← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gida muka sauka, da yake tare da Balarabe muke, Yaya ya tsaya suka gaisa da Baba, anan ma suka sha ruwa tare da Baban da Balarabe, sannan suka wuce masauki.
Tarba mai kyau muka samu wadda ban yi zatonta ba, ba daga Baban ba, ba daga matan nashi ba, ba daga yaran ba, kowa ya nuna farincikinshi da ganinmu har abin ya bani mamaki.

Sai bayan tafiyar Yaya sannan na fahimci cewa da wani abu a kasa. Tunda muka je, Aliyu da Ramata suna daki, tun lekowar da suka yi suka mana sannu da zuwa suka koma daki, basu kara lekowa ba.
Yanayin yadda na ganta ya tsorata ni, tayi wata irin rama, sai girman shekarunta ya kara fitowa.
Bayan mun kebe a dakin Maryam inda nan na saba sauka, na tambayata abinda yake faruwa da masu gidan. Abinda ta fada min ya girgiza ni.
Wai Aliyu aka kama yana saida ganyen Iblis. Jiya yan sanda suka zo unguwar aka kama gungun yan unguwar da suke shaye-shaye, ga namakinsu sai aka hada dashi. Har wajen karfe ukun dare suna police office din wai, da kyar aka bada shi.
Na kama baki ina jinjina kai kamar zanyi ihu, "garin yaya haka?", na tambayeta, "ban sani ba", itace amsar data bani.

Muna nan a dakin nata muna maida magana, Awwal ya leko yace in je dakin Baba yana kirana. Na dauki hijabita na saka na tafi. Shi kadai na samu a dakin nashi. Na zauna a kasan kujera, muka sake gaisawa dashi a nutse ba kamar ta dazu ba da aka yi ta a tsaitsaye.

Kafin ya daga baki ya sake magana, sai ga Alawiyya da Ramata sun shigo dakin kusan a lokaci guda, duk suka samu waje suka zauna. Na kurawa matar da tunda na mallaki hankalin kaina ta hana ni shakar numfashi mai dadi a rayuwata. Akwai wani lokaci a can baya, da ko sautin muryarta naji tana tashi, sai naji faduwar gaba ta ziyarceni. Akwai wani lokaci da zan mata kallo daya, inji babu abinda nake so da kaunar sake gani kamar in daga idanuna in ga gawarta shimfide a kasan.

Sai dai a yanzu da nake sake dubanta sai naji babu wannan tsoron, babu wannan tsanar, sai tsananin tausayinta daya lullube ni. Hakan kuma baya rasa nasaba da yadda naga ta makure a gefe kamar bera a gaban mage, kanta a kasa yake tunda ta shiga dakin, bata yi gigin daga ido ta kalli kowa ba.
Ba'a jima ba, sai ga Aliyu ya shigo shima, ya nemi waje can kusa da Ramata shima ya makure.

Sai da kowa ya nutsu sannan Baba yayi gyaran murya. Hakan yasa duk muka maida hankulanmu gare shi.
Ya fara da cewa "Ke Na'ilah ke da baki gida, ke kadai ce anan da baki san abinda yake faruwa ba...", nan ya zayyane min duk abinda Maryam ta sanar dani.
Baba ya cigaba da cewa, "saboda haka na yanke shawara, ba zan cigaba da zama da tantirin yaro kamar Aliyu a gidan nan ba. Ba zai lalace ba, kuma daga baya yazo ya lalata min yara, ba zai yiwu ba. Don haka nace mishi ya fita ya bar min gida na tun a jiyan. Ban fada maka kada ka kuskura in dawo gidannan in gan ka ba?".

Aliyun bai ce komi ba sai kara lafewa da yayi a jikin Mamanshi yana shesshekara kuka, yayin da Ramata din take share hawaye itama.

Alawiyya ta wurwusa ta matsa kusa da Baba, tace "Alhaji kayi hakuri da wannan magana da zanyi, amma matakin daka yanke kwata-kwata bai dace ba, ina ga da dai ka sake shawara".

Baba yace "shawarar me zan sake? Zubda kimata da mutuncina yaron nan ya riga yayi, yanzu duk cikin unguwar nan kowa zancen yake yi. To zai zauna yayi min a gida kuma? Ba zan iya ba, ya tarkata nashi-i-nashi ya bar min gida kawai".

Sai lokacin na samu kwarin gwiwar yin magana, nace "Baba kamar yadda Anty tace, wannan fa ba shawara bace. Zancen zubewar girma da sauransu, duk bata taso ba, tunda abinda dai ya faru ya riga ya gama faruwa, kuma ba'a dawo da hannun agogo baya. Abinda ya faru ya riga ya faru, sai dai a tari na gaba kawai. Amma korar Aliyu daga gidannan ba mafita bace, Allah ya gani. Baka tunanin idan ka kore shi din, maimakon ya saduda, sai hakan ya kara sanya shi yabi wata hanyar daban kuma? Duk kuma dai abinda zai yi nan gaba kana da alhaki akai, kuma duk inda zai je ya dawo dai, nan da shekaru goma ko dari, dole ya dawo gareka saboda danka ne, tsatsonka ne. Shi hannunka ai baya rubewa ka yanke ka zubar".

Baba yace "sai dai in hannun baya damuna. Amma tuni zan yar da dan banza in huta. Tun yaushe Aliyu yake bata min rai? Makaranta baya zuwa daga ta boko har ta islamiyar, bai san komi ba sai daukar magana a cikin unguwa. Yau ya zagi wancan, gobe ya bugi dan wancan, shi kadai ranshi yabi ya addabi mutane ina dalili?".

Nace "hakuri dai za ayi, shima ba zai kara ba".

Baba ko in ce iyaye da dama, suna da wani hali na sangarta yaransu, to the extent that sangartawar zata wuce misali. Yara zasu lalace, su daina ganin kan kowa da gashi, wani abin dariya ko tausayi shine yadda hatta da iyayen nasu ma zaki ga basa jin maganar su. Sai labari ya sha banban, yaro yaje ya dauko magana, sai kuma anan iyaye suzo su ce basu san wannan ba. Su zo su kori yaran. To me kenan aka yi? Ihu bayan hari kenan. Maimakon tunda da sanya hannunka hakan ta faru, ka tsayawa yaronka ya koma gagara-badau, lokacin da yayi tashen tsageranci da rashin da'a ka tsaye mishi, maimakon idan sun dauko maganar da tafi karfinsu su sake tsaye musu, a'ah, sai suce sun janye hannunsu daga garesu.
Sun manta lokutan da suka tsaye musu suka dinga yin abinda suka yi din, har suke ganin babu wani ko wata wadda ta isa sai su.
Don bana manta lokuta da dama da mutanen unguwa zasu kai karar Aliyu wajen Baba, akan wani abu da zai musu, muma mun sha kaiwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma bai taba daga baki yace mishi don me? Ko kul ba.
To yanzu idan iyaye basu dauki responsibility din laifukan 'ya'yansu ba, wanda idan aka yi duba tun tali-tali suna da kamasho a ciki, wa zai dauka?

Bayan doguwar muhawara da jeka-ka-dawo, da kyar muka samu ni da Anty Alawiyya Baba ya sassauto. Duk wannan abu da ake yi, Ramata da Aliyu na gefe in banda sharar hawaye babu abinda suke yi.
Daga karshe dai yace ya hakura, akan sharadin idan makamancin haka ta sake faruwa lallai zai kore shi. Ni dana kasance zabiya, ni nace naji na amince. Nan ya sake hada mu yayi mana nasiha mai shiga jiki, yace ya sallamemu.

Ina tashi, Ramata ta kamo hannuna. Kuka take sosai kamar wadda aka yiwa mutane, godiya take jera mana kamar harshenta zai fado kasa, "nagode, nagode, Na'ilah! Yau da ba don ke ba ban san yadda zanyi ba, Allah yayi miki albarka, nagode!!".
Ni kam na ma rasa abinda zan ce mata, jiki a sanyaye na dinga binta da kallo har sai da tayi radin kanta ta sake ni, sannan na juya na fita daga dakin.

Kai tsaye dakin Aliyu na wuce, na same shi a gefen katifarshi a zaune. Zama nayi dirshan a tsakiyar dakin, magana muka yi mai tsayi ni dashi game da abinda ya faru. Ba karamin mamaki na ci ba lokacin daya fada min wai kudi yake bukata shi yasa ya fara saida tabar saboda yaga abinda yaran unguwar sa'anninshi suke yi kenan, kuma suke samun kudi.
Nace "kai kuwa me ka nema ka rasa haka?".
Yace "to Baba baya bamu kudi, yanzu ko Mama baya bata. Kudin makarantarmu kusan term biyu bai biya ba, sai da aka koro mu. Kuma Mama bata da lafiya, in taje asibiti aka bata magunguna, Baba baya sai mata. Ya zamu yi?".

Wannan a halin Baba kam ba abin mamaki bane, haka yake. Duk wadda baya dasawa da ita a cikin matanshi, to ba ita kadai ba, har 'ya'yanta ma sai sunji a jikinsu. Na gani a kaina, hakan kuma ta faru akan ido na. Ina ga ina bukatar mu sake zama na musamman da Baba. Yana bukatar wani ya fahimtar dashi irin wannan rashin adalcin nashi, ba abu bane mai kyau. Sai dai dana sake tunanawa, sai naga ba hurumina bane hakan. Watakila Yaya dai zai iya shiga cikin maganar tunda duk cikinmu, baya jin maganar kowa kamar tashi.

Nan na zaunar da Aliyu, na fahimtar dashi cewa hakan fa ba mafita bace, sai jefa kanshi daya kusa yi a cikin halin k'ak'a-ni-kayi. Na tunatar dashi muhimmancin hakuri, da cewa ita rayuwar duniya ba lallai bane sai ka mallaki abinda kake so ba. Tunda ba duka kake samun komi ba, kuma idan kace kai sai ka mallaki komi to kai zaka kwana ciki kuwa. Na jima sosai a dakin nashi kafin na tashi na koma dakin Maryam.
Ina zuwa na tadda Kulsum, nan muka hau hirar yaushe gamo. Tana nan har an sanya musu ranar aure da wani lakcaran su. Sai da za'a rufe gida sannan ta mana sallama ta tafi.
Bayan munyi shirin kwanciya, na dauki waya na kira Yaya Mudatthir na zayyane mishi duk abinda ya faru. Yace Baban ya mishi waya a jiyan, amma bai sanar dashi hukuncin daya yanke ba. Mun jima muna tattaunawa dashi, daga karshe muka yi sallama dashi akan cewa cikin satin zai zo. Bayan mun kashe wayar, Yaya na kira muka raba dare muna hira. Muna gamawa ko barcin minti talatin banyi ba, na tashi sallar tahajjud.

Da asuba muka tashi ni da Maryam muka dafa abincin sahur. Bayan munyi sahur, Mazan sun tafi masallaci, mu kuma muka yi tamu sallar a daki. Na dauki Al-Kur'ani mai girma na fara karantawa.
Chapter 85 · 0% Book details