← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 95

Sashe 80

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabadaya yinin yau a kasalance nayi shi, tunda na tashi da safiyar yau nake ji na ba daidai ba. Jikina yayi min nauyi, da kyar na dinga gudanar da ayyukan dana saba yi.
Zuwa yamma, abin ya kara tsanani da kamari. Ina zaune ina yin azkar din dana saba yi, idanuna suna likewa saboda wani azababben barci daya mamaye min idanu. Duk yadda naso in daurewa barcin nan, kasawa nayi. Ban san lokacin daya kwasheni ba anan.

Sai gab da magriba na tashi a firgice. Nayi salati ina jan addu'o'i a cikin raina, ban saba barcin yamma ba, kai barcin rana ma gabadaya ban cika yin shi ba, balle na bayan sallar la'asar.
Mutuwar jikina har tafi ta dazu, na lallaba na fada bandaki nayi wanka da ruwan dumi. Kasancewar bana yin sallah, sai na gyada jikina kawai na fito.

Washegari, na shiga gaida Yaya. Yana zaune a falonshi, matan nashi sun zagaye shi yana karin safe. Ameerah da har yanzu ciki bai fara turowa ba, an ci kwalliya ta kece raini, fuskarnan baka ganin komi sai kyallin foundation, concealer da eye shadow.
Raheemah ma taci tata kwalliyar babu laifi.

Na duka a gefenshi na gaida shi, bai ko daga kai ya kalleni ba, ya amsa ciki-ciki kamar wanda aka takurawa, yaci gaba da cin abincinshi. Babu tambayar 'ya kika tashi' ko kuma 'kin tashi lafiya?'. Wasu lokutan ma da yake cikin yanayi mai dadi, ya kan kara da 'da fatan kinyi mafarkina?'.

Sai ban kawo komi a cikin raina ba, na juya na gaida matan nashi da suma suka amsa ciki-ciki, su dama sun saba, don haka ban damu ba. Yaya ne dai da ba haka ya sabar min ba, duk sai naji abin yayi min wani iri. Amma zata iya yiwuwa ko bai tashi cikin dadin rai bane yau. After all, mu dukanmu mutane ne, we all have our moments.

Ban jima ba, na koma dakina na gama shiryawa nima na tafi asibiti. Aikin safe nake yi wannan satin.

Koda na dawo daga asibitin, kasa zama dam nayi. Jikina tun jiya nan bai dawo daidai ba. Ji na nake yi kawai kamar ba ni ba. Ranar sai dana juya gabadaya tsarin dakina duk don in dan ragewa kaina zaman banza da tunanika marasa amfani.
Har zuwa can yamma ina abu daya, nayi wanka na sanya wata doguwar riga single, na dauki wayata tare da zura takalmi flat a kafata na fita falo.

Raheemah na kicin tana kammala girki, na zauna akan kujera, na dauki remote na kunno wata tasha suna karatun kur'ani. Na kwanatar da kaina akan hannun kujerar ina bin karatun a nutse. A hankali naji nutsuwa ta fara shigata.

Ina nan har Yaya ya dawo daga wajen aiki. Na tashi zaune ina kallonshi cikin murmushi, "Yaya sannu da...".

Kafin ma in gama mishi sannu da zuwan, ya fada falonshi da sauri. Babu alamun ya kula dani a cikin falon da ya nuna, idan ma ya ganni din, ba karamin kokari yayi wajen share ni ba. Sai na bishi da kallo baki a dage.

Da dare kamar yadda aka saba, na tafi falon Yaya da niyar zuwa yin hirar dare. Suna zaune su duka ukun, Yaya da Raheemah suna hira, Ameerah kuma zaune a gefensu.
Na zauna a kusa da ita na musu sannu, Yaya da Raheemah suka yi shiru da hirar da suke yi suna kallona, babu wanda yace min ci kanki. Kafin suka komawa hirarsu.

Ko minti goma cikakke banyi ba, naji zaman wajen ya isheni. Yadda Yaya yayi kamar babu wata halitta a cikin falon face Raheemah kadai, abin ya sanyayar min da gwiwa. Ita kanta Ameerah din da idan da ne, duk wani motsi da zata yi zai yi ta binta da sannu, yanzu ko yunkurin tsoma baki tayi cikin hirar da suke yi, haka zaka ji yayi duf, sai kallo da zai yi ta binta dashi.
Da abin ya dameni, sai kawai na tashi na musu sai da safe don ba zan iya cigaba da zama a haka ba.

Wasa-wasa fa karamar magana sai ta fara kokarin zama babba. Shi kenan a wannan gidan yanzu babu wadda Yaya yake ganin tsakiyar kanta da gashi sai Raheemah kawai.
Lokacin da girki ya juyo kaina, sai dana kara raina kaina. Ranar Yaya bai shigo gidan ba sai can bayan isha'i. Na mishi sannu da zuwa ya amsa ciki-ciki, ya shige can kuryar daki.
Ban yi fushi ba, na bishi har dakin nace mishi ga abincin shi fa. Sai ce min yayi ai ya koshi.

Nace "ka ci abinci ne a waje ko kuma cikinka ne a cike?".
Sai ya dago ya kalleni fuskarnan a cune, "to wai idan ma naci abincin ko kuma na kasa ci, menene matsalarki? Cikinki ko nawa?".

Da yaga nayi shiru ina kallonshi ban ce komi ba, sai ya wawuri towel dinshi ya fada bandaki yana mitar duk na bi na tsangwame shi sai kace wani karamin yaro.

Na zabga uban tagumi har ya fito daga wankan ya sameni a yadda ya barni. Bai ce komi ba, ya fara shafa mai.

Nace mishi "Yaya, ko dai wani abu nayi maka ne? Idan ma haka ne, don Allah kayi hakuri. Ba da sani na nayi hakan ba".

Murya ciki-ciki yace "to ni nace ne kin min wani abu? Ko kuwa don dai shi mutum bashi da damar yace ya koshi da abinci, sai a hau tuhumar shi. Wai ni karamin yaro ne, iye?".

Gabadaya sai nake ga kamar Yayan an canza min shi da wani na daban. Wanda ban sani ba, wanda ban san komi nashi ba. Naji kwalla ta fara cika min idanu.

Sai ya dakata da abinda yake yi, ya kama baki yana kallona. Yace "to yanzu kuma me na miki da zaki sanya ni a gaba kina kuka?". Na girgiza mishi kai alamun babu komi.

Yace "abinci ne dai ko? Bari in zo in ci, shikenan?".
Na gyada kai ina dan murmushi, ina share kwallar data fara zubar min.

Bayan ya gama, muka rankaya zuwa falo, na zuba mishi abincin. Kadan yaci, hakan bai dameni ba, cin kadan din ai yafi rashin ci gabadaya.

Anan na barsu shi da matan nashi suna shan hirarsu. Har yanzu dai jiya i yau, bata sake zani ba. Ita kanta Ameerah na kula hakan ya dameta, bata fito fili ta fada bane kawai.
Dana koma falon, ban zauna ba, sai na shige can ciki nayi kwanciyata. Har Yayan ya shigo shima, ya gama duk abubuwan da zai yi, ya hayo kan gadon ya kwanta.

Ganin ya juya min baya ba tare da yace komi ba, yasa na gangara zuwa gefen daya kwanta. Nima na kwantar da kaina akan kafadarshi. Daga farko sak yayi kamar wanda lantarki taja, sai kuma ya saki jikinshi. Ana jimawa naji ya zame ya kara matsawa can gefe guda.

Wani irin makaki yazo ya takure min a cikin makoshina, wata kwallar ta sake ciko min idanu. Sai nima na juya mishi baya.

Zuwa can cikin dare na farka, na ganshi zaune a gefen gado, idanunshi kur a kaina kamar wanda yayi nisa cikin dogon tunani. Ban nuna alamun na farka ba, naci gaba da kallonshi ta cikin dan hasken dakin har barci ya sake kwasheni.

*☆⋆46⋆☆*

Har na fita daga girki na sake shiga wani, bata canza zani ba tsakanina da Yaya. Hankalina idan yayi dubu to a tashe yake. Wannan shine karo na farko dana taba fuskantar yace baya daga mijin aurena, bana kuma fatan hakan ta kara faruwa koda wasa ne. Yadda yake yi kamar duk duniya babu abinda yaki jinin ya gani kamar ni, shine yafi tayar min da hankali. Nan da nan nayi rama. Yanzu na samu yana cin abincina ba tare da bacin rai ba, sannan yana dawowa da wuri ranar girkina. Daga wannan shikenan, idan ma na samu ya amsa min gaisuwata da sannu, to naci sa'a.

Inda naji dadi daya ne, duk da dai ba abin jin dadi bane, ganin cewa ba ni kadai hakan take faruwa da ita ba, har da Uwargida Ameerah, duk da cewa dai ita yana dan daga mata kafa saboda cikin jikinta, amma dai babu gwara.
Hakan ya tabbatar min da cewa lallai da wata a kasa. Ta fannin addu'a da kula da jiki, ina iyaka kokarina dama, sai kara dagewa da nayi. Takanas na dauki kafa naje har Suleja wajen Malam Ali, da yake ya daina kawo mana rubutun da yake kai mana duk sati. Bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan, aka min jagora zuwa inda yake karbar bak'inshi.
Mun jima muna hirar yaushe gamo, daga karshe dai na mike kafa na mishi bayanin abinda yake tafe dani, tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yau.

Nan ya bani wasu addu'o'i yace in lazimci yin su, shima kuma yace zai dinga taya mu. Ya kara da cewa "ku matsalar ku ta yan boko, sai ku ce baku yarda da sadaka irin wadda ake rabawa yaranmu suyi ayi yanka da sauransu ba. Ita kuwa sadaka abu ce mai kyau, koda wani abu mummuna bai faru da kai ba, ta kan kiyaye mutum daga munanan abubuwa da dama, haka kuma tana tsare shi daga kambun baka, sihiri da sharrin jinnu. Baka san bakin mutane ba, akwai wasu zababbu a cikinmu, da idan suka yi mana addu'a zaki ga kamar da bakin yan amin suka yi ta, Allah ya karba. Shi yasa muke rarrabawa, saboda bamu san inda albarkar take ba".

Na gyada kai cikin alamun fahimta, nace "haka ne Malam. Muma din muna kwatanta yin hakan, amma zamu kara zage damtse in Allah ya yarda. Yanzu zan bayar da kudin sadakar kafin in tafi, in yaso sai ayi duk abinda yakamata dai".

Ya girgiza kai, "kada ki damu 'yar nan, babu abinda zai gagara da yardar Allah. Yaran nan namu ne, dan abinda ya rage kuma bai fi karfin aljihunmu ba, saboda haka za ayi duk abinda ya dace. Ke din ai diya ce a wajena, jinin Malam Audu tamkar jinina haka na dauke su".

Nayi murmushi nace "nasan da hakan Malam, amma duba da cewa sadakar tawa ce, me zai hana ka barni in bayar da kaina?".
Chapter 80 · 0% Book details