauri ta fito daga cikin aki tare da cewa "Ke lafiya irin wannan kira haka?" "Inna wallahi na ga Humaira tare da wasu maza su biyu, kuma inna masu ku i ne fa, saboda a cikin wata dan areriyar mota su..." Ta yi saurin katse ta ta hanyar cewa "Ina suke!" "Sun shiga mota su tafi?" "Sun tafi ina?" "Nima ban sani ba, amma na gansu a farkon layi sunzo siyen koko sun tafi." Inna ta ora hannu akai tana salati "Amma tunda na ke ban ta a ganin mutum wanda ya ke saurin manta alkhairi kamar waccen yarinyar ba, wato ta samu namiji ta mance da ni ko?" e baki Salma ta yi tare da kau da kai. "To ba ke kika tura ta ba." "Ko da na tura ta dan ta nemo ku i ta kawo mani, ba wai ta je ta tare gidansa ba." Nan dai ta cigaba da masifarta ba mai cewa ta yi shiru, Salma dai itama ta fara typing tunanin hanyar da zata bi dan ta shiga irin rayuwar da Humaira ke ciki, domin tana ganin cewa karuwancin da Inna Habi ta ce ta je ta yi shine ta ke yi. Zaune ta ke a dinning chair tana shan koko tana tauna uli, yana zaune a gefenta yana kallonta, yadda ya ke sha, dan ko da ace yana shan koko da osai ma bazai iya shan na wannan aramin yankin ba. Yadda dai ya ga ana ebe shi ga yara masu siya sun dabaibaye ta kamar zasu shiga ciki, ga wajen ba tsafta ne da shi ba. Shima kansa ba wani breakfast na kirki ya yi ba, ruwan Lipton kawai ya sha. Dai da ta sha rabin jug in sannan ta ajiye, sauran mulkin m ya aure shi a leda ta ajiye gefe. Gyatsa ya yi alamar ta koshi, hakan ya sa ya juyo tare da kallonta. A hankali ta ce, "Alhamdulillah" Murmushi ya yi tare da cewa "Ma sha Allah" Wayarsa ce ta fara ruri, kallon wayar ya yi ya ga Abdallah ne ke kiransa, ta shi ya yi ya nufi akinsa dan dama yana bu atar tattaunawa tare da shi. aukar wayar ya yi gab da zai shiga akinsa. "Assalamu alaikum" Daga can angaren Abdallah ke kwance a saman gado, sai Maryam da ke zaune a gefensa. "Wa'alaikumus salam, na Humaira ka sha amari. Ajiyar zuciya Adams ya sauke tare da cewa "Ina jin tsoron ranar da Ummana zata gane ba yi aure ba tare da na sanar da ita ba. Bansan ya zata kalli lamarin ba." "Komai zai zo d sau i kuma kada ka damu tunda, ja bi shawara ta zaka ga amfanin hakan." "To abu na biyu kuma dangabe da yarinyar nan Humaira ne." "Me ya sa me tane?" "Ba abunda ya sa me tausai dai ina jin tsoron abinda zai sa ta me a dalilina." "Kaga yakamata ja daina tunawa da abubuwan da suka faru da wa ancan matan, kana ganin cewa itama Humaira wani abun zai sa me ta, suma wa ancan addararsu ce haka kuma ba wanda ya isa ya sauya masu shi. Ni dai ina mai ara jaddada maka kada ka bari wani wanda ya ke da wata da kai ya san da zancen auren, akwai amfanin yin hakan." "Amma gaskiya ban zan iya juriya da ha uri cewa na cigaba da zama ba tare da na sanar da ita ba." "Ba wai na ce kaada ka fa a mata bane, a'a ina son ka bari zuwa nan gaba ka an, abinda ya sa na ce kada ka fa a mata shine duk sirrin da ke cikin cikin ka sirri ne amma da zaran ya fito sunansa tonon asiri, to wannan auren sirrin na ka kada ka sanar da kowa tukunna. Da sannu zaka fahimci me na ke nufi." "Shikenan" ",Kai kanka yanzu baka fara ganin sauyi ba?" "Sauyin me?" "A cikin mata guda bakwai da ka aura akwai wacce ka zauna da ita na cikakken mintuna biyar a inuwar ma'aurata?" "Babu" "Ita wannan ga shi a cikin kwana aya har ka sha romon amarci ." Nan dai ya cigaba da arin ya bashi Shawara akan rike auren nan ya barshi a matsayin sirri ba tare da sanin kowa ba. Kamar kullum da yammacin ranar ma sai ga shi an kawo masu abinci daga restaurant. Kamar yadda kullum ake kawo masu sau uku a rana. Bayan ya kar i abincin ne ya ajiye da dinning table, dama an riga da an bawa sauran ma'aikatan gidan nasu kowa leda aya. Yana shirin shiga akinsa ne sai ya ji arar ararrawar ofa, komawa ya yi ya bu e, inda ya ga Mustafa ne wato kuku da zai dinga masu girki. usawa ya yi cikin girmamawa ya ce "Ina wuni yalla Cikin sakin fuska ya amsa masa da murmushi a fuskarsa. "Barka da isowa Mustafa ya gajiya?" "Alhamdulillah" "Ga shi lokacin sallar magrib ta gabato, an gyara maka akinka da ke can angaren ba "Godiya nake yalla "Badamuwa idan anyi sallar isha'i sai ka shigo muyi magana ko?" Sallama ya masa ya nufi angaren ba i, wanda dama ya ta a zama a gidan lokacin kafin Adamsy ya yi auren farko yana masa girki idan ya shigo Kaduna. Komawa akinsa