Sashe 66
A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na sake yin banza na kyaleshi. Bai san tunda na baro su shi da Raheemah a falon nan ba wani haushin shi ya cika ni ba taf? Ji nake kamar in koma in janyeta daga kusa dashi, in jefata dakinta in kulle don ma kada tayi tunanin sake fita ta koma wajenshi, haka nan dai na danne zuciyata na dawo daki.
Yanzu kuwa da nake ganinshi a gabana, tunanin wajenta fa zai koma ba wajena zai dawo ba, naji wani irin matsanancin kishi ya rufe min idanu, kishi irin wanda ban taba jin shi ba.
Ya shafo gefen fuskata daga bayan kunnena zuwa kan lebuna na, cikin nuna damuwa yace "wani abu yana damunki ne? Ko baki jin dadi ne?".
Wani haushin shi ya kara tuko ni, to ko ina ruwanshi ma da wata rashin lafiyata? Koma dai menene, daga karshe dai tafiya zai yi wajen matar shi ya kyaleni anan.
Nace "wai ina ka baro matarka ne ka taho nan? Ta ma san kana nan kuwa?".
Ya daga gira cikin alamun mamaki, kafin wani murmushi ya subuce mishi, ya zauna sosai a gefen gadon.
"a'ah, bata sani ba, na taho yiwa baby na kuma amaryata sai da safe ne. Ko kuwa nayi laifi ne?".
Nace "to ni sani zan yi? Sai ka bari sai ka tambayeta, sai kaji ko?".
Yace "haka ne, bari inje in tambayeta inji kuwa".
Bai jira ya sake cewa komi ba, ya duko ya bani peck a kumatuna, ya mike tsaye yana kallona cikin murmushi, "sai da safe baby na, kiyi barci mai dadi".
Bai jira na amsa ba, ya juya ya fita daga dakin bayan ya kashe min wutar dakin. Na sauke ajiyar zuciya a hankali bayan fitar tashi, ina ji wani irin abu yana mintsinin can kasan zuciyata. Daga karshe dai nayi addu'ar kwanciya barci, na shafe jikina.
Cikin yan kwanakin nan shida, ba karamin sabo nayi da kwanciya a jikin Yaya ba, ban san nayi sabo da jikinshi sosai ba sai da barci ya nemi ya gagareni. Na dinga juyi ina karawa akan gadon, Allah kadai yasan iyaka tsawon lokacin dana dauka, kafin da kyar barci yayi awon gaban dani.
o
Kamar yadda ya saba a Zaria, da asuba ya leko ya tasheni inyi sallah, shi kuma ya tafi masallaci.
Bayan na gama sallar barci na sake komawa. Bani na tashi ba sai daya leko kafin ya tafi wajen aiki, lokacin karfe tara saura. Bayan munyi sallama dashi, na bishi da addu'ar Allah ya kiyaye hanya, na tashi na shiga bandaki nayi wanka. Na fito na shirya cikin riga da siket na paper lace. Dinkin ya matukar karbata kamar yadda ya bi jikina ya zauna sosai kamar second skin. Ni kaina nasan cewa ba karamin gogewa jikina da fatar jikina suka yi cikin dan lokacin wannan ba.
Na fita zuwa falo, babu kowa sai kuloli da flask ajiye akan dinning table. Naje na fara dagawa, indomie ce zallarta da ruwan shayi a cikin flask. Na girgiza kaina cike da tsananin mamaki, Allah dai yasa ba abinda Yaya yaci kafin ya fita ba kenan.
Dama can indomie ban maida ta abinci ba, na maida kular na rufe, na wuce kicin na lalubo gwangwanin oats na fara damawa.
Ina tsaye ina jiran ya dahu, Raheemah ta fado kicin din kamar an jefo ta. Ta bude firjin ta hau dube-dube, da kamar in kyaleta, na dai daure nace mata ina kwana?.
Ta wani dago ta kalleni a dage, taja tsaki ta kara tura kanta cikin firjin.
Abin ya bani haushi ba kadan ba, nace "maida wukar mana baiwar Allah! Sai kace na roke ki wani abu?".
Daga gani dama a wuya take, kiris take jira, ta kalleni, "to na roke ki gaisuwar ne dama? Kaji wani aikin banza ma, har ki wani daga baki ki gaida ni? To an ki a amsa din, ko kina da abinda zaki yi ne?".
Ni da tsabar mamakinta ya kawo ni wuya ma, kasa maida mata martani nayi, ita kuwa tayi tsamnanin ko tsoro ne yasa na kasa magana ko kuwa wani abu? Ta ciro lemun exotic ta maida firjin din ta rufe garam! Tace "ya dai fi miki kiyi shiru din don baki da karfin gwabzawa dani. Masu kwacen miji kawai, idan ma don kinga Haleemo ta kwacen miki miji ne kika yi haka, to ita build taci, kuma nan da watanni biyu zamu je mu sha bikinta mu rakashe, ehe! Ke kuma sai mun ga takamar kwacen miji, zamu ga abinda hakan zai tsinana miki. Da kanki zaki nemi takardar ki wallahi, ko kuma ki kare a haka!". Ta fita daga kicin din fuu!! kamar guguwa.
Na bita da kallo cike da tsananin mamaki, me hakan yake nufi ne? Kuma ma daga maganar arziki sai ta koma ta tsiya, akan me? Naja tsaki lokacin da naga har oats din dana dora ya dahu ya dafe. Na sake jan tsaki lokacin dana zubar dashi na sake dora wani. Cikin tsananin tunane-tunane da saka da warwara na gama hada oats din, na juye a cikin mug na cicciba na wuce dakina.
Bayan na karya, na dauko wayata na kira su Fatsu muka gaisa, mun jima muna hira da ita, tana ta mij nasiha da nuna min muhimmancin hakuri, daga karshe ta ba Malam shima muka gaisa. Shi addu'o'i ya bani wadanda zan dinga yi safe da yamma na neman kariya, kafin shima ya dora da nashi waazin da nasiha, daga karshe dai muka yi sallama.
Ina kashe wayar na kira Sailu itama muka gaisa. Ranar dai wuni nayi kiran wayar yan uwa da abokan arziki. Bayan na gama kuma na dauko textbooks ina dubawa da yin bita, nan da sati biyu zan fara yin internship dina.
☆
Yau ma kamar jiya, sai da Yaya ya leko ya min sai da safe kafin mu kwanta.
Washegari na karbi girki, da safe zamu dinga karbar girkin bayan wadda zata fita tayi karin safe. Yaya yana fita na dauki makullin dakinshi daya ba kowaccenmu, na shiga na gyara mishi dakin tsaf. Na yaye zanin gadon dake kai na shimfida wani, shi kuma na hada shi da kananan kayanshi na wanke su tas, bayan sun bushe na goge.
Bayan na gama turare dakin da turaren wuta, na dauko kofi na tofa wasu muhimman addu'o'i da Malam ya koya min jiya, nabi lungu da sako da kowace kusurwa ta dakin na yarfa wannan ruwa. Sauran ruwan kuma nayi girkin abincin dare dashi. Kai hatta da ruwan da Yaya zai sha sai dana tofe shi da addu'a.
Sai dana tabbatar da komi ya hadu lafiya lau, lokacin har Yaya ya dawo daga wajen aiki, sannan na fada bandaki na tsalo wanka.
*☆⋆39⋆☆*
Satinmu uku da dawowa Abuja, na riga na saba da yanayin garin, gidana, mijina, da abokiyar zama na.
Tuni na riga na fara zuwa aikin internship dina, daga aikin safe sai na rana nake yi, bana yin na dare. Har yau dai babu bayanin uwargida Ameerah. Bata dawo ba, Yaya kuwa bai taba tado maganar game da ita ba, nima dai ban taba tada mishi zancen ba. Don haka muka cigaba da raba girkinmu a tsakaninmu ni da Raheemah, wadda har yau bata sake zaki ba, kamar ma kullum kara rura mata wutar masifa da neman magana ake yi kullum.
Kullum a shirye take da fada, kiris take jira taga gilmawata a tsakiyar gidannan, zaka ji ruwan habaici da bakaken maganganu ya fara tashi, malka-malka kuwa. Ban taba tanka mata ba, kai ban ma taba nuna mata na kula da abinda take yi ba. Illa iyaka idan na fito mun hadu da ita a falo, in mata sannu, ta amsa ko kada ta amsa, ni dai na fita hakkinta.
To sai ma ranar girkina ne muka cika haduwa, ranar da take yin girki wuni nake yi a daki abuna. Babu ruwana da ita, in wuni ina shan fruits da kayan makulashe, sai da dare idan Yaya ya dawo daga wajen aiki nake fita mu ci abincin dare, duk da dai shima ba kullum ba, don abincin matar nan is terrible Sam bata iya girkin azo a gani ba. Abinda zata iya dafa maka ya dahu, indomie ce, sai kuwa spaghetti ranar da sa'ar ta ta kai sa'a.
Don haka bata da damar gasa min magana a gaban Yaya, duk da cewa ta dauko hakan, sai da Yaya ya tsawatar mata sannan.
Da ta tsiro da maganar kin cin abincina, sai dai ta shiga kicin ta girka kayanta, a raina ni kam nace mata umma ta gaida assha. Sai da Yaya ya fatattaketa sosai, nan ma ta hau cewa wai ya daure min gindi, yana sawa ina raina mata wayau. Yace wani irin rainin wayau? Yace shi fa ya kula da take-takenta na rashin son sasanci da zaman lafiya, yace kuma ta kiyayi kanta don ba zai lamunci hakan ba. Abinci ne, ya hana wata ta girka nata daban, idan wata ta girka dayar taga bai mata ba, ta bar mata kayanta taje can ta karata ita kuma da yunwa. Da wannna aka tashi dai baram-baram.
Sai kuma lokacin dana fara zuwa wajen aiki. Ranar farko da zan je Yaya ne yayi jigilar kai ni da kanshi, washegari kuma direban gidan ya kaini, zai kuma cigaba da kaini da daukoni daga ranar. Ina daki sai jiyo tashin muryoyi na dinga yi, rigima suka yi sosai akan ya bada mota ana jigilar kaini wajen aiki.
Yace "kina nufin in barta tana kai da kawowa a cikin motocin haya ne, bayan ina da ikon da zan ajiye motar da zata yi jigilarta ne?".
Tace "ai wannna ma salon munafurci ne da rashin adalci. Ni me yasa baka ajiye min nawa direban ba sanda ina gidanka a Zaria, ka barni ina yawo a motocin hayar? Ko kuwa don ka nuna mana an shanye ka?".