← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 95

Sashe 94

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki naji cewa Ameerah ta samu tayi aure da kyar, bayan manema kusan shida na fitowa suna guduwa saboda zancen dalilin da yasa ta bar gidanta na farko da suke ji. Sai daya zama kamar ma kyautar da ita ma iyayen suka yi. Gidan mata uku aka kaita, itace cikon ta hudu. Ga tarin 'ya'ya. Hakan yasa ni zama wani tunani, duk wata kauna da iyayenki zasu nuna miki a matsayinki na 'ya mace, ta dan lokaci ce. Dole dai gidan aure nan ne gidanki na har abada. To ko meye amfanin shiga cikin rayuwar auren 'ya'ya da iyaye suke yi? Bayan sun san cewa, daga ranar da ka karbi sadakinta, duk wani hidima nata da komi nata ya tashi daga karkashinsu ya koma kasan wanda ka aurawa? Yakamata iyaye su bude idanunsu, su kuma kula da cewa shiga cikin rayuwar auren 'ya'yansu mata da suke yi suyi babakere, har su dinga karfafa mata gwiwa akan sabawa miji, hakan baya haifar da komi, sai zubewar darajarsu a idon yaransu da mazajensu, wanda hakan zai iya kawo rabuwar aurensu daga karshe. Kunga anyi biyu babu kenan. Tunda ba kowa bane zai iya zama ya iya jurewa a dinga yi mishi wasa da rayuwar aure.

Na sauke ajiyar zuciya a hankali ina kallonta, nace "baki kula da juyin da aka samu bane? Lokacin da za'a min kishiya nima fa haka kika zaunar dani kina min nasiha da bada shawarwari".

Ta gyada kai tana murmushi, "kwarai anyi haka. Sai dai ni ban taba zaton idan nawa lokacin yazo ba, zaki maidawa kura aniyarta ba".

Na hau karewa falonta kallo, hotunanta dana mijinta da 'ya'yansu, Abdul-Azeez kusan sa'an Muhaaseen, da dan kaninshi Sultan, sun mamaye falon. Shekaru uku da suka wuce aka wa mijinta Al-Mustapha canjin wajen aiki, suka dawo Abuja. Tun daga nan muka kara hadewa, kanmu a hade yake sosai. Musamman da wajen aikinmu ya zama daya, tare da ita muka yi masters dinmu anan wata private university. Hajara ma ta shigo cikinmu. Idan ka ganmu kamar wasu 'yan uku, babu mai cewa ita din kishiyata ce.
Kulsum ma ta auri wani dan kasuwar kayan masarufi, tana Kaduna abinta da danta Suleiman.

Nace "rayuwar kenan, haka take zuwar ma mutum a bai-bai, cike da ban mamaki da tu'ajjibi". Ta gyada kai.

Nace "to yanzu ya ake ciki ne?".
Tace "ni fa dama can ban hana shi yin auren shi ba, ce mishi nayi Allah ya sanya albarka. Kawai ina ta tunanin ta inda na gaza ne da har zai yi tunanin kinkimo min kishiya ya kawo min. Naga dai babu abinda na rage shi dashi. Gyaran jikin nan duk karshen wata yin sa nake, watarana ma kafin karshen watan yayi nayi. Ke karewa ma, VIP ce ni a Tee-Tee's Care. Ki duba fa yadda fatar jikina take taushi da laushi da komi!". Ta karasa fada tana nuna min hannunta.

Na matsa gefe guda ina harararta cikin dariya, "dalla can matsa Malama. Wai ke an fada miki wadannan abubuwan suna hana maza karo aure ne idan suka yi niyya? Kawai dai nasan suna kara miki wata daraja a idanunsu musamman idan ita wadda aka kawo miki din bata san sirrin gyaran nan ba".
Ta gyada kai.
Hakan ta tuno min, lokacin da Hajara ta haifi Suhaima, sai data kusa yin yaji saboda yadda Yaya ya dinga mata. A cewarta, ce mata yayi gabadaya ta canza, yace ta same ni in gaya mata yadda ake gyaran jiki idan aka haihu. Wanda hakan shi ya bata mata rai. Ni kaina naji na tausaya mata, sai dana sameshi kuma na fada mishi hakan babu dadi, kuma bai dace ba.
Saboda tsananin gyaran dana samu lokacin dana haifi Muhaaseen, sai da Yaya yayi min kyauta mai girma. Su Anty Haleemah kuwa da su Fatsu sun sha godiya tafi cikin daro.
Sai dana zaunar da ita na fahimtar da ita muhimmancin irin abubuwan nan, duk da hakan ma dai tana dan yi ne kawai. Su ainihin yan boko ne, irin wadannan abubuwan babu su a cikin dictionary dinsu. Lokacin data fada min haka, ba karamar dariya na sheka mata ba. Kitso da kunshi ma, musamman ma dai kunshin, sai idan zamu je ni da Janan muke jan ta muje.
Mawuyaci ne kaji fadan mu ni da ita, idan ma kaji, ba akan son zuciya bane fadan, abu ne ziryan tsarkakke, ko kuma kawai sabawa da zaman tare yake kawowa. Wannan kuwa is natural, fada ce kuma ta ma'aiki, duk zaman da za ayi shi babu ire-iren samun sabanin nan, akwai alamar tambaya a cikinshi.

Nace "ke dai kawai sai dai muyi fatan Allah ya hada mu dana kwarai ne kawai, amma fa wani gyaran jikinki da wasu karairayar ki, babu abinda zai sa balle ya hana wallahi".
Tace "gaskiya ne, Allah dai yayi mana zabi mafi alkhairi, ya kuma bamu ikon zama dasu lafiya. Allah yasa mu cike ibadunmu lafiya".
Nace "ameen".

Tashi tayi ta shiga kicin tana fadin bari ta duba abinda ta dora akan wuta. Ni kuma na dauki wayata na turawa Yaya da yake kan hanyarshi ta dawowa daga kasar Germany, sakon Allah ya kiyaye hanya. Shekara guda kenan da aka maida shi Manajan gidan jaridar Daily Trust. Alhamdulillah, budi ta ko'ina muke samu. Tuni na haura matsayin da zan jira ayi min wata hidima komi girmanta kuwa, sai dai in yiwa wasu. Ko babu aikin da nake yi, Yaya Bilal ya kasance mijine mai tsananin kula da duk wata hidima ta iyalinshi.

Janan ta fito da kwaton bowl a hannunta, tun kafin ta karaso kamshin daddawa da tafarnuwa ya min iso, naja miyau na hadiya mukut!. Cikin da nake dauke dashi mai kimanin wata uku, ya sanya min tsananin son kwadayi da son ciye-ciye.
Ta ajiye farfesun kayan ciki dana sameta tana dafawa a gabana. Na shaki numfashi, dadin kamshin yana ratsa min har cikin kwanyata.

Nace "kyawunta abinnan ace har 'yar uwata zata samu".
Janan ta zauna a kusa dani tana zuba farfesun a cikin madaidatan plates, "ai fa, komi 'yar uwa, 'yar uwa. Na ajiye mata nata a microwave, don nasan kalar mitar da zan sha idan ban ajiye mata ba".
Nayi dariya, "kin kyautawa kanki kuwa", na karbi plate din data miko min na fara ci.

Ina cikin ci wayata tayi kara, hoton Hajara da aka dauka rungume da Muhaaseen ya bayyana, nayi murmushi, "kinga yar halas din ba", na dauka.
Fada min tayi ta tashi daga wajen aiki, zata biya makaranta ta dauko yara sai ta biyo nan ta daukeni, nace mata sai tazo.
Muna yan hirarrakinmu, har suka iso gabadayansu. Yaran suka zo suka rungume ni, na dauki Suhaima da take rarrafe na dora ta akan cinyata.
Janan ta zubowa Hajara da sauran yaran, suka fara ci. Yaranta sun riga su Muhaaseen samun hutu, suna Kaduna.

Suna gamawa muka fara haramar tafiya, Al-Qaseem da muke kira Papa, yarona mai kimanin shekaru uku da rabi, ya dauki Suhaima ya fita waje da sauri yana cewa bari ya riga mu. Duk muka rufa mishi baya muna dariya.
Janan ta raka mu har gaban motar Hajara, dankareriyar Maybach GLS 650, shigen tawa ce. Ba'a jima ba da Yaya ya canza mana su, ni tawa ruwan maroon ce mai duhu, tata kuma ruwan hoda mai haske. Na shiga gidan gaba, ina zama Papa ya dora min Suhaima akan cinya data mishi tumbud'i, yana yatsinar fuska yana mitar shi fa shiyasa baya son daukarta. Ni da Hajara kam dariya muke ta mishi. Janan ta karbi tissue a hannun Hajara data yago, ta goge mishi gefen riga. Daga nan dai muka daga mata hannu muka harba kan titi.

Muna isa gida, muka tura yaran daki akan su je su shirya kafin lokacin zuwa islamiya yayi. Mu kam shirin tarbar maigida zamu shiga yi.
Hajara tace "Yaya, idan mun gama zan nuna miki wasu sababbin kayan daki, kila wadannan suyi naga suna da kyau".
Nace "to shikenan".

Bikin Maryam yana ta matsowa, wannan shekarar zata gama degree dinta akan chemistry a ABU, tana gamawa kuma za ayi aurenta ba da jimawa ba. Ni da Yaya Mudatthir aka dorawa alhakin kayan dakinta, hakan bai dameni ba ko kadan, hasalima naji dadin hakan. Ko babu komi an nuna mana cewa muna da wani gurbi a wajensu.
Shi yasa ni kuma na daurawa Hajara aikin nema mana kayan daki har ma da wasu daga na kicin, masu kyau na garari, tunda fanninta ne. Tana aiki da wani babban kamfani ne anan Abujar, sukan zana abubuwa iri-iri, kayan daki ne, gidaje ne, makarantu, masana'antu, da sauransu. Akwai ainihin kamfaninsu dake Saudi-Arabia, shi yake kera ire-iren abubuwan da suka zana din, a sayar.

Tuni magriba ta fara kawo kai lokacin da muka gama. Muka yi wanka, muka cancada kwalliya kamar masu zuwa fashion show. Dole Hajara ta koya min zana gira da yafa eyeshadow, haka nan nake shafawa duk da ba ko wani lokaci ba. Amma kuma duk lokacin dana yi din na kan sha yabo da kirari wajen wanda aka yi domin shi din. Suma yaran muka shirya su bayan sun dawo daga makaranta. Daga nan zuwa kowane lokaci Yaya zai iya dirowa, tun dazu Balarabe ya tafi dauko shi.
Muka zauna akan manya-manyan leather seats din dake cikin falon da muka canza, muna duba kayan dakin. Har dai muka tsaya akan wasu jajaye da farare da suka mana, tace zata saka su cikin oda, nace mata to. Daga nan muka koma dakinmu muka yi sallah. Tun kafin in gama na fara jiyo hayaniyar yara, hakan ya tabbatar min da cewa maigidan ya karaso kenan. Banyi gaggawar fita ba sanin cewa ba nice da girki ba. Nasan zai fara yin wanka ne kafin ya wuce masallaci sallah.
Ina dakin a zaune ina karatun Kur'ani ya shigo, na mishi sannu da zuwa muka gaisa, ya wuce masallaci.

Sai bayan sallar isha'i muka hadu gabadayanmu a falonshi muka ci abinci. Ni da Hajara muka fara jidar kayan muna maidawa kicin bayan mun gama, Papa da Muahaaseen kuma suka tafi daukowa Abbansu takardunsu na makaranta ya gani.
Chapter 94 · 0% Book details