Sashe 12
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Falon ba kowa kai tsaye ya nufi akinsa dan damuwa ce fal a tare da shi, sautin kukan Amina ya ji yana tashi daga akinta, cikin tashin hankali ya nufi akinta. Tura ofar ya yi bakinsa auke da sallama. "Assalamu alaikum" Kukanta kawai take yi ba tare da ta san ya shigo akin ba, a hankali ta tako har ga gabanta jin motsin mutum ne ya sa ta ago kai ta kalle shi, mi ewa tsaye ta yi ta zuba masa idanu kamar wacce ta ga sabon halitta, fa awa jikinsa ta yi tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya. Tausayin Adamsy ne ya kama ta, hannayensa ne ya sa ya ago ta daga jikinsa ya ce, "Me ya faru kike kuka?" Shiru ba amsa sai ajiyar zuciya da take saukewa. "Ne ce me ya sa me ki ne kike kuka ko rasuwa aka yi ne kike kuka?" Girgiza masa kai ta yi alamar a'a daga nan ta cigaba da kukan da ta ke yi, "To ki fa a mani me ke saka ki kuka?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Bakomai." "Ban yarda da cewa bakomai ba, haka kawai ba zaki zauna kiyi ta rusa kuka ba tare da wani dalilin ba." Kai ta jinjina alamar eh, girgiza kai yayi tare da cewa "Sai dai idan zaki oye mani ne." "Mafarki na yi da ya firgita ni na dinga kuka." Duk yadda Adamsy ya lalla a Amina kan ta sanar da shi abinda ya sa me ta har ta dinga kuka in fa a masa ta yi haka ya gaji ya yale ta. Da ya samu tayi shiru ta daina kumar ne sai ya nufi hanyar fita daga akin, har ya kai bakin ofar ya juyo ya kalle ta ya ce, "Na hango motar Umma da zamu shigo layin nan lafiya dai ko?" Jinjina kai ta yi tare da cewa "Lafiya lau ta shigo ta gaishe ni ne?" "Kuma wannan kukan da kike bida nasaba da zuwanta?" "Ko da ta shigo ta fita lafiya lau bayan fitarta ne kaina ke ciwon?" "Kinsha magani?" "Eh na sha." "To ki kwanta " Nufar gado ta yi ta kwanta kamar yadda ya umarce ta. Shima fita ya yi tare da barin akin kai tsaye ya nufi akinsa. Zama ya yi akan sofa tare da jinginar da bayansa ya shiga aikin tunanin da ya saba yi, dan labarin haukacewar Hauwa'u da mutuwar Fauziyya sun girgiza shi sosao, hawaye ne suka fara gangarowa daga idanunsa ya furta a hankali. "Allah kai kasan sirrin oye da na fili, Allah ka iya mani abinda bazan iya ba, Allah ka magance mani matsalata." Wayarsa ce ta fara ruri dubawa ya yi ya ga manajansa ne na Kaduna, agawa ya yi tare da cewa "Assalamu alaikum" Daga can angaren manajan ya ce, "Wa'alaika salam. Barka da warhaka yalla ai." "Yauwa Barka dai." "Akan maganar da muka yi azu ne na tanadi komai tunda ka ce a fitar da komai na gidan a zuba sababi gidan ma a sabunta sa duk an fitar da komai na gidan kamar yadda ka bu ata za'a sabunta shi, amma kayan da aka fitar daga cikin gidan ya za'ayi da su ne?" "Ka bawa masu bu atarsu." "To yalla ai Allah ya saka da alkhairi. Uban giji ya ara bu i, yanzu idan an gama sabunta gidan sai a yi order sabbin furniture's da kayan kitcheen." "Ba matasla." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran. Farin ciki ne kawai ya lullu e manaja dan ya san cewa wasu daga cikin kayan wasu kuma zai ba wasu dan komai sai da aka fitar daga cikin gidan kuma ba wai dan sun tsufa ba sai dai ura da suka yi. Gaba aya kayan falon biyu sautin kujera biyu da gado da ke cikin kowane bedrooms guda hu u sai da aka fitar, da fridge da freezer gas kayan kitcheen labulaye carpet komai sai da yasa aka fitar ya ce a zuba sababbin a cikin gidan . Sake kiran wayar manaja ya yi inda cikin rawar jiki ya aga kiran wayar tare da karawa a kunnensa. "Hellow yalla ai ." "Kana jina?' "Eh ina ji yalla ai." "Ka samo mani mai gadi da zai zauna a gidan ya dinga kwana, kasan wancan mai gadin tunda ya yi jinya ya koma auyensu bai dawo ba nima ban nemi wani ba, so yanzu ina bukatar mai gadi." "Okay ba danuwa yalla ai zansa a samu ko mai gadin kamafaninka idan na masa magana zaiyi saurin samo mani, dan kwanakin baya ba'ayi sati biyu ba ya zo ya same ni wai abokinsa na son aiki ko na gadi ne, zan masa magana sai ya kawo wancan in idan bai samu aikin ba." "Okay to ka bai cika sai na jika." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran wayar. Tana tafiya tana auke da bokitin tallar doyar da ta ke yi, amma kallo aya zaka mata ka gane cewa arfin hali ce kawai, amma tana jin jiki sosai. Tafiya ta ke yi tana angisa afarsa da inna Habi ta buga mata ita ce, ga duk inda ta ta a a jikinta ciwo ne sai kuma wasu wuraren da sun uri ruwa sunyi bororo musamman ta cikin rigarta daga gefen ugunta, gashi bata jin zata iya yawon rallar da ta saba saboda yanayin tafiyarta afarta na ciwo sosai ara sawa ta yi wani ofar gida da maza ke taruwa ta yi sallama ta ajiye robar doyar, dama kullun suna siya idan ta kai masu doyar, dan haka suna ganinta suka fara tambayrta. aya daga cikinsu ya ce, "Humaira lafiya kuwa?" "Lafiya lau. ina wuninku?" Wani dattijo da je gefe ya ce, "Ruwan zafi ne ya zube maki a jiki?" Kai ta girgiza alamar a'a. sai tya sake tambayarta da cewa "Ga jikinki duk kunar wuta " "Idanunta ne suka ciko da wallon ta ce dukana aka yi." Gaba aya jama'ar da ke wajen suka ha a baki cikin mamaki suka ce "Duka?" Kai ta jinjina alamar eh Wani daga cikinsu ya ce, "Wane irin duka jikinki ya yi haka?" "Da itacen bakin wuta ne shiyasa " Salati suka saka tare da tambayarta waye ya mata haka, nan ta sanar da su matar babanta inda suka shiga tsinewa Inna Habi . Mallam kallamu ne ya yi sallama kofar gidan abokinsa Mallama Musa, baya nan sai inna Habi ta amsa ta sanar da shi baya nan. Yana shiri barin ofar gidan sai ga Mallam Musa ya araso zai shiga gidansa. "To Mallam Kallamu kai ne da rana tsaka?" "Eh ni ne." Hannu ya mi a masa suka gaida inda ya ce, "Sauri na ke zan koma bakin aikina, samu ne ya sa na zo na sa me ka." Murmushi yayi tare cewa "Alhamdulillah" "Yauwa abinda ya sa na zo na same ka saboda maganar da ka zo har wajen aikina ka sa me ni kan cewa kana neman aiki ko gadi irin wanda na ke yi ne hakan yasa na samu manajan kamfanin da nake gadi ya ce babu yanzu kuma na sanar da kai." Kai Mallam Musa ya jinjina tare da cewa "Eh haka ne ba shakka." "To yanzu aikin gadin ya samu dai dai ba irin nawa bane ban sa ni ba ko zaka iya." "Gadi ai gadi ne." "Mallam Musa kenan, ai nawa gadin daga arfe bakwai na safe ne zuwa bakwai ma magrib na tashi akwai security da ke kwana yana gadi,to kai kuma na ka yanzu na zama ne din din din, wato nan zaka dinga wuni kana kwana, akwai akinka da ban aki a cikin gidan kowane lokaci kana nan zaka iya, dan irin wannan aikin 'yan cirani sunfi haka, amma kai na ga da iyalinka." Bakomai zan yi na gaji da zaman nan na rashin abinyi ga wula ancin Habi akan abinda ta ke wa Haumaira, saboda bana kawo abinci bata kallona a matsayin mai gida, yanzu haka sammakon barin gidan na yi amma ban samu abinyi ba. Na amince zanyi gidan waye?" "Shugaban kamfaninmu shi zai dawo nan da zama yanzu haka ana kan gyaran gidan ne an ce gobe na zo da kai." "Masha Allah. Allah ya kaimu nagode sai mu tafi na fara aikin. *Daga al alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *INA KUKE BIG LADY'S KIKARANTA KOBAZE ANFANEKIBA ZE AMFANI WANI NAKI*