← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 95

Sashe 95

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 4 min read

Na zauna a gefen Papa da yake gaban Abbansu yana duba nashi takardun cikin gyada kai, da yake yaron tubarkallah akwai ilimi, mawuyaci ne suyi jarabawa yaci kasa da casa'in a cikin dari.
Bayan ya gama dubawa, ya janyo yaron cikin jikinshi yana shafa kanshi, yace "good boy, kayi kokari sosai Baba na. A cigaba da kokari ko?".
Yaron ya gyada kai cikin murmushi, yace "that's my boy", tare da bashi peck a kumatu.

Yaron ya wani yatsina fuska, Yayan yana dagawa yasa bayan hannu yana goge kumatunshi, yace "ewww Abba!". Ni dasu Yayan me zamu yi idan ba dariya ba? Yaya ya kama kumatunshi duka biyun yana ja, yace "Babana har yanzu baka daina jin kyankyami na bane?".
Na shafa kan yaron ina murmushi, haka Allah ya halicce shi da son jiki da kyankyami.

Ya maida hankalinshi ga Muhaaseen da tayi shiru a zaune tana kallonsu cikin dan murmushi. Ita kuma kunya da kawaici ne da ita kamar me, abinda wani lokacin nake cewa mai sunanta ta biyo.
Yace "Maama fa, ya ake ciki ne?".

Awa daya da kusan rabi yana ta hira ne da yaran nashi, ya dauko tsarabar su ya kunce musu, kowa aka bashi nashi. Daga nan ne suka mana sai da safe, kowa ya nufi dakinshi. Suhaima kuwa tana kwance akan cinyar Yayan tana barci.

Bayan tafiyar su ne muma aka kunce mana tamu tsarabar. Kaya ne na ado iri-iri, dogayen riguna, takalma flats da heels da kayan su jikkuna masu kyau da burgewa, turaruka da sauran tarkace. Muka hau mishi godiya sosai, Hajara tace "Abban Maama mu kam kana shagawaba mu da yawa wallahi, mun gode, Allah ya saka da alkhairi Ya kara budi mai amfani".

Yace "ai ban muku komi ba cikin abubuwan da kuke yi min, hadin kanku ma kadai ya isheni, balle kuma tallafawarku a gareni da kulawar da kuke bani. Allah dai yayi muku albarka, Allah ya kara hade min kanku gabadaya".
Duk muka amsa da "ameen", a tare.
Abinda ke kara mana kwarin gwiwar kyautata mishi kenan, Yaya baya kyashin yabonmu a ko'ina ne, a kuma gaban ko waye sai dai idan bamu yi abinda ya burge shi ba.

Bayan mun zauna, yace "yaushe yara zasu samu hutun makaranta?".
Nace "nan da sati hudu muke sa rai".
Yace "to ku shirya, umara zamu je gabadaya har yaran".
Muka kalli juna ni da Hajara, kafin muka saki ihun murna muka dira jikinshi muna ihun murna da godiya. Aikin hajji kam mun je shi babu iyaka, mun fara zuwa ni da Yaya, muka koma har Hajara. Haka su Malam ma shekarar data wuce suka je suka sauke. Shi dama Baba yaje ya kai matanshi.
Ranar har wajen karfe sha daya da rabi muna falon ana ta hirar yaushe gamo, kafin na mike tsaye ina musu sallama.
Hajara ta kwashe kayanta ta kai daki bayan ta kai Suhaima ta kwantar a dakin Yaya, Yaya ya taya ni kwaso kayana muka kai dakina.

Yana zube kayan akan gado ya juyo ya janyo ni jikinshi, ya nutsa kanshi a cikin gashin kaina, nayi yar dariya tare da zagaye hannuwana a bayanshi.
Yace "ya kike, ya babynmu, hope baya matsa miki ko?".
Nayi dan murmushi, "dukkanmu lafiyarmu lau. How was your trip?".
Yace "Alhamdulillah, mun samo fiye da abinda muka je nema".
Nace "to madallah, haka ake so".

Mun dan jima a haka, kafin na dago kaina na kalleshi, "kada fa ka tsaida Hajara da jira, nasan itama tayi kewarka, sai da safe ko?".
Yace "wato har kin gaji da ganina kenan?".
Nayi dariya ina kama baki, "ni har na isa in ce na gajii da kai? Ban ki mu dawwama a haka ba. Amma bana so mu shiga hakkinta ne ko kadan".

Yace "to shikenan, sai da safe".
Nace "sai da safe, ku tashi lafiya".

Ya wuce gaba na bishi a baya, a bakin kofa ya juyo ya manna min sumba a goshi, sannan ya juya ya tafi. Nayi murmushi kawai tare da girgiza kai, na maida kofar na rufe tare da murza makulli.
Shirin kwanciya barci nayi, na kashe wuta na bi lafiyar gado.

*_...Alhamdulillahi Rabbil-Aalameen. Masha Allah La Quwwata Illah Billah!_*
*Da haka muka kawo karashen littafin 'A Zato Na'. Ina fata Allah yasa mu fi karfin zukatanmu, Allah yasa kuma mu amfana da sakon da wannan littafi yake dauke dashi. Kurakuran dake ciki, Allah ya yafe mana, ameen.*

*Ina mika sakon dumbin gaisuwata da fatan alkhairi ga daukacin jama'ar ZAB, bamu da bakin yi muku godiya da baku hakuri amma duk da haka zan kwatanta. Mungode, Mungode, Mungode, Allah ya kara dankon zumunci. Bamu so abubuwa suka kai har haka ba, mun gode kwarai da hakuri da tarin uzurirrika da kuka mana, bamu da abin cewa sai Allah ya kara dankon kauna kawai. Fatan alkhairi gareku bakidaya! Jeedderh Loves you all!* 😘 ♥ ♥ ♥
Chapter 95 · 0% Book details