← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "haka kika ce ko? To ba laifi. Dama ina bin kanki ne kawai saboda kada kice anyi miki rashin adalci ko wani abu, amma tunda ke kunnenki na kashi ne, kuma idanuwanki a rufe suke, ba kya fahimtar komi, to zan biyo miki ta hanyar da baki so. Idan ke kin iya yiwa zuciyarki rashin adalci ne, ni ba zan cuci kaina ba akan wani dalili can naki! Ina ce ba mahaifinki ne da bakinshi yace ba zaki aureni saboda ina da mata ba ko? Kuma ba Allahn daya halicce ki bane? To ki kashe kunnenki da kyau, ki saurareni kiji, maganar neman aurenki yanzu na fara ta, ba kuma zan tsaya ba sai inda karfina ya kare. Zan kuma yi duk abinda zan yi in ga cewa kin shiga gidan da kike matukar ki, don Allah ki kashe kanki ranar da aka kaiki gidana a matsayin matar aure, sai in ga karshen tsana!".

Nace "Wallahi ba zai yiwu ba, ba kuma zan yarda ba. Ni dama nasan ba sona kake yi ba kamar yadda kake ikirari, in Allah ya yarda sai Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Mugun kudirinka ba zai cika a kaina ba!".
Yace "zamu gani Na'ilah!". Daga haka ya kashe wayar.

Naji kamar in fasa ihu, jikina har rawa yake yi tsabar bacin rai. Lallai Yaya Bilal has got some nerves! Har yana da bakin da zai daga yace wai zai aureni ba da izinina ba? Har yana da wannan ikon a kaina?! To ai idan yasan wata bai san wata ba. Zan ga da abinda yake takama dashi kuwa!.

Na share hawayen da suka zubo min, na kara daukar wayata da nayi jifa da ita, na shiga cikin contacts dina. Ina ganin sunan wanda nake bukatar gani, na danna kiran ba tare da bata lokaci ba. Tayi kara daya, biyu, ana uku aka dauka.
.Cike da cheeriness da alamun tsokana da baka taba raba muryarshi da ita, yace "hello, Nas. Ya kike?".

Na dauki ajiyar numfashi na sauke a hankali, na dan kakaro murmushi duk da nasan cewa ba ganina yake yi ba, nace "hello Doctor, maganar ganin iyayena da kayi ranar nan, ka shirya yi yanzu?".

Yace "of course Na'ilah! Dama ni ai jiranki kawai nake yi. Yaushe ake bukatar gani na ne?".
Nace "idan ma a gobe ka shirya, zaka iya zuwa ka gansu".
Yace "Masha Allah, that's good. How about in zo anjima sai mu sake tattaunawa akan yadda za ayi?".
Na dan jinjina kai sama, "yeah, hakan ma yayi. Sai ka zo kenan?". Yace "in shaa Allah. Gani nan zuwa".
Nace "sai kazo!". Na ajiye kan wayar.

*

Kwana uku bayan haka, Janan ta shigo asibiti tun da safe ranar alhamis. Abin ya bani mamaki. A bakin hostel muka ci karo da ita, ni zan fita ita kuma zata shiga. Na kalleta cike da mamaki, nace "lafiya kuwa? Mai ya shigo dake nan da wuri ne?".

Bata tsaya amsawa ko yi min bayani ba, taja hannuna muka koma daga ciki, can gefe, tace "abinda kika yi kina ganin shine daidai a wajenki?".
Nace "me nayi?".
Tace "Yaya Mudatthir ya kira ni dazu tun da sassafe".

Sai lokacin na fahimci dalilin shigowarta din da kuma tambayoyinta. Nima bamu jima da yin wayar dashi ba.
A yadda muka yi da Dr. Na Abba lokacin da yazo ranar litinin, mun tsaya akan cewa zai je Gashua ya samu su Malam su akan maganar mu. A washegari talata na kira su Fatsu na sanar dasu bakin da zasu yi, zai je ne kawai suyi magana, a san dashi, sannan a tsaida ranar da yakamata magabatanshi su je. Su Malam suka yi farinciki matuka, har Fatsu tana cewa har ta cire rai da zaton zata ga wannan rana, ni dai kawai uhmm nace mata.

A daren ranar jiya bayan Dr. ya kira ni ya sanar dani cewa sun dauki hanyar Kano daga Gashua, Yaya ya kira ni. Tambayata kawai ya hau yi akan wai na tabbatar da cewa wanda na turo mishi na amince dashi? Nace ta yaya zan tura wanda naji ban aminta dashi ba wajen iyayena?. Yaya yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, kafin yace "amma kuma Baba yace wani yaje wajenshi a jiya din, shima duk akan maganar ki ne!".
Naji an fara min wani luguden daka a kirji, ashe dai Yaya Bilal da gaske yake ba da wasa ba. Amma a zahiri sai na dake, nace "ni fa bansan ko wanene ba, don ni babu wani wanda muka yi magana dashi akan zai zo bayan Dr. Na Abba".
Yaya yace "to ai shikenan".
Daga nan muka dan yi hira, na tambayeshi jikin Sailu da har yanzu tana asibiti. Yace dukansu lafiya lau. Sannan muka yi sallama.

To yau kuma da safe sai ya sake kirana, yana tambayar wai dama wanda yaje wajen Baba Yayan Janan ne? Nace "ni fa Yaya na fada maka ban san kowanene ba".
Yace "kada ki raina min wayo mana Na'ilah. Ni nasan yadda kika sako karatun nan naki a gaba, maganar aure yanzu bata cikin kanki. Tunda naji dama wai kin turo wani gida kai tsaye, nasan da wata a kasa. Don haka ki fada min abinda yake faruwa".
Nace "to ni Yaya sai dai kuma in karya kake so in maka, amma babu abinda yake faruwa. Kawai na samu wanda hankalina ya kwanta dashi ne, dama can don dai ban samu wanda ya shiryawa auren bane".
Yace "ina wannan yaron da kuke tare dashi kuma fa, sojan nan?". Nace "ni tun yaushe da muka rabu dashi?".

Yaya Mudatthir yace "shikenan Na'ilah, ni dai ina shawartarki da ki bi koma menene a hankali!". Bai jira abinda zan ce mishi ba ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo cikin yamutsa fuska, me yasa ne yake wani magana yana bani a linke? Sai ban saka maganar a kaina ba, naci gaba da shiryawa ta.

To kuma gashi ina fita naci karo da Janan, itama tana bani tata linkakkiyar maganar.

Nace mata "eh, ina ganin shine mafi a'ala a wajena Janan. Ina ganin kuma hankalina zai fi kwanciya a hakan".
Tace "ki dai bi a hankali, kada kije ganin neman gira ki rasa idanu. Ki gujewa garwashi ki fada cikin wuta!".

Na dan jefa mata harara, "ni fa saboda wutar da Yayanki ya hada min yan kwanakin nan, kwalwata bata gane maganganu masu baki biyu. Don haka ki daina bani a dunkule kawai ki fito ki min magana kai tsaye don bana fahimtarki".

Itama ta harareni, tace "shi wanda kike likewa din, kina da tabbacin zai rike ki kamar yadda kike hange ne? Kin kuwa san waye Dr. Na Abba? Shekarunshi talatin da biyar, aurenshi bakwai Na'ilah! Aure bakwai! Amma yanzu bashi tare da mata ko guda daya sai 'ya'ya kashi-kashi dake gaban mahaifiyarshi wadanda matanshi suke ajiyewa idan suka rabu. Kin san me yake hada shi da matan har su rabu? Kika sani ko yana da wasu halaye da basu dace bane shi yasa? Kina da tabbacin ke idan kika aure shi a hakan, zaki zauna a gidanshi ne? Wallahi ina jiye miki yin dana sani Na'ilah".

Nace "na farko ba ni na like mishi ba, idan da wanda ya likewa wani a cikinmu to shine. Sannan nasan da labarin hakan ai, kawai mutane ne da basu rabuwa da tashin zaune-tsaye. Kika sani ko matan nashi ne masu halaye marasa kyau? Idan ma ba hakan bane, wai meye ruwan mutane ne da rayuwarshi iye?".

Janan ta daga baki cike da mamakina, tace "wai lafiyarki lau kuwa? Kin ma san abinda kike fada ne? Auren mutumin wannan da zaki yi sunan shi gudun gara, kin guji auren mai mata kin fada gidan mai 'ya'ya. Yo ba gwara auren mai matar da kika sani ba sau dubu akan wanda baki sani ba? Kodayake, rayuwarki ce ai. Kiyi duk yadda kike so da ita. Daga yau na daina yi miki magana game da Yaya Bilal in Allah ya yarda. Kiyi duk abinda kike ganin shine daidai a wajenki, jiki magayi!".

Ta juya ta wuce abinta, ni kuma na bita da kallo na wasu lokuta, kafin na bi bayanta da sauri ina kwala mata kira.

Da yamma Yaya Mudatthir ya kirani, Anty Sailu ta haifo yaranta maza biyu.

🙏🙏🙏🙏

*☆⋆29⋆☆*

"Yanzu yaushe kike tunanin zamu tafi wajen sunan ne? Ina ganin kamar mu tafi Talata ko? Ya kike gani?".
Janan take tambayata a washegarin ranar da aka yi haka, bayan mun dawo daga masallaci.

Nace "zaki je ne?".
Ta dan yamutsa fuska cikin nuna alamun rashin jin dadi, "ban gane ba? Kina tunanin ba zan je bane ko me?".
Nace "kinga, ni fa ba cewa nayi ki hayayyako min bane. Nasan Yayanki da protectiveness dinshi, ban sani ko zai barki kije bane, shi yasa".

"Wannan kuma matsalar mu ce ni dashi, don't you think? Kawai ki fada min lokacin da kike ganin yakamata mu tafi!". Ta fada a dan zafafe, har sai dana kara kallonta cikin mamaki.

Naja tunga na juya ina kallonta tare da kama kugu, nace "ni fa na kasa gane miki ne, tun da kika zo yau kike hade min girar sama data kasa. Na miki wani abu ne?". Duk yadda naso inyi masking damuwar data lullubeni, na kasa. Janan ita ce mutum daya kacal da duk duniya nake ganinta kamar jinina, kai wasu lokutan ma fiye da jinina. Ita ce kuma kadai nake ganin duk duniya, babu abinda ba zan iya sadaukar mata ba. Sai dai banyi tunanin sadaukarwa zata zo da consequences kamar wannan ba, wannan shine abu dayan da ba zan taba iya sadaukarwa ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin cewa ban biye mata mun raba kai a tsakiyar titi ba, nasan cewa zuciyarta cike take da haushina dankar. Amma na fara kaiwa bango.

Tayi ajiyar zuciya, kanta yayi kasa cike da nuna nadama, "am sorry... Kawai na kasa wrapping kaina akan abubuwan da kike yi ne. Kin san cewa na damu dake, bana so ki aikata abinda zai zo ya zame miki dana sani daga baya wallahi. Why not Yaya Bilal kam? Kinga bayan mun bar nan, babu ruwanmu da tunanin rabuwa, zamu sake zama tif da taya, mu zama yan uwa na hakika".
Chapter 50 · 0% Book details