← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi maganar abinci sannan naji cikina yana juyawa, ba musu na tashi na cire hijabin jikina na ninke ta da abin sallar. Tun kafin in zauna kamshin kifi ya cika min hanci, naji yawun bakina ya guda. A kasa na zauna muna fuskantar juna, ta turo min plate cike da faten doya. Anyi garnishing dinshi da green beans, peas, alayyahu, hanta da aka yanka kanana, ga kifi da dafaffen kwai a gefe. Ina yin loma daya na lumshe idanuna, kai na hau girgizawa, "ramgwadi! Gaskiya yau ba karamin baje basira kika yi wajen girkin nan ba, meye sirrin?".

Ta kalleni, "ke yanzu nace miki ni na dafa wannan abincin yarda zaki yi? Yanzu na amsa shi wajen Anty Sarah".
Na bude baki cikin mamaki, watakila lokacin da yan kirki suke kan Anty Sarah bamu taba sa'ar cin karo dasu ba sai a wannan lokacin. Iyaka sanina da ita, wannan baya daga cikin halayen dana santa dashi. Amma zata iya yiwuwa dama can hakan take, kila sanin hakan ne bamu taba yi ba.
Nace "ta kyauta sosai, nagode".
Ta kai cokali daya bakinta, "ta shigo ne taga yanayin jikina fa sai ta ganki da drip a hannu. Dazu kuma sai ta turo Mimah tace in je in amsar mana abinci". Na gyada mata kai. Har muka gama cin abincin babu wanda ya sake yin magana. Bayan mun gama, Janan ta kauda kayan can gefe, ta dauko magungunan ta fara balla tana miko min. Da kyar na iya watsa su a baki na hadiye. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa naki tashi dazu da safe zuwa asibiti yana nufin allura da magunguna, ni kuma bana son allura da magunguna.

Janan ta harareni lokacin dana hadiye kwayar maganin karshe da kyar, na fara kakari. Tace "dazu ai da ana tsira miki allura a jiki ko a jikinki".
Nace "kema kin san saboda bana cikin hankalin kaina ne, amma ina ji ina gani in zauna a tsira min allura? hauka nake?".
Ta kwashe da dariya, na harareta, "muguwa kawai!". Gwalo ta min kamar wata karamar yarinya.

Tashi tayi ta dauki kwanukan ta fita. Na lallaba na lalubo wayata daga bayan katifa inda na jefata jiya. Nasan anyi ta nemana babu kakkautawa, musamman ma Muhammad. Na kunna wayar na tsaya tayi loading kafin na bude ta, nayi gaskiya kuwa. Sakonni daga Muhammad sun fi cikin kwando, tambayarshi daya, lafiya? Na hade fuska lokacin dana kula daga cikin sakonnin akwai na Umar, ko kara kallonsu ban yi ba na goge su gabadaya. Na tafi dungurungum nayi blocking dinshi daga wayata.

Komawa nayi daya bayan daya ina karanta sakonnin shi. Duk karantawar da zan yi, zuciyata kara narkewa take yi cike da begen shi, Allah ya sani, a kullum kaunar bawan Allahn nan kara yado take yi a sassan zuciyata. Ban sani hakan ko abu mai kyau bane ko kuma akasinsa. Kafin in gama karantawa jikina yayi wani irin sanyi, daga cikin kalaman shi kawai, babu tantama zaka karanci tsananin kulawa, tsantsar so, da kauna mara iyaka a cikinsu. Jikina yayi sanyi saboda babu mahalukin daya taba nuna min kwatankwacin irin wannan so, kauna da kulawar da wannan bawan Allahn yake nuna min. A duniya yanzu waye yake damuwa kawai don ya kira wayar wani daga dare zuwa safe ya ji a kashe? Sai Muhammad. Sai daya kai ga tambayar ko dai wani laifi yayi min ne, a cikin sakon. Ina gama karanta shi na lalubo lambar shi na danna kira, ban ma san me zan ce mishi ba. Sai dai cewa aka yi line busy, alamun yana waya. Don haka naci gaba da karanta sauran sakonninshi, nasan idan yaga missed call dina zai kira.

Janan ta dawo dakin da waya a kunnenta, daga yanayin yadda take maganar da Yaya Bilal take wayar. Hankalina yana kan sakonnin M.B da nake ta nanatawa, kamar wani karatu. Don haka sama-sama nake jin muryarta a kaina. Bayan ta gama ta zauna a gefena, tace "Yaya ne ya kira yana tambayar ko kin tashi nace eh. Yana Funtua shi da Anty Ameerah, wai ya kaita wajen sunan kawarta," ta fada tana tabe baki, ni kuma na dan murmusa saboda yadda ta bani dariya, "yace a duba ki da jiki dai kafin ya dawo".
Nace "babu komi wallahi, ai na warware".

Tace "yauwa, na ma tuna! Ummah tace tana so ta duba ki itama". Ta ciro wayarta ta kirata, bayan sun gaisa sun yi yar hira, Janan ta miko min wayar na amsa, na gaisheta cike da girmamawa kamar tana gabana. Tace "Janan dai ta goga miki, daga zuwa jinya sai kema ki buge da jinya?", ni da Janan muka yi dariya sosai. Mun jima muna hira da ita, Ummahn su Janan ta iya bi da mutum cikin sanyin kalami kaji ka saki da ita, akwai lokuta da dama da zamu fara hira da ita cikin dari-dari ko rashin sakin jiki, amma cikin dan kankanin lokaci zan ji na saki da ita sosai, inji na hau hira da ita sosai. Wasu lokutan sai daga baya zan zauna ina mamakin hakan. Munyi sallama da ita tana ta zuba mana addu'o'i kamar yadda ta saba, na kashe wayar na mikawa Janan.

Kwanciya tayi rigingine tana kallon ceiling din dakin, ni kuma na lalubo game din candy crush a wayata ina bugawa. Shiru ya ratsa dakin na dan wani lokaci, can naji tace "Nan da sati biyu Yaya zai tafi umarah shima".
Na kalleta cikin mamakin dalilin da yasa ta fada min, nace "and?".

Ta kalleni tana wani yin kasa-kasa da idanu, "don Allah kizo ki taya ni zama kafin ya dawo!".
Na zaro ido, "wa? Ni?? Ki rufa min asiri in mutu maza su kaini ba mata ba! Ana zaman lafiya, da hankalin kaina, anya kina ma so na kuwa?".
Ta harareni, "yo meye na wani zaro ido? Wuta nace ki zo ki taya ni zama?".
Na koma na kwanta ina dariya, "lallai ma, zama a gidan nan naku ai sai wanda ya shirya, ni kuma ban shirya ba. Jira nake goben nan tayi, idan na cira kafa na bar nan gidan sai kuma baba ya gani. Idan da son rai na ne ma, har in bar Zaria ba zan kara zuwa nan ba!".

Tace "inaa, kema kin san wasa kike yi coz you are stuck with me babe, babu yadda zaki yi dani. Sannan gobe babu inda zamu je sai jikinki ya kara yin kwari sannan, maybe zuwa talata?".
Na kalleta ina dan murmushi cike da jindadi, "babu wani hutu da nake bukata don ni nan garas nake ji na, amma kuma wa zai ki hutu koda na kwana daya ne musamman daga wannan asibitin?". Itama tayi murmushi.

Karan da wayata tayi ne yasa na kalli hannuna duk da kida na musamman ne, na riga nasan mai kiran. Na turo baki cikin shagwaba, ban san dalili ba, duk lokacin da nake tare da Muhammad, na kan ji ni kamar wata yarinya karama, kamar wata sabuwar halitta.
Cikin shagwabar na daga, yana ta magana nayi shiru, yace "haba baby na, come on, talk to me mana. Nayi laifi ko? Am sorry!". Nayi shiru ina jinshi ya cigaba da cewa "haba baby na, baki so in ji daddadar muryar nan taki ne? Come on...".

Na turo baki kamar yana gabana, "ba kai bane ka ki daga wayata dazu ba?".
Ya saki murmushi mai sauti, "tuba nake gimbiyata, ina amsa wata waya mai muhimmanci ne. And you are the one to talk, idan maganar gaskiya ake yi ai nine ma yakamata ace nayi fushi. Na ga tun jiya nake kiran wayarki a kashe. Baki ji warin kunar da zuciyata ta dinga yi bane?!".

Ban san lokacin dana kwashe da dariya ba, nace "oohh, da gaske?".
Yace "sosai ma, da yadda nayi ta kiran sunanki. Duk baki ji ba?".
Na sake yin wata dariyar ina girgiza kai cikin wani irin matsanancin farinciki, nace "ban ji ba gaskiya!".
Yace "nayi tunanin gabadaya mutanen Zaria sun ji!". Na cigaba da kyalkyala mishi dariya.

Mun jima sosai muna kwasar hirar soyayyarmu, har na rasa tracing din lokaci. Lokacin da muka yi sallama dashi, bakinshi yana furta I miss you's da I love you's. Zuciyata fara kal, kamar farar takarda.
Janan da tunda na fara wayar take kallona baki a dage, ta kalleni tana murmushi, "anyi nisa a lambun soyayya!!".
Nayi dariya ina birgima a tsakiyar dakin, "baki san komi ba Jan... You've no idea. Ya Allah, I love that man!!".
Dariya ta saki, ta taso ta rungume ni, ban san dalili ba, amma nima rungumeta din nayi. Tace "na taya ki murna, dear. Congratulations!". Nayi murmushi.

#F.W.A

*☆⋆17⋆☆*

Yinin ranar a daki muka yi shi. Bayan munyi sallar la'asar, Janan ta kunna mana film din X-Men a wayarta muka fara shi tun daga farko. Babu abinda ya dinga tada mu sai sallah da cin abinci.

Bayan isha'i, Janan ta tado ni muka fita waje, a cewarta kafa zamu dan wasa musamman ni da babu inda na fita tun yau. Ban damu ba, na dauki hijabi ta na saka muka tafi. Garin tun da yamma tayi yayi alamun hadari, ga wani irin zafi da aka yi kamar zai kona mutane. Sai dai zuwa yanzu ya dan yi sanyi, iska mai sanyi yake bugawa a hankali.
Muka taka ni da ita har bayan layin su, can wajen irin masu suyar wara da doya da fulawa dinnan don Janan tace abinda take son ci kenan yanzu.
Matar inyamura ce, sana'ar hannu take yi tun karfinta, safe, rana, dare, babu hutu balle kakkautawa. Shi yasa wajenta kullum cike yake da kwastomomi da kuma ma'aikatan da suke kama mata aiki.
Saboda yawan mutane yasa bamu samu mun siya da wuri ba, lokacin da muka tsaya a gabanta, ta kallemu cikin murmushi. Ba laifi mun dan saba da ita, saboda a yawancin lokuta a wajenta muke sayen buns da eggroll da rana. Ta kalli Janan tace "kwana biyu kun dauke mana kafa!".
Ni da Janan murmushi kawai muka yi muka gaisa da ita. Ta kulla mana wanda muka saya a cikin leda, muka amsa muka mata sallama muka juya.
Chapter 32 · 0% Book details