← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 95

Sashe 19

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na galla mishi harara, "kai a wajenka ba komi bane, saboda shaidan ya riga ya rufe maka idanu, amma ni a wajena it's a big deal. Kada ka manta, mun taba yin wannan maganar da kai, na fada maka idan kasan wani abu kake bukata daga wajena yafi mana sauki mu yanke alakarmu, don babu abinda zan iya maka. Ba zaka taba taking advantage dina ba Umar, ba zaka taba yin amfani da kayan banza ka yaudare ni ba wallahi, in Allah ya yarda nafi karfin haka. Don haka ka bude min kofa in fita tun muna shaidar juna ni da kai wallahi. Kuma ga wayar ka nan, bana so, kai bana so in kara ganinka ma!!".

Na hau kici-kicin bude kofa da sauri kamar wadda ta fita daga cikin hayyacinta. Ina ji yana kiran sunana amma nayi banza dashi. Ban tantance ba naji saukar hannunshi yana dafe min hannu, banyi wata-wata ba na wancakalar da hannun nashi can gefe. Bai daddara ba dai ya sake dafa kafadata, wannan karon dana kama hannunshi, twisting nayi da karfina duk da nasan ba lallai yaji zafin hakan ba, duba da yanayin aikinshi.
Cikin tsananin bacin rai da tunda muke dashi bai taba ganin kwatankwacinsa ba, daga murya da tsawa nace "kada ka sake taba ni!! Kada ka sake kuskuren taba ni!! Kuma wallahi ka cuce ni da kayi tunanin zaka iya saya na da kyale-kyalin banza, in shaa Allahu sai Allah ya saka min. Ka bude min kofa nace!!".
Tsananin ihun da nayi ni kaina ya bani mamaki balle shi. Ina jin hakan ne yasa bai ma san lokacin da hannunshi ya danna madannar ba, ina jin na taba murfin ya bude, na fita daga motar da sauri. Ko sakan biyu ba ayi ba naji shima ya fito, ya hau auna min kira. Babu ko waiwaye, na shige gida da sauri.

Jikina rawa yake, hannu, kafa, baki, kai, komi nawa rawa yake yi. A daidai parking space dinsu na tsaya, na dafa wani pole ina haki kamar wadda tasha tseren rai da rayuwa. Kodayake kusan hakan ne.
Tunanina daya a lokacin, da ace yaki bude kofar fa? Me zai faru da yaki bude kofar? Me zai faru idan bai daina taba ni ba? Me zai faru idan wajen da muke babu mutanen da zasu ji ihuna idan ina ihun neman taimako? Tambayoyin suka yiwa zuciyata yawa. Ban san lokacin da gwiwoyina suka saki ba, na zube akan gwiwata a wajen. Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a wajen, ban ma san a wani hali nake ciki ba. Kai ban ma san ina hawaye ba sai da naji lema da alamun gishirin hawaye akan lebena sannan na ankara. Sai kuma vibrating din da wayata take tayi babu kakkautawa. Na daga na ga sunan Umar yana rawa a jiki, tsaki na ja nayi declining, yana katsewa wani kiran ya sake shigowa. Wayar na dauka gabadayanta na kashe.

Na mike na kakkabe jikina tare da share hawayena. Sai dana tabbatar da na dawo cikin nutsuwata sannan na wuce cikin gida. Su duka suna falon suna kallo banda Janan, na musu sannu na wuce ba tare dana jira naji sun amsa min ko basu amsa ba.

Janan tana tsaye a tsakiyar daki da waya a kunnenta, ina shiga ta sauke wayar, "yanzu fa nake kiran wayarki, sai kuma naji ta kashe".
Na kalli wayar kafin na kalleta, "kashe ta nayi".
Ina tunanin bata kula da yanayin da nake ciki ba sai a lokacin, da sauri ta matso wajena, fuskarta dauke da alamun damuwa, "lafiyarki lau? Me ya faru??".
Na girgiza mata kai, "babu komi fa!".
Ban jira amsarta ba na yaye gyalena na rataye na shige bandaki. Alwala na dauro na fito.

Janan ta bini da kallo har na shimfida abin sallah, bata ce komi ba. Har na gama shafa'i da wutiri, na fara shirin saka kayan barci. Tasan ko ta dameni ma babu abinda zan iya gaya mata, sai ma karin bacin rai da hakan zai haifar min, don haka taja bakinta tayi shiru, tasan duk lokacin dana sauka don kaina, zan fada mata. Babu boye-boye a tsakanina da ita.
Instead sai tace "idan kin gama kafin mu kwanta, ki zo in danyi briefing dinki akan abubuwan da muka yi wannan satin".
Kai kawai na iya gyada mata. Dana gama shiryawan, naje gefenta na zauna, ta dauko littafinta ta bude ta fara min bayani.
Zuwa lokacin da muka gama, na dan fara saukowa daga fushin, haka ma zafin zuciyata ya dan lafa, amma duk da haka abin yana makale a cikin raina.
Kai har lokacin dana kai ga kwantar da jikina akan katifar Janan da niyar inyi barci, abin yana makale a cikin raina. Nasan cewa shi da fita har abada.

*☆⋆08⋆☆*

Da azumi muka tashi washegari, bayan munyi sahur, wanda ni ruwa kawai na iya sha, muka yi nafiloli har aka kira sallah, muka yi.
Janan ta tashi zata fita bayan gari ya fara yin haske kadan, lokacin na gama azkar dina kenan. Na dubeta cike da alamun tambaya, tace "breakfast zan je in hada, kiyi wanka kafin in fito".
A zato na ko haka dokar gidan take, don haka naga bai kamata in barsu suyi aikin su kadai ba. Na tashi na saka karamar hijabi akan kayan barcina, duk da ba masu fitar da jiki bane, kuma Janan tace Yaya a gidan Anty Ameerah ya kwana, still ba zan dauki chances ba. Sai dai ina zuwa kitchen din nayi turus, ganin Janan ita kadai a tsakiyar madaidaicin kicin dinsu tana kokarin dora tukunya akan gas. Na shiga ina karewa kicin din kallo, "ina sauran?".

Da sauri ta juyo ta kalli inda nake, ina tunanin bata tsammaneni a wajen ba shi yasa taji abin unexpected, "su wa fa?". Ta tambaya lokacin da take kokarin zuba mai a cikin tukunyar.
Na kada idanuwa, "ina nufin sauran wadanda kuke zaune a gidan dasu, ba zasu fito kuyi aikin tare bane?".
Ta danyi murmushi cikin girgiza kai, "ni kadai nake aikin dama can!".

Na zaro ido, "say what??!". Ta kwashe da dariya, na harareta, "wannan ba abin dariya bane Jan, this is serious! Ta ya za ace gardawan banza suna kwance sun saki baki da hanci suna barci, ke kuma zaki dage ki girka musu abinci? Wow! Ko da kike cewa suna sakar miki aikin gida, ban yi zaton har da wannan ba ai".
Tayi yar dariyarta a sanyaye, "ni ban ga abin daga jijiyar wuya a cikin wannan lamari ba. Na riga na saba ne, har ya zame min jiki wallahi. Sannan yawanci kafin Yaya ya wuce Abuja yana biyowa ta nan yayi karin safe, shi yasa nake tashi in hada, sai kuma abin ya zame min jiki."

Duk bayanan da take yi sai lokacin ta dago ta kalleni, ganin yadda nake kallonta kamar wata tababbiya yasa ta sake sakin wata dariyar, "da gaske ba wani abu bane, ni wallahi ban damu ba. Besides, su suke yin abincinsu da rana, wanda sai na ga dama nake ci".
Nace "ai shikenan, me zan taya ki dashi ne?".
Ta jefo min peeler, na cafe, tace "fara da dankalin can mu gani".
Na fara fereye dankalin yayin da taci gaba da soya kayan miya da tayi grating.

Cikin dan lokaci kankani na gama firar, muna yi muna hira jifa-jifa, duk da dai shiru yafi yawa. Na kunna stove tare da dora frying pan da mai a ciki, yana yin zafi na fara zuba dankalin da na yanka a tsaitsaye, bayan na zuba maggi da dan gishiri, wata dabarar soya chips da Fatsu ta koya min.

Muna gamawa ta dauko kula da flask, ta zubawa Yaya nashi da kunun gyada, fari tas dashi yana ta kamshi, ta kai falo ta ajiye.
Muna cikin maida kayayyakin da muka yi amfani dashi bayan mun wanke, muka jiyo karan bude gate. Janan ta leka ta tagar kicin din da take fuskantar gate, ta jiyo ta kalleni "Yaya ne!".
Na ajiye frying pan a inda yake na juya ina kallonta, "bari in shiga wanka kawai, bakwai ta kusa yi", kai kawai ta gyada min saboda hankalinta yana kan sauran kunun gyadar da take juyewa a cikin wani babban silver flask. Na fita daga kicin din.

Ina shiga daki na hada kayan da zan bukata na fada toilet. Bandakinta babba ne, yana da fadin shi daidai misali da kuma kayan amfani na zamani. Nayi amfani da sabulunta na 'Vix' mai kamshin sandalwood nayi wanka. Ban tsaya bata lokaci ba don nasan bamu da cikakken lokaci.
Ina gama wankan nayi amfani da karamin towel na kafe jikina. A cikin bandakin na zura doguwar rigar material ruwan kasa mai laushi, kafin na fita.

Janan tana gefen katifarta daure da towel, waya a hannu, da alamun jirana take yi. Ta daga kai ta kalleni lokacin da taji na maida kofar bandakin na rufe.
"wai fada kuka yi ne ke da Umar?".
Naji wata irin faduwar gaba lokacin da naji ta ambaci sunanshi. Tunda na tashi da safe nake ta gujewa tunaninshi a cikin raina. Na hana kaina sakat, da naji sunanshi ko fuskarshi na shirin fado min a cikin raina sai inyi saurin sako wani abun daban.
Na daka fuska ina zama akan kujerar dake gaban dressing mirror dinta, "me kika gani?".

Cike da tuhuma tace, "ban sanar dake bane kawai, amma tun jiya da dare yake kiran wayata da turo texts, sai daina dagawa nayi. Yanzu ma tun dazu yake kira, yace in baki hakuri".
Nayi kwafa kawai ban amsa mata ba, ta tashi tsaye tazo ta dafa kafadata, "ki daure ki daga kiranshi don Allah, baki san abinda yake son ya fada miki ba. Nayi zaton kun wuce matakin irin wannan fadan ke dashi?".
Na harareta ta cikin madubin, "bamu wuce ba, kuma ma in Allah ya yarda wannan shine karo na karshe da zamu yi fada dashi, we are done Jan!".
Chapter 19 · 0% Book details