← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 95

Sashe 15

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashin Maryam a dakin shi ya bani damar jingina da bango, na tsunduma cikin tunani mai zurfi. Yakamata ace na saba da abinda Baba yake yi min, sai dai, kamar yadda ba'a taba sabo da wahala, haka ma ba'a sabo da bacin rai. Musamman idan wanda yake haddasa maka hakan ya kasance majibanci, kuma majingini a gareka, wanda kake ganin zaka iya rab'a a duk lokacin da komi ya yaye maka baya, kuma ya tallafa maka. Sai dai no, ko kadan ba hakan take ba.
Lokacin da zamu tafi registration dinmu na farko, haka Baba yayi min wannan delaying din. Sanadiyar haka na rasa accomodation a cikin hostel, wata kawarmu da muka yi sbrs da ita, ita tayi squatting dina. Believe me when I say, it wasn't fun at all. Ban taba raina kaina ba sai a wannan lokacin, ban taba jin dadin rayuwar gidanmu ba, in fact, ni zan iya dukan kirji in ce rayuwar makaranta ta fiye min rayuwar gidanmu, amma a wancan lokacin sai dana fara rethinking wannan tunani. Sai dana gwammace rayuwar gidanmu sau dari akan wannan rayuwar. At least a can, ina da wajen da zan kira dakina, sannan duk lokacin da dare yayi, a gida nasan cewa ina da wajen da zan kwantar da hakarkarina, amma ban da nan.
Haka taci gaba da faruwa, for once, ban taba biyan makaranta akan kari ba, kullum, kuma kodayaushe, sai na kara kwanaki ko satika, duk da cewa kowani lokaci nakan fadawa Baba da wuri yadda zai tanadi kudin, but no, kodayaushe akwai uzirin da zai ratso ya shiga ta cikin kudinnan. Ban sani ba, daga gareshi ne ko daga matanshi, ko kuwa in ce matar shi? Allah ne masani.

Yaya Mudatthir, Allah ya albarkaci rayuwar shi. Da ba don shi ba kam, ban san yadda karatuna zai kasance ba. Idan Allah ya taimaka yana da kudi, shi yake daukar jigilar registration dina, daga baya in Baba ya turo, in tura mishi, duk da a yawancin lokuta ya kan dawo min dasu ko kuma yace in barsu, sai dai in maida mishi rabi ko ya dawo min da rabi.
Ko last year, Allah ne yasa Yaya Jameel, yayan Janan, da yake lecturer ne a cikin makarantar, ya bata daki, Yaya ya hanata zama, ni kuma ta bar min shi.

Da tunanika iri-iri na kwanta. Sau tari sai inji gabadaya karatun ya fita a cikin raina, inji kawai gwanda in hakura dashi, in huta da bakinciki da takaicin da nake kwasa daga wajen Baba. Sai dai wasu lokutan, sai in ga daurewar tafi. Musamman idan naga cewa shine kadai gatana a yanzu. Karatun shi zai tallafa min, in tsaya akan kafafuna ba tare dana jingina da wani ba. Idan nayi hakuri, na dan lokaci ne. Komi wucewa zai yi, ya zama tarihi, kamar bai taba faruwa ba. At least, abinda nake fata kenan.

*

Washegari da dare, mun zagaya nan bayan gidanmu ni da Kulsum dubo wata Hassana wadda muka yi aji daya da ita a makarantar Islamiya. A hanyarmu ta dawowa, muna tattaunawa game da matsalolin da ita Kulsum din take fuskanta daga tsohon mijinta.
Ya fara mata zarya akan cewa yana so ya amshi Muneerah daga wajenta, ita kuma tace gaskiya bata son bashi ita.

Ni kaina shawarar dana bata kenan. Nace idan da yadda zasu yi akan haka, gaskiya suyi, ya bar mata diyarta ta tarbiyantar da ita a gabanta. Tunda ma ba maganar aurenta bace ta taso, ko iddah bata gama ba, balle yace ta wannan dalili yake son karbar ta.
Wahalhalun dana sha a hannun kishiyar uwa, shi nake guje mata. Duk da cewa ni rashin mahaifiya ne ya jawo min, ita tata mahaifiyar tana raye. Kuma tana ji tana gani, haka za'a fi karfinta akan diyarta. Bana fata ko makiyina ya dandani kwatankwacin abinda na dandana. Abinda na dinga tunani a cikin raina kenan, ban furta mata hakan ba amma.
Koda kasancewarta kawata, ko ma ince aminiya, tarihin gidanmu, da irin zaman da nayi da mutanen gidan, dama wanda nake yi, ba duka ta sani ba. Ta dai san wanda kunnenta ya jiye mata, kuma idanunta suka gane mata, shikenan. A tunanina, tado abinda ya wuce, yake kuma sosa ran mutum, duk ba solution bane. Hakan babu abinda zai haifar sai ma wani karin bacin rai, hakan zai sa ka kullaci mutane a cikin ranka, kila dan mutuncinta da kake gani nasu ya zube. Babu abinda zai sa, kuma babu abinda zai hana.

Daidai bayan gidanmu, na hangi wata yarinya Lubah, yar dakin Ramata ce. Anan cikin unguwar take, duk wata gulma da tsegumi daya taba gidanmu, daga gidansu yarinyar yake fara fita.
A durkushe na ganta, kamar tana tona kasa ko kuma wasa take yi? Sai waiwaye take yi da kalle-kalle, kamar dai wadda take tsoron wani ya ganta. Na dan yamutsa fuska in suspicion, kamar zan karasa in ga abinda take yi, sai kuma naga hakan ba hurumina bane, tunda ba shiga harkarta ko ta mutanen gidansu nake yi ba. Muka wuce ta.

A tsakar gidan su Kulsum muka zube ni da ita akan tabarma, muka cigaba da tattaunawa. Mun yanke shawarar zata je ta samu Kawunta tayi mishi bayani, zai je ya samu iyayen Mukhtar din sai suyi mishi magana. A cewar Inna, hakan zai fi kawai, in yaso idan ta tashi yin aure, ko kuma Muneerah din ta fara mallakar hankalin kanta, sai ta koma din. Tunda dai duk inda za aje a dawo, gidan mahaifin nata dai nan ne mutuncinta. Da wannan na musu sai da safe na wuce gida.



Washegari Laraba, nayi sa'ar samun Baba kafin ya tafi wajen aiki. Na gaida shi, ya amsa yana kora shayin da Alawiyya ta hada mishi, yayin da Ramata take gefenshi zaune a hakimce. Yadda nayi zaune a gabanshi, nasan cewa yasan dalilin yin hakan, amma ya basar dani.
Ban yi fushi ba, na kaskantar da murya, nace "Baba zancen registration dina?".

Daga farko shiru yayi kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi gyaran murya, yace "kudin nan naki fa sai dai kiyi hakuri sai zuwa satin da zai kama. Ranar litinin zan biyawa kaninki kudin waec da neco, abubuwan zasu yi min yawa!".

Wani abu daya kusa bani dariya shine, jarabawar waec da neco zata iya jira har nan da watanni biyar zuwa shida masu zuwa, tunda dai ba'a fara zancen yin ta ba balle akai ga saka deadline din wadanda basu biya ba zasu rubuta jarabawar ba da sauransu. Naso in tunatar dashi hakan idan ma mantawa yayi, yadda naga ya zubo min ido ne yana jira yaji ta bakina, Ramata ma da Alawiyya sun zubo min nasu suna jira inyi magana, kila dalilin haka Baban ma yayi fushi, satin samar ma yazo yace bashi da kudi, yasa na hadiye duk takaicina da kududun daya makale min a makoshi, nace "to babu laifi, Allah ya hore!". Na tashi na kara gaba. Banyi kuskuren ganin yadda suka bini da kallo baki a dage ba.

Magana ta gaskiya ita ce, na gaji da takaicin da suke guma min. Daga Baban har su. A kullum, kuma a kodayaushe, hidimar kansu data 'ya'yansu ita ce ta farko a idanunsu, koda tawa matsalar tafi bukatar agajin gaggawa, haka za ayi shagulatin bangaro da ni da lamarina, har sai an biya musu nasu bukatun. Idan kuma nayi magana, sai cibi ya zama kari. All tables will turn, and bets will be off. Sai laifi ya dawo kaina, ace na cika bakin ciki, su ce bana son cigaban su ko na 'ya'yansu, su ce bani da godiyar Allah, daga karshe kuma su zo suyi sanadin wannan abin ba za'a yi shi ba kenan. Idan ma anyi, to a kurarren lokaci ne.
Saboda haka naga, meye amfanin yin maganar? Babu abinda hakan zai karas dani sai bacin rai. Meye kuma amfanin sanya maganar a cikin raina, again, sakamakon hakan dai bacin rai ne. Don haka nayi wurgi da maganar cikin kwandon shara, naci gaba da harkokina cikin kwanciyar hankali.

Sai dai Baban yana fita, sai ga Ramata ta fiddo dankareren Swiss lace daga daki, ta fito tsakar gida tana ba danta Aliyu da bai je makaranta ba, labarin jiya Baba ya bata kudin, dubu ashirin da biyu ta sayo, ya kara mata da dubu uku kudin dinki. Tace yayi maza-maza yazo ya kai mata shi wajen telanta ya watsa mata dinki na rashin mutunci, na shiga taron manya.
Nasan duk don inji haushi take yin hakan, sakonta kuma ya shigeni yadda yakamata, naji haushin. Sai dai wannan karon ma maimakon magana, sai na kada kaina na shige daki. Ai sai ina wajen sannan zata yi tunanin tsokano ni ko? Sai dai ga yadda na ga fuskar Alawiyya, to ta shaka da yawa. Nasan a cike take dam, kiris take jira ta fashe. Nasan kuma da Baba ya dawo zata tare shi da maganar, idan Allah ya taimaketa, ya dorata a kanshi itama ya siyo mata lace din ko ya bata kudin yace ta dinka. Wanda kuma da kyar ne, hakan sau daya yake faruwa a gidanmu a shekara.

A tunanina, idan mutum ya sai wa matarshi wani abu, itama dayar tana da hakkin ya sai mata irinshi, ko kuma ya bata adadin kudin daya batar wajen sayen abin? But no, banda gidanmu. Ban taba ganin haka ba, koda wasa.
Yawanci idan abu makamancin haka ya faru, sai dai hakan ya kare ga fada kawai. Ita Alawiyya bata hakura, kullum aka yi haka sai ta bukaci itama a bata nata kason, lokuta daidaiku ne Baban yake bata, basu fi a daga hannu a kirga su ba.
Wani lokacin tausayinta dana 'ya'yanta yana cika raina, amma nafi tausayawa Ramata dana 'ya'yanta.

Wunin ranar haka nayi shi smoothly. Da yamma ina kicin ina tuka tuwom dare, Maryam ta fado kicin din da sauri, wayata dana bata tayi kallo tana ringing a hannunta, ta miko min. Na duba naga mai kiran Janan ce, da sauri na daga ina murmushi.
"Hi...", na furta a hankali, da niyar gaisuwa.
Tace "hii yourself, yaushe kike da niyar dawowa makaranta ne? Ni fa har na dawo Zaria".
Na zaro ido cike da mamaki, "wow, lallai kina kaunar Zaria da yawa. Ni yanzu haka ban san ranar dawowata ba".
Chapter 15 · 0% Book details