Sashe 3
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta shirya ya kaita ta gaida Ummansa, dan sunyi magna da Umman akan Fauziyya zai kai mata ita su gaisa. Bayan ya gama shiri cikin manyan kayansa ya saka hula ya fesa turare, takalminsa ya saka tare da aukar wayarsa ya fito zuwa falo, Amina na zaune a falo idanunta na kan wayarta, amshun turarunsa ta ji yasa ta ago da kai tana kallonsa, murmushi yayi tare da zama a gefenta. Hannunsa ya ri o cikin nata tare da cewa "Zan an fita ne? "Fita kuma naga yau weekend ne baka zuwa ko ina?" "To idan kuma fitar ta kama da ya za'ayi? " "Wannan irin kwalliya haka kamar wani ango?" Dariya yayi tare da cewa "Ai ango ne" Da sauri ta sake kallonsa "Ango wace ce?" "Angonki mana " Dariya tayi tare da cewa a mani gaskiya ko dai anwa kake shiri sake kawo mani ne, tunda Husnah ta guje mu." Shiru yayi yana nazari wayarsa ta soma ruri dubawa yayi yaga Fauziyya ce take kiransa, sai ya juya ya kalli Amina dan yaga ko ta lura da mai kiran wayarsa, ita kuma ta lura taga sunan wacce ta kira, amma sai tayi saurin auke kanta, dan taga zai kalle ta, ganin ba wayar take kallo ba idanunta na kan wayarta yasa shi tunanin bata ,gani mai kiran wayar ba, bai aya daga ba har wayar ta tsinke aka sake kiransa a karo na biyu duk Fauziyya ce, nan ma bai aya ba sai dai ya saka wayar a silent. "Ba kiran wayarka ake ba ne?" "Kiran ba mai mahimmanci bane shiyasa." Murmushi tayi tare da maida hankalinta kan wayarta, text message ne ya shigo wayar dubawa yayi yaga Fauziyya ce take cewa "Na gama shiryawa kai nake jira.' Amsa ya mayar mata inda ya ce "Okay gani nan zuwa' Daga nan sai ya kalli Amina da duk abinda yake akan idonta ne ya ce "Ni zan fita ne" "To mijina muje na raka ka ko?" Tashi sukayi hannunsu sar e cikin na juna, inda ta rika shi har bakin motarsa, sannan ta koma ciki. Horn yayi mai gadin gidan ya wangale masa gate ya fita da motarsa. Har ya fara tafiya ya samu gefen hanya yayi parking inda ya lalubo number Fauziyya ya danna mata kira, bugu biyu ta aga tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki salam" "Ina ta kiran wayarka baka agawa fatan dai lafiya?" "Lafiya lau ina gaban Madam ne shiyasa ban aya kiran naki ba." Shiru tayi tana nazari kafin ta ce "Wace madam kenan?" "Mata ta mana" "Oh dama dan kana tare da ita ne baka auki waya ta ba? Ko kuma wayar kowa ne baka auka idan kana tare da ita?" "Naki ne dai kawai bana auka a gabanta, dan gudun aci ranta." Cikin ba in ciki Fauziyya ta katse kiran wayar, ajiye wayar yayi tare da tada motar ya auki ga hanyar gidansu Fauziyya. ofar gidansu yayi parking tare da aukar wayar ya sake kiranta, sai da ta kira sau uku kafin ta auka tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki salam" "Ka iso ne?" "Eh ina ofar gidanku yanzu haka." "Okay gani nan fitowa" Daga nan ta katse kiran wayar tare da aukar hijabinta ta saka ta auki hand bag inta ta fito. Mama ta samu a tsakar gida tana zaune a kan tabarma tana sauraren rediyo, dur usawa tayi a gabanta tare da cewa "Mama sai mun dawo" Jinjina kai Maman tayi tare da cewa "To adawo lafiya, dan Allah Fauziyya kada ki da e ku dawo da wuri kafa kiyi ta zama can " To ta amsa mata da shi sannan ta fito zuwa waje, a motarsa ta same shi zaune yana jiranta, ta fito, bu e murfin gaban motar tayi tare da yin sallama ta shiga. amsar mata sallamar yayi tare da cewa "Gimbiya kin fito?' e baki tayi tare da cewa "Gimbiya ba ka baro ta a gida ba?" "Eh kema Gimbiya ce" Hmmm, Adamsy kenan, wallahi da nasan kai mijin ta ce ne da ban amince da kai ba, da nadan cewa tsoron matarka kake da ban amince da aurenka ba, ko yanzu ban makara ba, dan kan bazan iya auren mijin da matarsa tafi arfinsa ba." Dariya ya yi ya ce, "Wai duk wannan maganar ta meye?" "Na kira ka a waya baka aya daga ba saboda kana gaban matarka, wato ba zaka auki waya a gabanta ba saboda kai mijin ta ce ne? To gaskiya banzan iya ba dan kada na aure ja ace kana tsoron matarka yaushe zaka ita adalci a tsakanin mu har ka sauke ha ina dake kamala?" "Fauziyya kenan ni ba irin wannan tsoron nake ba, ina dai girmama mata ta dan gani nake idan na yi waya a gabanta kamar cin fuska ne, nasan kuma hakan bazai mata da i ba shiyasa ina girmama mata ta sosai Kuma nu ba irin mazan nan bane wadanda suke juyawa mace baya ko su lallatata a wajen Amaryar bane , ko ke na aura abinda zan maki kenan." Murmushi tayi tare da cewa "Na fahimce ka" Shima murmushi yayi yana tada motar suka bar kofar gidan kai tsaye suka nufi gidan Ummansa. Da sallama suka shiga Falon Umma na zaune akan doguwar kujera tana kallon T.V inda ta kamo tashar Africa t.v 3 inda suka saka wa'azi Sheikh Jabir Sani mai hula. Sallamar su fa ta ji yasa ta kalli bakin ofar shigowa ta ce, "Wa'alaikumus salam, barka da zuwa sannunku" arasawa sukayi suka zauna a saman center carpet, cikin girmamawa Fauziyya ta ce, "Ina wuni Umma?" "Lafiya lau 'yata kuna lafiya?" "Lafiya lau Umma" "Ya su Maman naku duk suna lafiya?" "Duk lafiya Umma" "Masha Allahu" Adamsy ma ya gaishe ta ta ta amsa masa cikin jin da in da ya kasa oyowa a zuciyarta, tare da tambayarsa Amina ya amsa da tana lafiya. Mai aikinta Saude ta walawa kira bayan ta zo ta umarce ta da ta kawo masu abinda sha. Nan Saude ta cika gaban Fauziyya da kayan ciye-ciye da sha, ita dai Fauziyya da yar ta iya shan ruwa, nan dai Umma ta dinga janta da fira daga eh sai a'a take amsawa har suka tashi tafiya Umma ta ha a mata kayan turarruka tabawa Adamsy ta ce, "Babana ga wannan ka bata ko?" "To Umma tana godiya." Lokacin ma duk Fauziyya ta fita tana jiran fitowarsa, bayan ya fito ne suka shiga mota ya tada motar tare da yin horn mai gadin ne ya bu e masu afa suka fita. Sai da ya biya wani super market ne yayi mata siyayyan kayayyakin tun daga kan kayan ciye ciye da ma ulashe har har ya zuwa kayan kwalliya duk ya cida mata. A mota ya same ta tunda ya ce, ta zo su shiga ta i dan haka ya shiga yayi mata siyayyan ya dawo. Manyan ledoji ne guda biyu ya zuba su a bayan motar sannan ya shiga ya tada motar dai da suka fara tafiya ne ya kalle ta ya ce, "Me yasa baki shiga ba ko akwai abinda zaki so a ciki?" Kai ta girgiza tare da cewa "Kada ka wahalar da kanka na bana bu atar komai." Daga nan bata sake magana ba ganin tana kallon lokaci yasa ya ce, "Wai saurin me kike yi?" "Lokacin islamiyya nake dubawa dan daura mintuna goma, kuma bana son na makara." Daga nan bata sake magana ba har suka ara da ofar gidansu. Ganin tana arin fita ne yasa ya ce, "To ai ga sa on Umma baki kar a ba." Sunkuyar da kanta tayi, ya auko sa on Umma da kuma aya daga cikin ledoji guda biyu da ya siyo daga super market ya saka saka ku i 100k ya saka mata a cikin ledan da yayi mata super market.mi a mata yayi tare da cewa "Gashi." ganin arin ledan yasa ya ce, Wannan kayan sunyi yawa ai." "To ki rabar idan sun maki yawa." Godiya yayi tare da kar ar ledojin ya fita, shi kuma ya ja motar yabar wajen. Kai tsaye gidansa ya koma inda ya kaiwa Amina ayan ledan da ya siyo daga super market. ********** ********** Kwanci tashi asaran mai rai yau saura kwanaki bakwai auren Adamsy da Fauziyya, yayin da kowane ango da Amarya zaku ga yana zumu i da farin ciki amma a waurin Adamsy da Fayziy akasin haka ne, domin kuwa Fauziyya bata aunar ganin Adamsy yanzu ta tsane sa sosai ko kiran sunansa ta ji anyi sai gabanta ya fa i. Ita kanta bata san dalilin hakan ba, dan a iya saninta tana matu ar kaunar Adamsy a cikin zuciyarta, bata son aci ransa kullum bata da wani buri da ya wuce ta mallakar shi a matsayin abokin rayuwarta. Amma yanzu kam ya zamo tamkar mujiya a wurinta, ko auka wayarsa m bata yi yayi ta kira bata agawa ko text message yayi mata bata maida masa reply arshe ma sai tayi blocking nasa. Da abun ya ishe sa ne ana saura kwana uku aurin auren ya je ya sami Baban Fauziyya bayan sallar Isha'i. Bayan sun gaisa ne Baban Fauziyya ya kalli Adamsy ya ce, "Ya shirye-shirye?" "Alhamdulillah, Baba" Shiru ne ya biyo baya inda Baban Fauziyya ya ce, "Lafiya dai ko akwai mata matsala ne?" "Eh Baba akwai wata 'yat matsala." "Subhanallahi ina jinka" "Baba yanzu gaba aya na kasa gane kan Fauziyya yanzu a alla mun kai sati uku bamu yi maganar arziki da ita ba, gaba aya ta daina aukar waya ta ko message na tura mata ba amsa, arshe dai blocking ina tayi, ko na zo nan na aiko a nan nazo bata fitowa haka zan gaji da zaman jiranta na ha ura na tafi. Har abokina da ke unguwar nan Sadik ya zo ya same ta sai ta ke sanar da shi cewa wai yanzun bata so na ta canza ra'ayinta." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu haka Fauziyya ta yi haka da kanta?" Jinjina kai Adamsy yayi tare da cewa warai kuwa, yanzu haka na janye zancen aurenta dan da muguwar rawa gara in takawa." Shiru Baban Fauziyya yayi tare da cewa "Ka bani kwana biyu zan binciki lamarin nasan inda matsalar take." Godiya Adamsy yayi mata tare da sallama ya tafi. Koda