← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 95

Sashe 27

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya saki wata irin tattausar dariya data sa na kara narkewa akan katifata, jin muryarshi nake kamar ana min busar sarewa a kunne, yace "da gaske nayi zaton sai na zauna dogon bayani, shi yasa tunda gari ya waye nake ta hardar abinda zan fada miki, ki ce da ban wahalar da kaina ba?".
Na gyada kai ina dariya kamar wata sakara, "gaskiya kam, da ka kira tun da wuri".
Yace "yadda zan katse miki barci? Yanzu ma naji kamar daga barci kika tashi, sorry, na katse miki barci. Na kasa daurewa ne wallahi. Ina fata banyi laifin komi ba?".

Na girgiza kai kamar yana kallona, "ko kadan baka yi laifi ba, zan ma iya cewa kayi daidai!".
Ina jin ajiyar zuciyar daya sauke, "good. Don ba zan so ace daga wayar farko ba na fara yin laifi ba gaskiya". Duk muka yi dariya.
Daga nan duk muka yi shiru, baka jin sautin komi sai karar dake fita daga cikin wayar kawai. Zuwa can yayi gyaran murya, yace "to Malama Na'ilah, kamar yadda nasan cewa kin san dalilin da yasa na tunkareki tun farko har ya kawo ga wayar da muke yi yanzu, magana ce ta so. Wadda nake so, kuma nake fatan idan Allah ya yarda ya amince, zata kaimu ga aure na sunnah. Magana ta gaskiya ban fito da wasa ba, kuma nayi niyar dana bayyana a gareki, muka samu fahimtar juna ni da ke, ba zanyi sanya ba zan fara zancen aurenmu, in samu in killace ki a dakina kafin kwado ya min kafa, me kika ce?".

Daga jin sautin muryarshi da yadda yake fitar da haruffa daya bayan daya, kasan cewa kaji mutum wanda yasan ciwon kanshi, wanda yasan me yake yi, ya kuma san yadda duniya take ci. Naji ya kara shiga raina. Nan nayi mishi bayanin cewa yanzu dai karatu nake yi, sannan kuma akwai wanda muke tare dashi a halin yanzu dai, ban boye mishi komi ba, na fada mishi komi da komi. Shi kuma ya burgeni daya saurareni tunda na fara magana har na gama bai katse ni ba. Hakan ya kara min wata martabar shi a cikin idanuna.

Sai dana gama, ya nisa yace "naji dadi kwarai da baki boye min komi ba game dake, sannan maganar karatu a wajena ba matsala bace, koda ace baki fara ba, zan iya daukar nauyinki har ki gama, balle kuma duka-duka Allah na tuba menene ya rage a cikin karatun naku yanzu? Sauran kadan ne. Zancen wanda kuke tare kuma, wannan ai lokaci ne zai nuna mana ko ke din ta wacece. Illa iyaka, mutum ya zage damtse, ya shiga filin dagar neman ki sai aga wanda yake da nasara!".
Nayi dariya sosai da maganganunshi, da alamu Allah ya hore mishi iya sarrafa maganganu matuka. Shima ya biye min muka yi ta kyakyatawa kamar wasu kananun yara. Sai dana nutsa sannan nace mishi, "to Allah dai yayi mana zabin mafi alkhairi".
Ina dire aya ya cafe da; "in shaa Allahu ma kece alkhairin", ko yawu bai bari na gama hadiyawa ba.
Nace "to Allah ya yarda".
Yace "ameen... Tunda yanzu mun yi wannan magana, ina fata mun fahimci juna ni dake? Kina da wata tambaya da kike son yi game dani?".
Nace "na fahimci komi, tambaya kuma bana tunanin a yanzu akwai ta, amma idan ina da ita nan gaba, zan yi maka".

Yace "zaki iya yi a koda yaushe, tunda yanzu na ji muryarki, ina tabbatar miki da cewa sai kin gaji da ganin kira na a wayarki, don zan so ace kullum cikin sauararen muryarki nake!".
A zuci so nayi in ce, "ai nima hakan take", amma a fili sai nayi dan murmushi kawai.

Yace "yanzu dai bari in barki ki karya, nasan baki karya ba kika fara waya da ni. Bayan kin gama cin abincin zan kira ki mu dora daga inda muka tsaya, ki huta lafiya Baby na!". Daga haka ya tafi.

Na bi wayar da kallo kamar shine a gabana, ina nanata kalmar 'baby na!' a cikin kaina kamar wata bakuwar kalma da ban taba jin kamarta ba sai yanzu. Gabadaya sai naji cikina ya cika, bana marmarin komi. Don haka na koma kan katifa na kwanta ina kara maimaita hirarmu da Malam Muhammad M.B a cikin zuciyata kamar wani shirin film da yake matukar kayatar dani, ina zabga murmushi kamar wadda ta fara zarewa.
Amma dan saurara, wani hanzari ba gudu ba., me yasa muryarshi take min kama da wani wanda na sani? Ban tabbatar ko waye ba, amma naji kamar na taba jin muryar nan, inda na taba ji dinne na kasa tunawa.

Ban san iya lokacin dana dauka a cikin wannan hali ba na tsananin bege, sai dana ji an daka min duka a cinya. Nayi firgigit! Na mike zaune ina sosa wajen. Esther dake gefen katifata a zaune dangargar ta kalleni tana murmushi, "Babe, tunanin meye kike yi ne haka? Hala oganki ne?. Ta fada cikin harshen turanci kamar yadda ta saba magana dashi.

Nace mata "nothing o...".
Tace "na lie... Kada kiyi tunanin ban ga yadda kike ta murmushi ba kina dariya lokacin dana zo fita". Na zaro ido ina kallonta, da gaske har fita tayi ta dawo ban sani ba?.
Ta kyalkyale da dariya ta dauki wata bakar leda da ban kula da ita ba, ta miko min, "dama kina ta soyewa ta ina zaki ji motsin mutane bayan kinyi nisa a duniyar da daga ke sai shi? Na tabbata za'a iya ciccibarki a lokacin baki ma sani ba!".
Harara kawai na jefa mata cikin murmushi. Na daga ledar, kamshin masa ne ya fara bugo ni tun ma kafin in ga masar. Sai a lokacin na tuna da cewa jiya da dare kafin mu kwanta na fada mata idan zata je siyan masar yau da safe ta tashe ni koda ina barci ne, don marmarin cin ta nake yi sosai.

Nayi murmushi ina kallonta, "nagode kwarai Esther, ta nawa ce kika sayo?".
Tace "ban san ko ta nawa kike bukata ba, sai na sayo ta dari biyu".
Nace "tayi, nagode fa".
Tace "babu damuwa!".
Tashi nayi na dauki purse dita na bude na bata kudinta, na kara mata godiya, sannan na sauka kasa naje nayi brush na koma dakin. Bowl na dauka karama ta plastic na juye miyar da aka daure a cikin leda, na fara cin masar.

Ina cikin ci ne na dauki waya na kira Janan, finally, abinda muke ta jira, mysterious dina dai ya kira waya. Nan muka sha ihun murnarmu da maida yadda aka yi. Wani labarin ma ai sai ta shigo ranar Monday sannan za ayi shi baki da baki.
Yinin ranar wannan gabadayanshi, Allah ne kadai yasan farincikin dana yini dashi, wata irin far'ah dana rasa dalilinta, nishadi dana rasa dalilinshi. God, I'm so whipped, totally!!.

Yini aka yi ana ruwa duk da ba mai karfi bane, amma yanzu da nake kudundune cikin bargo a dakina da dare, sanyin da ruwan saman ya haddasa da kuma kamshin ruwa da jikakkiyar kasa da yake tashi, da kuma tsananin taushin muryar Mysterious dake ratsawa ta cikin dodon kunnena a daidai wannan lokacin, sai naji babu wata damuwa a raina. Babu kowa, kuma babu komi a wannan lokacin sai ni sai shi kawai. And nothing matters!.

Tuni mun riga mun sabarwa junanmu jin muryar junanmu a kowace rana. Muryar dayanmu zamu tashi da ita, texts zasu mana rakiya duk inda zamu je a yinin ranar, haka kuma zamu ji muryar juna kafin mu kwanta da dare.
Da asuba tun ma kafin alarm dina ya buga, Muhammad zai kira ni ta waya, nan kira kawai zai yi in tashi, to idan na gama ne zamu yi wayar minti biyar zuwa goma, sai muyi sallama. In shiga wanka in shirya, in karya, in fita. Kafin in karasa ward ya turo min text mai cike da kalamai dadada da zasu sa in yini ina kallon wayata cikin murmushi, ina kara karanta shi over and over, sai in tura mishi amsa. Kafin yamma ta fadi at least zamu yi musayar messages sau uku ko fi, sannan da dare dole ne sai ya kira ni kafin in kwanta barci, watarana ma muna cikin hirar barci zai daukeni sai dai ya kashe wayar in yaji shiru.

Ni kaina nasan cewa na canza, kamar wani abu yayi snapping a jikina ne. Duk wasu makamai da katangu dana sa a jikina, daya bayan daya Muhammad ya bisu ya sassare, kamar basu taba wanzuwa ba.
Wani abu ne da bai taba faruwa dani a tarihin rayuwata, da shekaruna dai-daya har ashirin da hudu a duniya ba. Ban kuma taba zaton zai farun ba. Amma yanzu daya faru, sai nake jin ina zargi da tuhumar kaina, me yasa tun farko ban bar kaina nima naji dadin wannan abu ba? Na dinga takura kaina, ina matsawa kaina? Kodayake, komi yana da lokaci, kuma kamar yadda Janan take yawan cewa, _'idan lokacin ki kamu da so yayi, baki da yadda zaki yi, kina so ko ba kya so, zaki fada tarkon ko, kin sani ko baki sani ba!'._
To yanzun ma ina tunanin abinda ya faru kenan, lokaci na ne yayi. Na kamu da soyayya, soyayyar Muhammad mai zurfi. Zurfin da ya kai naji ina so inyi kugi da karaji, wanda duk duniya da mutanen cikinta zasu ji cewa ina cikin zazzafar kaunar mutumin da ban taba sakawa a cikin idanuna ba!.

* * *

"Kyawunta ace wannan azumi da zai zo, wani mutumin kirkin zai zo ya dauki dubu ko hamsin ce ya baka, ya hada ka da buhun masara, gero, sukari ko rabin buhu ne! Kai ai da kakar ka ta yanke sa'a!! Sai ka nemi inuwa mai ni'ima kawai ka fuske, ka yini tun safe har dare a kwance Malam, babu ruwanka!!".
Wani kwandastan mota da muka hayo daga asibitin Shika zuwa kasuwar Samaru yake cewa. Duk cikin motar aka saka dariya.
Chapter 27 · 0% Book details