Sashe 1
Adamsy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Table Normal No List Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_ *Alk alaminmu yancinmu* *GARGA Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Ina mai matukar ara godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan sabon littafin nawa *ADAMSY* idan akwai wani sharri wanda zai amfane ku ina ro on Allah kada ya bani ikon gama rubuta wannan labarin,ina ro on Allah ya bani ikon rubuta abunda zai amfani al'ummar musulmi. Alkhairin da ke cikin wannan labarin Allah ya sada mu da shi, ina ro onku kada kuyi amfani da abinda ba alkhairi ba da kuka ci karo da shi a cikin littafin nan, kuyi amfani da darasin da ke ciki, sannan ku tsoraci mai sunan eya (Danasani) dake cikin littafin, ina fatan zaku kar i wannan littafin na *ADAMSY* kamar yadda kuka kar i littafin Inteesar koma fiye da yadda kuka kar i Inteesar. Page0 Aguje ta fito daga cikin akinta tana ihun naman taimako,mayafinta ne ya fa i ya har afarta wanda hakan yasa ta fa asa. Fitowa yayi daga akinta yana wala mata kira. "Husnah! Husnah!! Husnah!!!" Tana ganinsa ta rintse idanunta tare walla ara, kanta ta cusa a tsakanin gwuiwarta. Amina ce ta fito daga akinta sakamakon jin ihun Husnah ke yi, cewa kin mamaki ta kalle su tare da furta cewa "Lafiya kuwa amaryar da aka kawo daddaren nan wa anda suka kawo ki ma ko awa aya basu yi da tafiya ba ki fito kina ihu me ke faruwa?" Jin muryar Amina ce yasa ta Husnah ta mi a da sauri ta nufi bayanta, oyewa take a bayanta kamar wacce za'a kama. "Adams wai me ke faruwa ne? Naji ihunta ne yasa na fito cikin tashin hankali dan ganin me ke faruwa, amma abin mamaki sai naganku ku biyu akwai abinda ka mata ne?" Girgiza kansa yayi cikin damuwa ya ce, "Nima abinda ke bani mamaki kenan, lokacin da muka shigo da abokina tana tare da awayenta, bayan anyi siyen baki sun tafi sai na bisu na raka su, kuma iyakar ofar falon nan na tsaya suna fita na rufe ofar, dawowa ta yanzun nan ina ina shiga naga ta kalle ni ta walla ara." Amina ce ta janyo Husnah daga gefenta, zuba mata ido tayi tare da cewa "Husnah me ke damunki ne?" Kuka kawai take mara sauti, idanunta kuwa kamar an bu e fanfon ruwa. Ganin bata da niyyar yin magana ne yasa Amina ta kalli Adamsy tare da cewa "Ko dai tana da wata larurura ce?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bana tunanin akwai wata larura a tattare da ita, dan da akwai da Ummanta ta sanar da ni" Kallon Husnah Amina tayi tare da cewa "Kinga yanzun dare yayi arfe goma sha biyu saura kwata, ki je ku kwanta." Ba musu ta nufi akinta yayin da shi kuma ya sunkuya ya auki mayafinta yabi bayanta suka wuce. Tura ofar akin ta yi ya shiga yana biye da ita a bayanta, bakin gadon ta zauna kanta a sunkuye, jin muryarsa tayi ya kira sunanta a hankali. "Husnah" A hankali ta ago kai ta kalle shi, gangar jikinsa ne kawai nasa amma kansa sam baiyi kama da na mutane ba, dan aho ne ta gani a kansa ga fuskarsa buzu-buzu da gashi, idanunsa kuwa jazir, wani irin ara ta sake saki wanda ya fi na azu a guje ta ruga sai da ta ci karo da ofa kafin ta fita. Amina da ke arin shiga akinta ne ta jiyo ihun Husnah, dakatawa ta yi tare da juya bayant, idanunta suka sauka a kan Husnah da ta fito a guje kafin ta ankare har Husnah ta rungume ta tana kuka, cikin mamaki ta ce, "Husnah me ya ke damunki ne haka? Kina ta ihu baki ga dare yayi ba ko so kike ki tara mana jama'a a daren nan dan Allah ki je ki kwanta." Girgiza kai tayi tare da cewa "Wallahi bazan bishi ba tsoro yake bani" "Ban gane tsoro yake baki ba, ba mijinki bane?" Shiru tayi bata sake magana ba, Amina ce ta maida dubanta ga Adamsy dake tsaye yana kallonsu ta ce, "Wai me ke faruwa ne? Ya daga kawo maka amarya yau sai matsaloli ke ta kunnowa tunda jama'a suka watse?" "Amina bani da amsar tambayar da kika mani, dan nima haka naganta tunda na shiga ta kalle ni take ta ihu." Jinjina kai tayi tare da cewa "Kodai tana da ta in hankali ne?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bana tunanin haka, sai dai idan wani abin ne daban, amma Husnah bata da kowane ta in hankali." Amina ce ta janyo hannun Husnah suka arasa jikin kujera, zaunar da ita tayi akan kujera tare da cewa "Husnah me ke damunki? Dama kina irin haka ne?" Kai ta girgiza tare da cewa "Bana komai shine ya ke canza siffarsa idan muka shiga aki, yake firgita ni" Kallon juna sukayi Adamsy da Amina suna mamakin jin kalamanta, inda ta cigaba da cewa. "Ke Aunty bai ta a canza maki siffarsa ba, idan kina tare da shi?" Kai Amin ta girgiza mata tare da cewa "Mijina ba wata siffa da yake da shi ko yake canza mani, ke dai sai dai kina da wata larura ne da yasa hakan take faruwa da ke, to wane irin canza siffa kamar wani aljani?" Da sauri ta kalli Amina tare da cewa "Eh wallahi Aunty ai kamar alhani haka nake ganinsa." arasa maganar tana fashewa da kuka. "Ke kin isa kiga aljani da ido ko?" Amina ce tayi mata maganar tana nuna ta da yatsarta manuniya, inda ta cigaba da cewa. "Kinga ki kwantar da hankalinki ta yiwu ma mafarki kikayi kike tsorata, idan kuma ba haka ba tabbas kina da ciwon hauka." "Wallahi gaskiya nake fa a maki ki yarda da magana ta, ni bani da ciwon hauka lafiya ta alau, ni da ido na na ganshi bayan ya raka abokansa ya dawo yana shie ya fara tsoratar da ni. Amma lokacin da suke nan bai yi komai ba ya tsaya a yadda yake, bayan tafiyarsu ne sai ya fara canza siffa kamar na aljani." Adamsy kam zuba mata ido yayi yana kallonta, ya ma rasa abin fa a, kai tsaye ya koma akin zuciyarsa a cunkushe. Amina ta dinga rarrashin Husnah tare da bata ha uri kam ta tashi da daure ta bi mijinta, sai da ta tabbatar ta an saki jiki sannan ta raka ta har bakin ofar ta tura mata ofar, ta shiga sannan ta janyo masu ofar ta wuce zuwa akinta. A hankali cikin tsoro Husnah ta ago idanunta ta kalli Adamsy, sai ta nufi ofar fita a guje, biyo bayanta yayi shima cikin hanzari yasha gabanta, wanda hakan yasa ta kalle shi tsabar tsorata yasa ta zube wajen asa sumammiya. Zama yayi akan aya daga cikin kujerar dake falon tare da yin tagumi yana fa "Na shiga uku" Ruwa ya uko a fridge, ya alle marfin robar tare da yayyafa mata a jiki, a jiyar zuciya ta sauke mai arfi, tare sakin kuka, a hankali ya kira sunanta. "Husnah" e ido tayi tare da sauke shi akansa, take ta fashe da kuka tana ja da baya cikin tsoro. Ganin haka yasa shi mi ewa ya nufi akinsa, tare da fa "Ki tashi kije akinki ki kwanta, sai da safe." Daga nan bai sake wata magana ba, akinsa ya shige yana magana shi ka "Wai wannan wane irin daren farko ne? Ace kayi aure ranar da aka kawo maka mata ta dinga gudunka tana tsoronka kamar taga wani dodo? Daren da yakamata ace nayi kwanan farin ciki sai gashi na yi kwanan ba in ciki?" Babbar rigarsa ya cire ya nufi toilet zuciyarsa cike da sa e-sa e iri-iri . angaren Husnah kuwa tana ganin ya shiga akinsa sai ta mi e tsaye, a guje ta nufi alibta tana shiga tayi saurin murza key tare da dur ushewa a wajen, ta jingina bayanta da ofar ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kallon agogon bangon da ke akin tayi, ganin arfe aya na dare yasa ta sakin kuka, dan ba zata iya fita a wannan lokacin da da ta fita, amma ina dare ne a tsorace ta ke , ba zata iya fita ba, Nan ta cigaba da kukanta ita ka ai ba mai rarrashinta. Misalin arfe biyu da rabi na daren ne ta ji barci ya ci arfinta, duk da cewar ita batayi niyyar barci ba amma kuma barci arawo ne lokacin da zai sace ka ma ba zaka sani ba, tashi tayi a hankali ta nufi bakin gadon ta kwanta, ko hasken akin bata rage ba haka ta kwanta dan a tsorace ta ke. Adamsy ma a angaren sa ma bai samu barcin kirki ba, dan tunda ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da auro alwala ya fito, jallabiya ya saka sannan ya shimfi a sallaya, sallar nafila ya gabatar raka'a hu u, ya dinga jera addu'a akan wannan matsalar da ta tunkaro masa, ya da e yana addu'a kafin ya shafa, arfe biyu ya kwanta. Misalin arfe biyar na asuba ya farka, ganin ya kusa makara ne ma yasa ya nufi toilet ya auro alwala, shiri zuwa Masallaci yayi inda ya fito dan zuwa sallar asuba. Sai da ya tsaya ofar akin Amina yayi mata knocking dan ta farka lokacin sallah yayi, jin motsi alamar ta tashi ne yasa shi tafiya, ya tsaya ofar akin Husnah da ba niyyar buga mata ofar, amma tuna cewa zata iya rikece mashi da asubar nan yasa shi fasawa, yayi ficewarsa dan zuwa masallaci. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa