← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 95

Sashe 33

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin sa'a kafin mu karasa gida ruwan sama ya sauka mai karfi, muka daga kafa cikin sassarfa muka kara sauri. Duk da haka kafin mu karasa gida, jikinmu ya jike sharkaf! Har digar ruwa muke yi. Da sauri muka karasa cikin falo, a dan corridor dinsu kafin a shiga falo muka tsaya domin mu dan kafe kada mu bata musu carpet din falo da lema.
Muna tsaye anan sai karan turo kofa muka ji, muka juya muna kallon Yaya daya shigo shima yana linke umbrella din daya shigo da ita. Muka zaro idanu mu duka a tsorace muna kallonshi, nayi zaton a gidan Anty Ameerah yake yau, ko kuwa ba acan yake ba? Aka fara kallon-kallo tsakaninmu dashi.
Ba Janan kadai ba, ni kaina sai da naji zuciyata tana tseren tashin hankali.

Ya hade fuska kamar yaga wasu mala'ikun daukar rai, "daga ina kuke?!". Ya tambaya murya a cune.
Janan ta fara kokarin ja da baya a tsorace, cikin in'ina ta fara cewa "um... nan.. ne baya!".
Ya daga murya, "ina ne nan bayan exactly?! Ba na hana ki fita waje da dare ba? Ban da rashin hankali kawai sai ku kama kafa ku fita daga gida da dare babu tunanin komi, kuna ganin hadari kuma! Ku duba yanda ruwa yazo ya muku duka, musamman ke da kike rashin lafiya! Karatun da kuke yi kenan dama? Idan fa jikin ki ya kara rikicewa?". Ya maido tambayar kaina. Na dan yi tsalle a tsorace, na koma bayan Janan na lafe kamar ita zata kare ni daga fadan shi.

Allah ne ya bata kwarin gwiwar iya daga baki don ni gabadaya jikina rawa yake yi, tace "kayi hakuri Yaya, abinci muka fita muka sayo".
Yace "abincin waje a gidana? An hana ku dafa abincin ne? Waye ya hana ku?!".
Janan tayi saurin girgiza kai, "babu ko daya wallahi, kawai mun ji marmarin awara ne, shine muka fita muka sayo. Bamu yi zaton ruwan zai same mu a hanya bane amma kayi hakuri...".
Ya dan sauke ajiyar zuciya alamun ya dan sauko, yace "to shikenan, amma kada ku kara". Muka hau gyada kawuna kamar wasu kadangaru.
Yace "to ku wuce kuje ku canza kaya kafin wani abin ya kama ku". Bamu jira ya sake cewa komi ba, muka bar wajen a sukwane.

Sai da muka shiga daki muka maida kofar muka rufe, sannan muka sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya, kafin muka kalli juna muka kwashe da dariya.
Bayan mun canza kayan jikinmu, mun shanya wadanda muka cire, muka cigaba da kallonmu muna cin awarar.

*

Washegari bamu tashi da wuri ba saboda mun san cewa ba asibiti zamu je ba. Da muka yi sallar asuba, Janan ta wa wata sister Mairo matron dinmu text akan cewa ba zamu samu damar shigowa ba saboda rashin lafiya, bayan ta turo mata da amsa akan babu damuwa Allah ya bamu lafiya, muka koma gefe muna dariya kafin muka koma barci. Sai wajen karfe tara na safe muka tashi. Janan ta fita kicin zata dora mana abinda zamu ci, ni kuma nayi amfani da wannan damar na shiga bandaki na watsa ruwa.

Kafin in fito ta dafo mana indomie, muka zauna muka ci ta sake daukar kayan ta fita dasu. Ta dawo ta zauna a kusa dani ina duba wasu textbooks dinta, zuwa yanzu naji na warware sosai, kamar ban taba yin wata rashin lafiya ba, amma duk da haka sai da Janan ta takura min ba sha magani.
Tace "ki zo muje ki taya ni in yiwa Yaya doughnut da cin-cin don Allah".
Nace "nayi zaton ya tafi?".
Ta girgiza kai, "sai gobe. Abin azumin da za'a fara gobe, yana can babban gida, jiya da yau yayi rabon azumi".

Na ajiye textbook din ina kallonta, "amma banda abinki Jan, saboda Allah me zai yi da doughnut da cin-cin da azumi?".
Tace "ya dinga sahur ko shan ruwa mana!".
Na fashe da dariya ina girgiza kai, "gaskiya Ummah tana da sauran aiki a gabanta wallahi, haka zaki yi aure kije ki dinga soyawa miji cin-cin da azumi?".
Ta mintsileni a gefen cinya tana dariya, "bana son iskanci wallahi, zaki taya ni ne ko yaya?".
Na mike ina laluben abinda zan sakaya jikina dashi, "kin san ni bana wuce tayin kayan zaki dangin fulawa". Muka fita daga dakin muna dariya bayan na dauki karamar hijabi data tsaya a ruwan cikina na sa.

Gidan shiru, haka falon babu kowa hatta da TV a kashe take. Na san kila sun tafi makaranta, wannan ko kuma suna daki suna barci. Muka fada kicin muka fara aikin daya kaimu.
Bamu yi minti talatin cikakke ba, muka ji an bude daki an fito. Ba'a jima ba Salama da Haleemo suka shigo kicin din cikin kayan barci, na kallesu na kauda kai cikin girgiza kai. Haka suke yawo wani lokacin a gidan cikin kaya masu bayyana jiki, a ganina duk da a gidan Yayarsu suke ai hakan bai kamata ba. Ba fa kowane mutum bane na Allah.

Haleemo ta dan dakata data ganmu a kicin din, sai kuma ta maze ta kallemu, wai "sannunku!". Muka yi banza ni da Janan muka kyaleta kamar ba damu take ba. Salama tayi dariyar mugunta tana bude firjin, tace "Allah ya kara, uwar sanabe da neman gindin zama!". Ta dauki abinda zata dauka ta fita daga kicin din ta bar Haleemo a tsaye.

Kame-kame ta fara, "uhmn, Na'ilah nace., ni fa ban san wannan gayen saurayinki bane! Shi ya fara zuwa wajena, kuma sai daya ne, na rantse da Allah...".
Na katseta ta hanyar juyawa ina watsa mata harara, nace "ni fa kinga Haleemo, idan na raina kasuwa ko sako bana badawa cikinta. Ban tambayeki alakar ki da tsohon saurayi ba ba, ko kallon banza ban miki ba, saboda baki kai matsayin da zan zauna ina cacar baki dake akan wani saurayi ba wallahi. Alfarma kika min babba da kika lallaba kika hillace shi, godiya ma yakamata in miki, don haka ki kwashi jikinki ki bar nan wajen wallahi, duk abinda mutum yayi dai ai kansa ya yiwa, walau mai kyau ko marar kyau!".

Ta saki baki tana kallona, sai kuma ta juya ta bar kicin din da sauri. Naja dan siririn tsaki.
Da yake kwabin doughnut din da muka yi babu yawa, nan da nan muka gama soya shi. Muka fara na cin-cin din, zuwa lokacin rana ta fara yi.

Ni kadai ce a kicin din lokacin da Raheemah ta fado kicin din kamar wata kububuwa, Janan ta leka waje zata samu wani yaro ta suka can bakin titi.
Na gaidata a kaikaice, hankalina yana kan fulawar da nake murzawa.

Maimakon ta amsa, sai naji ta ja dan tsaki, "uhumm, ihunka a banza kenan! Ina amfanin wadda za'a kwace saurayi a hannunta tana zaune? Hakan yana nuna aikin banza ne, kuma abu mai wahala ace za'a iya kwace miji! Don ma dai mutum yaji ya sani, idan ma saboda mijina ne ake min zarya ana min shige da fice a gida, to wallahi mijina yafi karfin haka. Nima kuma nafi karfinshi!".

Allah sarki, naji maganganunta sun bani takaici sun kuma bani dariya, na girgiza kai a hankali ina dan murmushi. Banda tsabar hauka da rashin tunani, har ta wani kalleni tace wai zanyi kwacen miji? Tsakanin ni da ita ko wa yayi kama da wanda zai yi kwace? Na sake girgiza kai.

Ta kama kugu tana wani jijjiga jika ganin ban tanka ta ba, tace "ke Baiwar Allah dake nake, aha! Ni dai na fada na sake fada miki, mijina yafi karfinki!".
Na juya na kalleta ina murmushi, "ai na fiki sanin haka, saboda haka ki kwantar da hankalinki, mijinki naki ne ke kadai, ban iya snatching ba wallahi!".
Sai ta hau wasu tsalle-tsalle cikin masifa, "dariya ma kike min kenan? Ke wallahi na ga alamun iskancin ki yawa yake yi fa! Ke har kin isa ki zauna kina min ba'a? Wacece ke, yaushe aka haifeki? Aikin banza dana wofi!! An ga mijina mai kudi an makale mishi kamar maganadisu, ana ta wani shige da fice a gida har da rashin lafiyar karya. To ta Allah ba ta mutum ba wallahi, kuma duk dan iskan da yace zai kara dani wallahi shi zai ji jiki. Haka nan za'a koma gida aci gaba da cin tuwon datsa miyar kuka tsanwa, mu dai mun fi karfin mutum!!".

Na janye robar hannuna gefe ina kallonta, raina ba karamin baci yayi da maganganunta ba, amma na danne, nasan so take take raina ya baci in biye mata. Na fuskanceta sosai, ina watsa mata wani wulakantaccen kallo, babu shiri ta shiga taitayinta. Nace "na farko, ban san abinda na miki ba da zaki zo haka kawai ki hau zagina, sai dai bari in tabbatar miki da wani abu daya, I'm not into your husband! Hakan da kike yi ya tabbatar min da cewa ko dai kema kwacen mijin kika yi, ko kuma dama can kwacen samari da mazaje a jininku yake. Kowanne ne dai wannan matsalar ku ce, don ni ban saba ba, ban iya ba, kuma ba zan yi ba. Ke gida da dukiyar miji suka dama, dama don su kika aure shi. Mijinki baya cikin yan kayana, ki godewa Allah, da ba don haka ba wallahi da sai na sa kin zubda hawaye, don haka baiwar Allah, ki shiga taitayinki. Gida ne, daga gobe idan kika kara ganina a cikinshi ki min duk abinda kika ga dama!".

Ta daga baki zata yi magana, amma ta kasa. Tayi haka yafi sau uku, kafin tayi kwafa a fusace ta juya ta bar kicin din da sauri, na ja tsaki ina furta "sakarkaru" a kasan raina. Raheemah sakara ce, daukar zugar kanne da kawaye yana nema ya jefa rayuwar aurenta cikin garari da matsala. Wani abun ban dariya da takaici shine, zasu zuga ta ta wa miji ko danginsa rashin mutunci, ta hau kai ta zauna, su kuma su koma gefe suna mata dariya da ba'a, me amfanin hakan kenan?
Chapter 33 · 0% Book details