← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 95

Sashe 55

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Napep din da muka hayo daga bakina titi yayi parking a kofar gidan, muka biya shi, sannan muka fita daga ciki.
Na daga kai na kalli gidan da kallo, yan kadan daga cikin memories dana tara a gidan, suka dinga flooding suna shiga cikin kwakwalwata. Na girgiza kai a hankali, ina kokarin shaking din komi daga cikin kaina.

Ni da Janan muka shiga gidan, bayan mun gaisa da maigadin gidan. Kai tsaye dakin Anty Sarah muka wuce. Da yake yamma ce, babu cunkuson mutane sosai. Muka gaisa na mata barka, ta amsa tare da min godiya. Yanayin yadda take fara'a da tambayata bayan rabuwa, sai kayi tunanin irin mun saba sosai dinnan ne.
Aka miko min diya na amsa, kamar yadda Janan tace, kamar su daya da Mimah babu banbanci. Na kura mata idanu ina kallo kamar in sude ta saboda birgewa. Yadda ta nade cikin towel din da aka nadeta a ciki, kamar irin magen nan sabin haihuwa, very adorable.

Mun jima sosai dasu ana yar hira, ba karamin mamakinta ta nuna ba akan maganar aurena da taji ba. Musamman ma da wani, ba... Bata karasa ba, naji Janan tayi saurin ta katse mata maganar. Na bisu da kallon mamaki, ban tsaya tambayarta wa take nufi ba, duk nayi zaton da Umar take, don haka na share maganar don nima bana son tuni akan irin rayuwarmu da Umar, da irin cin amanar da yayi min.

Ina shirin tashi da niyar yi musu sallama in tafi, kawai naji tashin sautin muryar data matukar rikitar dani. Da sauri na koma cikin kujerar dana fara tashi dabas, wata irin rawar jiki ta ziyarce ni. Ba shiri na fara janyo salati da hailala ina ja ina karawa a cikin raina.

Yaya Bilal da Yaya Jameel suka shigo cikin falon. Yaya Jameel sanye da casual jeans and T-shirt, yayin da kamar kodayaushe, Yaya Bilal yake sanye da shadda ruwan sararin samaniya, rataye a kafadarshi ta dama, brief case dinshi ce, da alamu dawowarshi kenan daga wajen aiki.

Suka samu waje suka zauna, kallon nan daya dana musu, ban sake daga kai na kallesu ba. Falon daga mu, maijegon, sai kuwa wata makociyarsu Ikilima data shigo bayan mun shigo muma.

Ina jin tashin muryarsu suna gaisawa da mutanen falon, nasan nima dole ne in gaida su.
Na daga baki da kyar na gaida su, ba tare dana iya daga kai na kallesu ba. Tashin muryar Yaya Jameel kadai naji ya amsa, hakan yasa naji jikina ya kara yin sanyi.

Ko lokacin da Janan ta karbi diyar daga hannuna da niyar mika musu, ban iya daga kaina ba.

Na yan wasu lokuta, dakin ya dauki shiru, babu motsin abinda kake ji, sai tashin muryar Yaya Bilal kawai da kake ji yana tashi, yana yiwa jaririyar addu'o'in tsari da kariya kala-kala.

A lokacin ne na samu na iya daga kaina a hankali, na saci kallon inda Yaya Bilal din yake zaune dauke da yarinyar. Rabon da in saka shi a cikin idanuna ko kuma inji muryarshi, run rana daya tsare ni a hanya a asibiti da kuma lokacin da muka yi waya dashi ta karshe.
A yanzu da nake kallonshi, yadda ya rike yarinyar nan a hannunshi kan-kam, kamar wanda yake tsoron wani abu ya faru da ita. Tsananin soyayya da zaka gani a cikin idanunshi, tsantsar adoration da wani irin hope, hope wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunshi, ya sanya naji wani matsi a cikin zuciyata har sai da naji kwalla ta cika min idanu. Ba zan iya jurar wannan abu ba, na zabura na tashi tsaye da sauri, har wayata da take kan cinyata ta fadi. Nayi sauri na wawureta tare da sungumar jakata na rataya, na kalli Janan da Anty Sarah da suka bini da kallo cike da mamaki.
Nace "zan tafi ne, Anty Allah ya raya baby, Janan, sai mun hadu ko?". Anty ta amsa da ameen, Janan kuma ta matso kusa dani da niyar taka min zuwa waje.

Ina tunanin sai lokacin Yaya Jameel ya kula da nice a cikin falon, yace "a'ah! Wai dama Na'ilah ce?".

Na daga kai a hankali ba tare dana kalli inda yake ba.

Yace "ke kuma sai kawai muji labarin aurenki daga sama babu sanarwa kamar saukar aradu?". Mutanen falom suka saki dariya da jin haka, nima sai dana dan murmusa.
Yace "da gaske fa! Da har munyi fushi ai, daga baya dai na hakura. Allah yasa ranar asabar din zamu je daurin auren wani abokinmu, tunda shi nashi da safe ne ba kamar naku na rana ba, in Allah ya yarda zamu yi kokari mu leka".
Na gyada kai a hankali, nace "Allah ya yarda". Ban tsaya jiran jin wani yace wani abu ba, na daga kafa na fita daga cikin falon da sauri Janan tana bina a baya.

Muna fita, Allah ya taimakeni naga dan adaidaita sahu, na tsayar dashi da sauri na haye. Ko tsayawa muyi sallamar kirki ni da Janan banyi ba, dan adaidaitan yaja muka tafi.

A cikin adaidaitan, na saka fuskata cikin hannuwana, ina kokarin slowing down irin gudun da zuciyata take yi. Nayi tunanin na manta da Yaya Bilal a cikin raina. Nayi zaton na binne shi a cikin raina gabadaya. Ashe I was wrong. Innalillahi, na shiga uku. A haka zanyi auren?.

Cikin wannan tashin hankalin na sauka garin Gashua washegari. Ganin su Fatsu da kuma yan biyun Sailu da suka yi wayo bul-bul abinsu, shi ya sanya gabadaya na manta da ganin Yaya Bilal da abinda hakan ya haddasa min a cikin raina.

Tunda na sauka ban huta ba, Fatsu bata bari ko rintsawa inyi cikin sauki. Ina sauka, masu gyaran jiki suka tare ni da kayansu na tsuguno da turaruka. Washegari kuma aka yi su dilka da halawa. Kwana biyun nan da nayi, ba karamin gyara na sha ba. Ni a karan kaina sai da naji canji a jikina ba na wasa ba.

Ko a ranar da zan tafi, tare muka tafi da wata mai gyaran jikin, zata cigaba da gyaran data fara har zuwa ranar da za'a kaini gidana. Daga Maiduguri tazo, diyar wata aminiyar Fatsu ce wadda suke mutunci da ita sosai.

*

Tun ana saura kwana uku biki gida ta fara cika da yan'uwa na nesa. Mutanen Gashua da yawansu sun zo, sauran kuma sun tsaya a gida da yake suma can kalar nasu bikin zasu yi.

Janan ana saura kwana biyu fara biki tazo, muka hadu dasu Kulsum da sauran abokanmu muka cigaba da planning harkar bikinmu.
Da yake akwai dakuna biyu manya spare a cikin gidan, nan aka gyarawa yan biki. Duk da haka, ranar da aka fara harkokin bikin, sai da wasu bakin suka dangana da dakin Anty Alawiyya da namu dakin. Su Hajiya Ramata kam kane-kane tayi, babu wanda yayi gigin tunkarar dakinta ma saboda yadda ta cune fuska.
Ranar bikin ma haka ta yini tana ta shiga da fita tana zubda habaici, sai dai duk cikinmu babu wanda ya tanka mata. Muka cigaba da gudanar da bikinmu.

Wani abin mamaki shine, har ranar da muka yi walima, babu wanda muka gani ya leko daga cikin dangin anguna. Shi dama ango sai ranar daurin aure muka yi dashi zai zo, kwana uku ne kadai aka dauka ana shagulgulan bikin Koda na mishi korafi, cewa yayi kada in damu, zasu zo ne. Har ranar daurin aure shiru.
Maganar tafiya ma bai sake tada min ita ba, kuma a yadda muke tunani, an daura aure ranar asabar, jirginsu zai tashi ranar Lahdi da yamma. Dana taba tambayarshi yadda za ayi, naga yana neman manna min hauka, wai me yasa na cika wutar ciki ne da gajen hakuri? Na ga an daura auren ne ya dauki kafa ya barni ne? In zuba idanu mana in ga abinda zai faru. Na bashi hakuri a lokacin, na kuma kawo idanun na zuba mishi kawai.

Ranar assabar, ranar da za'a daura aure. Karfe goma sha biyu na safiyar ranar za'a daura auren a babban masallacin juma'ah dake nan cikin unguwarmu. Da safen muna can gidansu Kulsum saboda yadda gidanmu ya cika da jama'a babu masaka tsinke.
Na lume akan katifar Inna a can uwar daka, duk da uwar kwalliyar da nasha, da kuma zufar da ake yi, hakan bai hana ni fita ko nan da falo ba. Tunda garin yau ya waye, ko in ce tun a daren jiya ma, nake jin wata irin faduwar gaba akai-akai. Zuwa yanzu gabadaya jikina yayi sanyi lakwas kamar an watsa min ruwan sanyi a jiki.
Idanuna kur akan agogon bangon dake cikin dakin makale a jikin bango. Duk wucewar dakika daya, da karuwar faduwar gabana take wucewa. Har lokacin da hannuwan agogon suka hau kan sha biyu, suna nuna karfe sha biyu ce daidai a wannan lokacin. Jikina ya hau rawa yana kadawa, shikenan, na zama danyar nama.

Karfe goma sha biyu da rabi, na jiyo muryar Malam a tsakar gida da sauran muryoyi. Ban san abinda yake faruwa ba, ban kuma yi yunkurin tashi inji mai yake faruwa din ba, na cigaba da zamana. Sai da Inna ta shigo dakin ta ganni, tace "kina nan ashe? Ai an daga auren zuwa karfe hudu na yamma".

Daga farko ajiyar zuciya naji ta ziyarce ni, kafin na kalleta a rikice, "me yasa?".
Tace "wallahi nima Malam bai fada min ba, kawai dai yace sun ce an daga".
Ina ji da yawa suna fata da addu'ar Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, a zuciyata nace ameen.
Idan haka ne, kenan yana nufin sai gobe sannan za'a tafi Zaria da ni. Tsarin dama shine idan aka daura auren yanzu, zuwa bayan azzuhur kuma sai yan kai amarya su dauki hanya. Nayi kokarin tuntubar angon nawa ta waya inji yadda ake ciki, waya bata shiga. Tun da yau tayi ban samu wayar shi ba, nayi tunanin ko network ne ya hana tunda a jiya da rana da muka yi wayar mu ta karshe dashi, yace yau da sassafe zasu taho da abokan shi.
Na sake kokarin tuntubar babban amininshi, Salisu inji ko me yake faruwa, wayar shi ta karaci kara har sau biyu bai daga ba. Daga karshe na maida wayar cikin jaka.
Chapter 55 · 0% Book details