← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 95

Sashe 74

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da aka turo min kudin na gansu kamar a mafarki, har sai da nayi hawaye. Yau dai wahalhalun nan da muka sha, sun fara biya. Na shiga kasuwa, siyayya tun daga kan su Auwal, har matan Baba da shi kanshi, babu wanda ban ssiyawa abu ba, haka su Fatsu dasu Yaya.

Anyi hakan da kwana hudu, na tafi Gashua. Yaya ya sai min tiket din jirgi wanda ya sauke ni a Yobe, daga can na wuce Gashua.
Ba karamin jin dadin yadda na samu su Fatsu nayi ba. Yan biyun Yaya suna ta guje-gujensu da surutu. Sai lokacin naji cewa ashe bayan aurenmu, sau biyu Yaya yana zuwa suna gaisawa. Bai kuma taba gaya min ba. Yanzu ma da zan taho haka ya hado ni da kudin tsaraba wadda sai da nazo nan sannan na siya abubuwan da zan raba. Kamar kullum, a gidan Fatsu na sauka.

Kwana na biyu ina yawon gaisuwa da ganin dangi, ana uku ne muka je Kauyen Alkali wajen Anty Halima. Ba karamin murna tayi da ganina ba. Muka mata yini ni da Sailu da twins, sai da yamma sannan muka koma. A gidan su Sailu muka sauka, na zube akan kujera ina nishin gajiya. Tunda nazo nake a gajiye, barci bai taba isata ba, wanda nafi danganta hakan da gajiyar mota.

Sailu kuwa tunda muka zo ta fada kicin ta hau girki, nan da nan gida ya bade da kamshi. Ina so inje in tayata yin girkin, amma kwata-kwata na kasa motsawa. Wani irin barci ne ya fara fuzgata ba tare dana shiryawa hakan ba.

Sailu ta fito daga kicin, ganina a kwance yasa ta dakata tana kallona, Malam da Abul-khairi suna ta wasan su a tsakiyar falon. Na dago kai a dan galabaice ina kallonta, tace "wai lafiyarki lau kuwa? Tunda muka dawo kika wani langwabe a kan kujera kamar wata mara lafiya?"

Nace "wallahi nima ban sani ba, ina ga kamar gajiyar hanya ce har yanzu bata sake ni ba".

Ta kyalkyale da dariya, "hahh, ina ruwan ba sabon shiga ba! Idan ma zaki warware ki san abinda yake damunki, ki mike. Ko in zo inyi palpating dinki ne?".

Na tashi zaune da kyar, "palpat... me??", na zaro ido, "ba fa haka bane, bani da komi, da gaske".
Ta gyada kai tana dan murmushi, "kada ki wani gaya min ba haka bane, duk ga alamu nan sun bayyana a jikinki?".

Nace "kin dai san wannan abin fannina ne ko? To bani da komi da gaske".
Tace "to ai shikenan, kada dai ki koma barci don an kusa kiran sallah". Ta koma kicin, nima haka nan na tashi na bita kenan din ko jikina ya dan warware.

Kwana na biyar cur anan, sannan na musu sallama na tafi. Wannan karon motar Kaduna muka wuce kai tsaye, sai wajen karfe hudu muka shiga cikin Kaduna. Jikina yadda kasan an yi min dan banzan duka haka nake ji, ban taba jin wuyar tafiya ba sai yau.

Direban gidan su Ummah yaje ya dauko ni daga tasha zuwa gidan. Nan na samu tarba mai kyau daga wajensu. Su Firdausi suna makaranta, aka kaini dakinsu nayi wanka da sallah, sannan naci abincin da aka kawo min. Saboda gajiya ma ban iya cin komi ba, na koma na baje anan kusa da kayan.

Sai da Yaya ta leko sannan na tashi da kyar, ganin yadda nayi daidai yasa tayi dariya, tace "ki koma kan gado mana ki kwanta, kwanciya a kasa ba dadi, ga sanyin tiles. Ke kuwa yanzu sanyi zai iya cutar daku a halin da kike ciki", ban fahimci komi take nufi da mu ba, na tashi na koma kan gadon na kwanta dai.

Washegari a gidan Janan na yini. Itama tunda na isa, zancenta daya, na harbu. Duk yadda naso in fahimtar da ita akan ba haka bane, kin yarda tayi.

Tana dariya tace "wai ki hakikance akan abinda baki gwada kin tabbatar da gaske bane ko ba haka bane? Ni naga abinda na gani, ke dai da idanuwanki suka rufe kika kasa ganin komi, sai kije kiyi tayi".
Na kada mata idanu sama, na dauki kankarar da ta dalilinta ne maganar ciki ta taso, na kai baki ina harararta, "sai kuci gaba da lakaba min abinda bani dashi ai, ku zaku yi disappoiting din kanku!".
Tace "to ai shikenan, zamu gani".

Sai da nayi sallar la'asar sannan na mata sallama, muka wuce Abuja.

*☆⋆43⋆☆*

Saboda tsabar gajiya washegari ko asibiti kasa zuwa nayi. Yini nayi cur akan gado, ga yunwa da take ta rarakar min ciki amma na kasa samun kuzarin fita. Sai yoghurt da maltina nayi ta durawa a cikin cikina wadanda na jera su a cikin firjin, har sai da naji kamshinsu yana neman sanya ni amai sannan na kyalesu.

Sai can da yamma sannan na iya tashi, wani abin mamaki kuma babu gajiya balle ciwon jiki, sai lokacin nayi wanka, na dauki wata doguwar riga yar Saudiya, ruwan madara na saka a jikina. Nasan lokacin Yaya ya kusa dawowa daga wajen aiki, ranar Raheemah ce take yin girki.
Falon Yaya na wuce, wayar hannuna a hannuna. Sai da yammar nan sannan naga tarin kiran dana rasa da sakonni, tunda na dawo wayar take cikin jaka, ban daga ta ba sai yanzu.

Yaya Bilal naso in fara kira ganin kiranshi har sau uku, da sakonshi da yake tambayar lafiya ban dauki wayarshi ba? Sai dai ina zama, sai gashi ya fado falon. Da alama yau ya tashi da wuri daga wajen aiki.
Na mishi sannu da zuwa, daidai lokacin da Raheemah da Ameerah suka shigo suma kusan a lokaci guda. Ya amsa yana kokarin cire neck tie din shi, "lafiya nayi ta kiran wayarki baki dauka ba?".
Nace "gajiyar hanya ce ta hana ni ko motsi yau wallahi, sai yanzun nan na gani".
Yace "ok", ya shiga daki, Raheemah ta bi bayanshi, Ameerah kuma ta samu waje ta zauna.

Babu wanda yayi magana a cikinmu, ni Janan ma na kira da naga nata missed call din, muka sha hirarmu da ita har sai da Yaya ya fito zai tafi masallaci, sannan muka yi sallama. Nima dakina na wuce da niyar yin sallar na bar su anan.

Sai da naji motsinsu a babban falo sannan na fita nima.
Yaya na zaune akan kujera, su kuma sun sanya shi a tsakiya. Sai naja kujerar dake fuskantarsu na zauna.

Raheemah tana bude kwanon abincin, wani kamshin kifi daya bugo min hanci, ba shiri na ja da baya ina yatsina fuska. Wani irin yawo naji diyan hanjina suna min a cikin cikina.

Kwana biyu na kula yanzu tana kokarin zubawa Yaya abinci da kanta ba kamar farkon dawowarmu ba. Ko kuwa don taga daga ni har Ameerah ba ma barinshi ko ruwa ya zuba da kanshi? Ita dai ta sani.

Sai dana bari duk suka zuba nasu, ina kallo Ameerah tayi wancakali da nata plate din, ta tsoma cokalinta a cikin abincin Yaya. Na jinjina kai kawai tare da jan plate nima na fara zubawa kaina. Macaroni ne jollop, da ya sha kifi da nama sai lemun exotic na abarba da kwakwa, da ruwan gora. Duk yadda nayi ganin cewa na hana warin kifin nan damuna, kasawa nayi, don haka abincin ma kadan na zuba kawai. Idan da ba don yunwar da nake ji bama, babu abinda zai saka ni cin abincin nan. Haka nan dai na cije baki na kai cokalin farko bakina. Tun ma kafin in saka shi a bakin nawa, wani irin amai ya tuko ni kamar me.

Da sauri na ja kujerata baya na tashi cikin sauri na fada bandakin dake nan cikin falo, ina shiga na fara amayar da duk abubuwan dake cikin cikina.
Yaya daya biyo bayana da sauri, ya fado bandakin shima. Shi ya taimaka min na tashi saboda yadda nake jin gabadaya gabban jikina sun kasa motsi ga wani jiri da ciwon kai. Ya taimaka min na wanke bakina, ya gyara wajen dana bata sannan ya tallabo ni muka koma falon. Matan nashi na zaune, suka biyo mu da kallo har ya kwantar dani akan kujera.
Ya juya ya kallesu yace "Raheemah miko min ruwa".

Bata ce komi ba, ta dauko gorar ruwa daya ta tashi ta kawo mishi. Ya tallabo ni na dan tashi zaune, ya kafa min gorar a baki, dan kadan na sha na koma na kwanta. Ya rufe gorar ya ajiye, ya dafa kaina da tunda muka fito nake dafe dashi.
Murya cike da damuwa yace "me yake damunki ne? Dama baki da lafiya ne?".

Na girgiza kai a hankali, "a'ah, ciwon kai ne dai nake ji kadan, da alamu na gaji ne da yawa".

Yace "me zaki ci to, zaki iya cin abincin in kawo miki wani?".
Gabadaya na rasa kuzarin yin magana, kai kawai na iya girgiza mishi.
Yace "to me kike son ki ci?".
Nan ma na sake girgiza mishi kai, ya dan yi frowning, "kin san ba zan taba barinki ki kwana da yunwa ba ko baby? Ki fada min abinda kike son ci idan na dafawa ne sai a dafa miki".

Nayi shiru ina tunanin abinda zam ce mishi amma kuma ji nake kamar duk duniya babu abinda zai iya shiga cikin cikina yanzu. Ya fara jero sunayen abinci kala-kala, har da su Chinese da Italian, daga karshe dai nace mishi salad.

Ya shafa kaina har yanzu damuwar fuskarshi bata bar shi ba, yace "bari yanzu a siyo miki, sannu kinji?". Na gyada mishi kai, shi kuma ya tashi ya dauki wayarshi. Ban san me yace ba, na dai ji yana maganganu kasa-kasa, yana gamawa ya dawo kusa dani ya zauna. Ba ayi minti talatin ba, aka kawo salad din a cikin take away, na tashi zaune shi kuma ya zauna a kusa dani. Da kanshi ya dinga bani, na kuma samu naci da yawa.

Ina gama ci, na tashi nace mishi zan wuce daki in kwanta, nan na musu sallama, yana biye dani har zuwa dakina. Da kanshi ya taya ni sanya kayan barci sai da yaga na kwanta sannan ya kashe min wutar dakin. Babu jimawa barci ya dauke ni.
Washegari na koma bakin aikina.

*
Chapter 74 · 0% Book details