Sashe 36
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanzu na sauka gajiyar tafiya ne." "Shikenan idan ka huta gajiyar tafiya sai mu yi magana." "Okay" Daga nan ta katse kiran tare da sa a abubuwa da yawa a cikin ranta. Tana ganin ya hankalinsa na kan waya ta tashi daga cinyarsa tare rufe zip din rigarta. "Sannu da zuwa." Ta fa a tare da dur usawa ce cikin girmamawa. Lumshe idanunsa ya yi tare da cewa "Me ya sa baki jin maganata?" Ya fa a tare an tsuke fuska. Narai-narai ta yi da dara-daran idanunta. "Me na yi?" "Kafin na wuce ban sanar da ke cewa ban yarda ki zauna tare da Mustapha ba, ko ba ce maki na yi wurin mahaifinki kawai na amince ma ki tafi ba? Ko wurinsa sai kin sanya hijabi saboda ma'ikatan gidan kowa zai iya ganink. Amma saboda ban isa ba kike zama tare da Mustapha da wannan shgar da kika yi ko ankwali baki aura ba ko?" "Tunawa ta yi ita dai ko da ta shiga kitchen sanye ta ke da hijabi, daga nan ta zo ta kwanta, kuma ta san Mustapha baya shigowa falonta, daga ofar kitchen zai nufi dinning room daga nan ya fice, ita dai bata san dalilin da ya sa ya ga laifinta ba, ba zata iya musu ko jayayya da shi ba dan haka ta ce "Allah ya huci zuciyarka, ka yi ha uri." Sai ya ji wani san yi a ranshi, dan yarinyar tana da biyyayya bai ta a nuna mata ga abunda ya ke so ta i yi masa ba. Ko da bata son abu indai yana so haka zata ha ura ta masa biyayya, nata ta a bijire masa ba, sa anin Amina. Shi ya sa ya ke sonta har cikin zuciyarsa. Idanunta suka sauka akan plate d'in da Mustapha ya ajiye mata tare da rufe sa da wani plate. arasawa ta bu e plate din ta ga an wake ne da yaji da mai, sai kabeji da tunatar sai dafaffen wai guda biyu. Kallon Adamsy ta yi tare da cewa "Kai ka kawo mani?" Kai ya girgiza mata alamar a'a. Sai a lokacin ya fahimci cewa ashe ta dai bashi ha uri ta amshi laifnita ne ba tare da ta aikata komai ba." "Kina nufin cewa ba ki san lokacin da ya shigo ba?" Kai ta girgiza tare da cewa "Yanzu na gani." "To ki zauna ki ci abincin ni bari na shiga na yi wanka." Daga nan ya nufi aknsa, ita kuma ta nufi fridge ta auko robar ruwa da kofi ta zo ta zauna ta fara ci. Tana zaune ta ga ya fito ya sauya kayan jikinsa, zama ya yi a saman kujera da ke fuskantarta. "Zan fita yanzu Abdallah ya kira ni wai baida lafiya." "Subhanallahi ya jikin nasa?" "To ya ce da sau i, sai na je zan gani." Maraice fuska ta yi tare da cewa "Dan Allah ka tafi da ni ." Ba musu ya ce ta shirya su tafi amma bari ya tafi masallaci ya dawo. Cikin farin ciki da jin da i ta tashi tare da auke sauran an waken da ta rage ta nufi kitcheen. Shi kuma masallaci ya nufa. Ko da ya dawo daga masallaci ya tarar ta shirya ta sauya kayan jikinta, ta na sanye da riga da zani na atamfa, lemon green yana da ratsin Orange colour a jiki, sai hijabin da ta saka shima orange colour . Wayarta ta ri e a hannu, takalmin da jaka ba i ne, ta yi kyau sosai. Fuskarta ba kwalliya powder kawai ta shafa. Makullin motarsa ya auka dan baya bu atar Direba. A tare suka jero har zuwa harabar gidan, Mahaifinta ta yi wa sallama ya bu e mata gaban motar ta shiga, shima ya shiga ya zauna mazaunin Direban. Mallam Musa zuciyarsa cike da farin ciki, wai yau 'yarsa ce hankalinta kwance haka, lallai hausawa sun yi gaskiya da suka ce bayan wuya sai da Suna tafiya kan hanya ne ya kalle ta ya ce, "Ranar yaushe ne ma suka ya kawo Maryam ta wuni maki?" "Shekaran jiya ne fa" Yana ta hanyar da fira har suka isa gidan, bayan mai gadi ya wangakeasu gate ne ya shiga da motarsa. Parking ya yi tare da fitowa ya bu ewa Humaira itama ta fito. Kai tsaye suka nufi cikin gidan, ina suka tsaya suna knocking inda Maryam ta bu e masu ofa. Da sallama suka shiga inda ya tarbe su hannu bibbiyu, inda Haumaira ta ga Amatullah tana mata wasa. Bayan Maryam ta aje masu abun sha ne ta nufi akin Abdallah. Ba jimawa sau ga su sun fito a tare. ara sawa ya yi tare da mi awa Abdallah hannu suka gaisa. "Mutanen Katsina barka da sauka." Murmushi Adamsy ya yi tare da cewa "Barka dai, dama kwana biyu baka da lafiya shi ne baka sanar da ni ba." Murmushi Abdallah yayi "Ai na ji sau i sosai." "Toh Alhamdulillah ." "Ya mutanen Katsina ya Umma da uwar gida Amina." "Alhamdulillah duk suna lafiya" "Ma sha Allah." Nan suka ta a fira har lokacin sallar la'asar ta yi,mazan suka fita zuwa masallaci. Maryam ta ja Humaira zuwa bedroom unta. Bayam sun shiga ne sai Humaira ta kwantar d Amatullah . Bayan sun idar da sallar ne Maryam ta auki wani gora da zuma a ciki ta bawa Humaira ta ce "Ki shanye shi yanzu" Haka Humaira ta kar a ba tare da musu ba ta shanye shi , sai kuma ta bata wani tsimi nan ma ta bata ta shanye shi tas. Sai da ta bata magunguna sun kai kala biyar ta sha sannan ta ja hannunta suka dawo falo, inda suka tarar da su Abdallah sun dawo daga masallaci. Nan suka cigaba da fira sai arfe biyar suka baro gidan . Suna tafiya akan hanya ne kwatsam sai suka ga wani mahaukaci ya gifta ta gaban motarsa, iris ya rage Adamsy ya ka e shi sai ya taka burki da sauri. Fitowa ya yi daga cikin motar inda ya samu wannan mutumin mai kama da mahaukci. "Baka dai ji ciwo ba ko?" Adamsy ya tamabaye mutumin cikin tausayawa. Ganin kamar mutumin na cikin wahala ya sa ya shi jin tausayinta. i ya ciro masu yawa daga aljihunsa ya basa, mutumin yasa hannu biyu ya kar Kallon kudin ya ke yana kallon Adamsy,shi dai Adamsy ya juya zai shiga motarsa ya ji muryar mutumin na cewa a rayuwarka tana cike da alubale, Allah ne kawai ke kare ka. Ka cigaba da addu'a domin kana cikin wani hali Kai da Mahaifiyarka, domin addu'a zaka dage da shi wata har Allah ya sa Mahaifiyarka ta dawo cikin hankalinta, domin a halin yanzu bata san kanta ba tana cikin mawuyacin hali." Kallon mamaki Adamsy ya masa tare da cewa "Mahaifiyata fa bata cikin ko wane mawuyacin hali, domin ba da e da gama magana da ita a waya ba." Dariya mutumin ya yi tare da cewa "Wannan ba Mahaifiyarka bace zaluma ce kuma makira ce ba Allah a ranta." Wayarsa ce ta soma ringing, ya ciro wayar ya duba mai kiransa, sai ya juya bayansa dan magana da wannan mahaukacin amma ko sama ko asa gabas da yamma kudu da Arewa ba alamarsa. Mamaki ne ya cika Adamsy to ina ya ke? Shiga cikin motarsa ya yi ba tare da ya aga wayar ba. *Daga al almin* Maman Ihsan 09065327995 Love you Oll *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau *SADAUKARWA GA* _Jajirtattu Writer's association_ *TUKUICI NE GARE KA* Yusuf Gumel jajirtaccen marubuci gwanin fikira karamcinka gare mu ba zai fa u ba Allah ya arawa rayuwa albarka da kwanciyar hankali. *BISIMIILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5 Mamaki ne ya cika Adamsy, to ina ya ke? Shiga cikin motarsa ya yi ba tare da ya aga wayar ba. Humiara ta kalle shi ta ce, "Ina wannan mahaukacin da ka kusa ka ewa ya ke?" "Kema baki gansa ba?" Kai ta girgiza tare da cewa "Na ga kuna magana da shi, daga nan kuma hankalina ya dauke daga gare ku, ko da na aga kaina kuma sai na ga kai ka ai ne ban gansa ba." Shiru ya ya yana nazari ldan abun ya bashi mamaki matu a, yadda lokaci guda ta ace babu shi babu alamarsa ko sama ko asa. Wayarsa ce ta sake ruri a karo na biyu, Abdallah ne ke kiransa, agawa ya yi cikin sanyin murya ya ce, "Assalamu alaikum" Daga can angaren Abdallah ya ce, "Wa'alaika salam kun isa lafiya?" "Bamu isa ba tukuna, muna hanya." "Kuna hanya?" "Eh" "Amma kun tsaya wani wuri ne ko?" "Ina cikin tu i ne tsautsayi ya gifta saura ka an na ka e wani mahaukaci." "Subhanallahi. Bai ji ciwo ba ko?" "Allah ya kare ba abunda ya sa me sa, sai dai yana mani wasu zantuttuka wanda hankali bazai auka ba." "Kamar ya ban gane me ka ke son fa a mani ba." "Wai cewa ya yi wai Ummata ba mahaifiyata ba ce, wai azzaluma ce kuma wai..." Bai arasa maganar ba dan takaici ma abin ya ba shi, orawa ya ya da cewa "Kai mu bar maganar kawai dama tunda na kalle shi na san ba hankali ne da shi ba. Dan haka maganar ma bata da amfani, bari mu arasa guda ga lokacin sallar magrib ta yi." Jinjina kai ya yi tare da cewa "Allah ya kai ku gida lafiya." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran wayar. Tada motar ya yi suka bar wajen. Dan dama ba yawan mutane a hanyar. Koda suka isa gida an fara kiraye-kirayen sallar magrib, dan haka suna zuwa gida alwala alwala Adamsy ya yi ya nufi masallaci. Itama alwalar ta yi ta gabatar da sallar. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan ta tashi daga kan sallayar, bayan ta idar da sallar. Shima a bangarensa sai da ya yi sallar isha'i ya dawo gida, kamar yadda ya zame masa abi'a. Haka ya ke tafiya a hankali zuciyarsa cike da tunanin wannan mutumin, babban abinda ya aure masa kan shi ne, yadda a cikin da aya ya