← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 95

Sashe 44

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na sake bude idanuna, har yanzu hasken kan wayata bai mutu ba. Na dinga scrolling sama ina kara karanta sakonnin da muka dinga canzawa a tsakaninmu, kafin in san ko shi din wanene. A da, da ban san ko shi din wanene ba, kawai ina jinshi acan kasan raina ne, yeah, ina son shi, kuma ina kaunar shi, amma yanzu dana san ko shi din wanene finally, sai nake ganin komi daban, at least yanzu idan ina tunaninshi zan ga fuska kuma zan ji murya sosai. Sai dai nasan koma menene nake ji game dashi, dole ne in manta dashi. Ko za'a yi me, nasan cewa ba zan taba amincewa da Yaya Bilal ba.

Saboda haka na kashe hasken wayar, na ajiyeta a kusa dani na rufe idanuna cike da fatan barci ya dauke ni a lokacin.

***

"... Na'ilah?!".

Da sauri na bude idanuna, Janan na zaune kusa dani tana kallona cike da yar damuwa a fuskarta. Na sauke idanuna akan agogo, naga har karfe hudu da rabi tayi. Na tashi zaune ina salati. Tace "har an kira sallah, ki tashi muyi mu leka waje mu ga abinda zamu lalubo na shan ruwa, yau anan zan sha ruwa".

Na mike tsaye, ko don barcin da nayi ne? Jikina naji yayi min wani nauyi. Na tashi na dauki hulata na fita, idanun Janan a kaina. Nasan dalili, mafarkin da nayi ne wanda ta tashe ni a daidai lokacin da bana son tashi, daidai lokacin da nake kwadayi, kuma nake marmarin ganin wannan mutumi da duk duniya babu wani mahaluki da yake kada min sassan jiki kamar shi ba. Amma kullum anan nake tsayawa, ban taba ganin fuskarshi, muryarshi ma haka nan nake jinta sama-sama kamar ba a kusa dani yake ba. Wani lokacin ni nake tashi a karan kaina, watarana kuma sai ayi arashi wani ne a kusa dani zai tashe ni. Koma dai menene, na zubawa sarautar Allah ido ne kawai domin ni kam na kasa gane wannan abu.

Bayan munyi sallah, muka fita zuwa kasuwa muka sayo abubuwan da zamu bukata, muka dawo muka yi yam balls da kunun aya. Har muka gama shan ruwa da ita bata yi alamun sake tado maganar jiya ba, don haka naji na fara relaxing. Cikin annashuwa kamar yadda muka saba muka sha ruwanmu, na tashi na rakata ta hau mota na dawo, na tattare kayan da muka bata na ajiye a inda nake tara kayan wanke-wanke, nayi sallar isha'i.

Daga nan common naje nayi kallo. Karfe goma na dawo daki. Na samu Maimuna da Esther a daki, na musu sannu suka amsa nayi shirin kwanciya barci na kwanta.
Wani irin sad feeling da naji ya rufe ni a lokacin, da ace da ne, da yanzu muna nan muna zuba soyayyarmu ni da Muhammadu na. Me yasa Yaya Bilal ne zai zama Muhammad? Mai yasa ba wani mutum ne daban ba, wanda bashi da mata daya balle mata har biyu? Me yasa? Wai me yasa abubuwa suke zo min ne a hagunce?
Daren ranar yau dai da kuka shabe-shabe nayi barci.

*☆⋆24⋆☆*

Ni a karan kaina nasan cewa idan nace bana yin kewar Yaya Bilal to karya nake yi, ina kewar shi fiye da tunanina. Sai dai wani sashe na zuciyata yasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi. Ko zan mutu, ko zuciyata zata tsattsage saboda damuwa, zama da Yaya Bilal ba zai taba zama maganin hakan ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin na danne duk ma wata kewa, so da bege da nake ji game dashi. Nasan cewa na dan lokaci ne, nan da lokaci kadan zan daina.

Sai dai duk wanda ya ganni, yasan cewa ina cikin damuwa. Idanuna kadai sun isa shaida, saboda bana samun barci mai yawa. Ko nayi, saboda tsananin sanya maganar Yaya Bilal da matanshi a cikin raina, haka zanyi ta mafarkinshi. Watarana ma har da matanshi, wani lokacin kuma barcin ne ma gabadaya baya zuwa.

Yanzu ma muna zaune a cikin ward ni da Janan da wata Aisha, a ranar alhamis kenan. Janan da Aisha ne suke ta hirar su, ni kuwa hankalina yana kan wata calender dake rataye a wajen. A zahiri idan ka kalleni, zaka yi tunanin jerin magungunan dake cikin takardar nake karantawa ko kirgawa, amma a hakikanin gaskiya hankalina ma kwata-kwata baya tare dasu. Tunani nake, tun wannan text din da Yaya Bilal yayi min ranar litinin, har yau bai sake kirana ba, kuma bai sake turo min wani sakon ba. Ta wani bangaren naji dadin hakan, so nake ya barni, ya kyaleni, idan ma da hali ya manta dani. Duk da cewa nasan har abada zan dinga kallonshi da wannan maganar, ba zan taba mantawa ba, sai dai in binne abin acan karshen bangon zuciyata.
Ta wani bangaren kuma tunani nake, dama kirarin da yake akan cewa yana sona duk kuri ne da cika baki? Har ya manta dani kenan? A yadda yake nunawa dinnan, nayi zaton zai zage damtsensa ne har sai inda karfinsa ya kare. Amma dana fara irin wannan tunanin, sai inyi gaggawar katse kaina, idan ma ya ci gaba da bibiyata babu abinda hakan zai sa sai ma kara min ciwon kai da damuwa da hakan zai yi. Don haka gara ma yaje can ya karata da matanshi ya fiye min alkhairi. Shima wannan kuri ne kawai da zuciyata take yi, can can kasanta, tana fatan ace ba haka bane.
Kai wasu lokutan sai inji da ace ana cire zuciyata a sake sabuwa, da na garzaya zuwa ko'ina ne na canza tawa. Komi nisan wajen kuwa.

Nayi nisa cikin tunani, ban ankara ba sai ganin Dr. Na Abba nayi a kaina yana snapping hannuwanshi a fuskata. Nayi firgigit! Kamar wadda ta tashi daga barci na kalleshi.
Yayi dan murmushi, "haba Nas, wannan dogon tunani haka har ina? Idan dai don nine kada ki damu, gani a gabanki. Ba zan matsa ko nan da can ba har sai kinyi min iznin hakan!".

Ban san sanda na saki dan murmushi ba, Allah ya zubawa mutumin baiwar iya ba mutane dariya koda mutum bai shirya ba kuwa, ko kuwa ni ce kadai?.
Yace "haba! Ko ke fa? Ba gashi har kyakkyawan murmushin nan naki ya fito ba? Wallahi ba karamin kyau kike yi ba idan kika yi murmushi!".
Nan ma ban iya daurewa ba sai dana kara yin wani murmushin.

Yace "so what's up? Kwana biyu na daina ganinki anan, nayi zaton ko kin bar ward dinne. Jiya sister Mairo take ce min ba canza ku aka yi. Kin san yanzu evening duty nake yi, ina ga shi yasa bamu cika haduwa ba".
Na dan gyada kai tare da cewa "haka ne kam, ya aiki?".
Yace "Alhamdulillah. Ko kina da yan mintunan da zaki taka min zuwa nan waje Na'ilah? Ba don kowa na shigo da wuri ba sai don ke".

Sai lokacin na kula da cewa yau ba sanye yake da labcoat dinshi ba. Na juya na kalli su Janan da suke yan rubuce-rubuce da danne-dannen waya, amma ni nasan hankalinsu gabadaya a kanmu yake. Na gyada mishi kai a hankali tare da sauka daga kan kujerar da nake, ni dashi muka jera muka fita.
Bai furta min komi ba, nima kuma banyi yunkurin cewa komi ba har muka fita waje. Kaina a kasa yake, ina dai bin sawun kafarshi ne dake sanye cikin takalmi sau ciki, don haka ban san sanda muka isa wajen ajiye motocin likitocin asibitin dake ta wannan bangaren ba, sai dana ji ya ja birki sannan. Ya jingina da jar motar shi 406, ni kuma na tsaya ina fuskantar shi.

Yace "Wato Na'ilah dalilin da yasa na so mu kebance muyi magana dake shine, ina so ne inji inda maganar mu ta kwana ne. Shin, har yanzu kina ganin bani da chance ne a wajenki?".
Na dan yi wuri-wuri da ido, kafin in tsaida su waje daya, murya a shake nace "to ni me zance maka kuma, ina tunanin tun ranar nan na fada maka anyi min miji a gida?".

Yayi dan murmushi, yace "Hmm, Na'ilah kenan! Aka yi miki miji ko kuma kika yiwa kanki miji, kika fada min?".
Nace "kamar yaya? ban gane ba!".
Yace "come on mana, daga jin yadda kike cewa 'ai anyi min miji a gida!', ko dan jariri yaji yasan cewa kin fadi ne kawai don kiji dadin bakinki!".

Ban san lokacin dana kyalkyale da dariya ba, musamman lokacin daya make murya wai shi ala dole kwaikwayo na yake yi. Shima yayi murmushin ya kara jingina da motarshi yana dan murmushi, nayi shiru ina girgiza kai, amma murmushin fuskata bai bace ba.
Yace "da gaske ba. So I'll like it idan kika manta da zancen mijin da ba'a riga an san ko wanene ba, let's talk about us for now. Kamar yadda na fada miki ranar nan, gaskiya kina burgeni. Kuma ina fatan ace zaki bani dama, mu samu fahimtar juna a tsakaninmu. Me kike tunani?".

Nace "magana ta gaskiya ni a halin da ake ciki yanzu likita, babu wannan maganar a cikin raina yanzu. Ina fata hakan bai bata maka rai ba?".
Ya girgiza kai, "ko kadan. Kin san ku mata da jan aji, hakan ba matsala bace a wurina. Zan baki iyaka lokacin da kike bukata, amma ina neman alfarmar dinga yin waya dake zuwa lokacin da zaki sauko?".

Nasan wannan rana ba zata taba zuwa ba, don dai mu rabu lafiya dashi sai kawai na gyada mishi kai. Yayi dan murmushi, "yauwa, nagode. Muje in dan taka miki ko?".
Nayi yar dariya, nace "nayi zaton ni na rako ka?".
Yayi yar dariya, "a'ah, ni na isa? Kawai dai ina so ne mu dan tattauna dake ne a waje dama dai kawai".

Muka sake kwasa muka sake komawa dai, anan ne yake dan fada min tarihin rayuwarshi. Gidansu yana palladan, har kwatance yayi min amma da yake ba sanin unguwar sosai nayi ba ban gane ba. Ya fara min bayani akan irin rayuwar da yayi, da kalar makarantun da yayi, muka koma wajensu Janan.
Muka yi sallama dashi ya juya ya tafi, ni kuma na zauna akan kujerar da nake. Ina zama naci karo da idanun Janan tana hararata. Nace "malama lafiyarki kuwa?".
Chapter 44 · 0% Book details