← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 95

Sashe 89

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya yace "ban gane ba? Ke lafiyarki lau kuwa? Me ke damunki ne?".
Tace "ka ga bawan Allah, ba wasu maganganun banza na tambayi ka min ba, idan kana son arzikin kanka, to kawai ka miko min takardata in kara gaba. Dole ne? Nace auren naka dole ne wai?".

Saboda tsabar mamaki Yaya kasa magana yayi, kawai zama yayi yana kallonta, kamar yadda nima na sankame a zaune.

Tace "ni fa bani da lokaci kaji? Ka sallameni don Allah".
Yaya yace "ba zaki zo kai tsaye ba kawai ki ce in sallameki, akan me? Akan wani dalili?".
Tace "saboda na gaji da zama da kai, zama da kai haukata zai yi. Kawai ka sake ni, ka sakeni nace!!". Zuwa yanzu karaji kawai take yi. Tana rufe baki ta juya zuwa dakinta a sukwane, bata jima ba ta dawo hannu rike da takarda, ta jefa mishi jikinshi, "maza maza rubuta min in wuce Malam".

Wani abu yayi snapping a jikin Yaya, kamar wani wanda aka yi possessing, kawai ya dauki takardar da biro ya hau rubutu, ko sauraren ihun kada ya aikata abinda ba'a so a aikata a cikin aure da nake mishi bai yi ba. Yana gamawa ya mika mata, ta warta tana karantawa cikin yatsina fuska.

"Saki biyu? Karya kake wallahi, wallahi sai ka cike min shi. An gaya maka wata tsiya nake kwasa a gidanka da zata sanya ni son dawowa gidan? Kai yau fa idan baka sallameni ba wallahi sai ayi yakin duniya a cikin gidannan! Kaji ma wani rashin mutunci!". Ta hau wasu maganganu marasa kan gado da ma'ana.

"...Dama boka sai da yace kada in bari iska ta share wannan maganin, wannan shegen tsinannen mai sharar wannan yazo ya share shi. Dama sai da yace kaikayi koma kan mashekiya ne, kaina zai dawo muddin bata tsallaka shi ba. Saki uku yakamata ka mata, ni me yasa ba zaka min saki ikun ba?".

Yaya ya tashi tsaye a hankali yana fuskantarta, "me kika ce? Me kike nufi?".

Ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya kamar wata mahaukaciya, "to ina ruwanka da abinda nace? Abinda za ka damu dashi shine karashen saki na. Kasan wani abu? Boka ya bani wani magani yace in jika shi ya kwana uku, sai in tace in ba waccan sakarar matar taka data kunshi ciki, tana wani daga kai sama tana tutiya ita zata haifi magaji..."
Ni da Yaya muka zare idanu muna kallonta, saboda nasan inda maganar ta nufa. Bata damu da yadda muka yi ba taci gaba,
"kasan me nayi? Sirinji na sayo na zuki ruwan maganin, nawa mangwaron da zata sha allura. Hahhha!". Ta sake wata dariyar. Tuni kwalla ta gama wanke min idanuna.
"Sakara, ina kallonta har wani rawar jiki take yi zata sha mangwaro, bata san cikinta zata fitar ba!".

Na kai hannu bakina na rufe cikin kokarin danne kukan daya taso min, ita kuwa taci gaba da sheka dariyarta.
Karan marin da Yaya ya zuba mata, sai daya karade falon gabadaya. Yace "dama kece kika zubar min da cikina? Kodayake, I've had my suspicions tun daga farko. Saki kike so ko? To kije na karasa miki sakin na uku, meye amfanin zama dake dama? Tunda na aureki na rasa walwala a cikin rayuwata, ban ma san dalilin da yasa na aurekin ba, amma hakanan nake hakuri ina zama dake. Kuma abu dayan da yake sanya ni farinciki ki ce zaki raba ni dashi? Ki fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura in dawo gidannan in same ki don wallahi sai na wulakanta ki. Kada kuma ki daukar min ko allura daga cikin kayana!!".

Yaya ya fita daga cikin falon da sauri kamar wanda zai tashi sama, ya barni sarkafe a tsaye ina kallon Raheemah da take ta dariya babu kakkautawa babu alamun zata daina.
Sai gashi kuma ya dawo, "kin san me? Fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura ki sake dawowa!".

Sai lokacin ta dakata da dariyar da take yi, "yo dama ko baka ce ba fita zan yi. Gidanka da kayanka din banza dana wofi?". Ta shige dakinta ta fito da gyale a hannu daya, purse da waya a hannunta daya.

Yaya ya saka ta a gaba kamar wata barauniya har bakin gate, sai data fita daga gidan sannan ya juya yana gayawa maigadi kada ya bari ko jingina da gate din gidan tayi balle ta kai ga shiga. Maigadi da rawar jikinshi yace "an gama Alhaji!".

Kawai sai ta zube kasa ta fashe da kuka, kukan ihu bayan hari, kukan nadama da bata da amfani. Tana ba Yaya hakuri, wai don Allah yayi hakuri ya maidata, sharrin shaidan ne. Yaya ko kallonta bai kara yi ba, ya ja hannuna zuwa cikin motarshi ya tada. Maigadi ya bude mishi gate ya fita a sukwane, muka wuce Raheemah tsugune anan, crying her heart out.



Wajen aikin su Yaya muka wuce. Kai tsaye ofishinshi da yake hawa na goma sha biyu muka wuce. Muna shiga ya dauki land-line ya kira secretary dinshi yace tayi oda din abinci. Ya zauna akan kujera yana maida numfashi.

Tashi nayi tsam na koma kusa dashi na zauna, na kamo hannunshi na rike a hannuna ina shafawa soothingly. Gabadaya ya ma kasa magana, mun jima a haka, kafin ya iya daga baki. Maganganu suka fara fita daga bakinshi kamar ana turo su, duk akan yadda Raheemah ta cuce shi ne.
Ban ce mishi komi ba sai hakuri kawai da nake bashi har ya dan nutsu, nace mishi "ka daina blaming dinta, abinda Allah ya kaddaro dole sai ya faru babu makawa, babu kuma tsumi balle wata dabara ta mutum. Raheemah ta saka min magani ko bata saka ba, dole cikin jikina ya fita tunda Allah bai kaddaro zai taka kasa ba. Don haka ka daina damun kanka don Allah, don't beat yourself for it".

Ya kalleni, "for real baby? How are you this calm? Da kunnenki fa kika ji abinda tace, ita ta zubar mana da ciki. Kin kuma ji abinda likita tace, that ba lallai ki iya kara samun wani cikin ba cikin lokutan nan".

Murmushi na sakar mishi mai sanyaya zuciya, na kamo hannunshi na dora a saman cikina, nace "saboda shi Allah ba azzalumin bawa bane, baya kuma dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba. Yasan abinda yake cikin zuciyoyinmu, ya kuma fimu sanin cewa muna bukatar ganin sanyin idaniyarmu a gabanmu...".

Nayi shiru ina kallonshi, ina jiran yayi calculating din abin da kanshi. Ba'a jima ba kuwa ya gama tarawa da ninkawa, ya kalleni, "kina nufin..?".

Na gyada mishi kai a hankali ina murmushi, gefe daya kuma ina danne kwallar data ciko min ido.
Bakinshi rawa yake, da kyar ya iya kakaro kalmar "how... wata..?".
Nace mishi "sati biyar".

Daga nan bai ce komi ba, sai janyo ni cikin jikinshi da yayi ya rungume. Ba sai yayi magana zan san yana cikin tsananin farinciki ba, saboda na sani, wani farincikin yafi karfin ka daga baki ka bayyana shi, saboda duk kokarinka da iya bayyana abu, farincikin nan ba zai taba iya bayyanuwa ba. Halin da Yaya yake ciki kenan a halin yanzu.

Sai da aka kawo abincin da yace a kawo, sannan ya zameni daga jikinshi, yadda ya maida ni cikin kujerar ma ya ajiye kamar wani kwai kadai yasa na bi bayanshi da kallo cike da murmushi, kaunar mijina tana kara dabaibaye ni.
Ya amso abincin ya dawo, da kanshi ya dinga bani abincin nan har na koshi. Daga nan kuma muhawara muka hau tafkawa akan gida zan wuce in huta ba wajen aiki ba, da kyar na samu na iya fahimtar dashi lafiyata lau, kuma zan iya zuwa wajen aikina. Sannan fa ya saka ni a gaban mota ya kaini har ward dinmu, bayan dogon bayanin in kular mishi da kaina fa da baby, ya juya ya tafi. Ya barni da su sister Hajara da suke ta sheka mana dariya.

*

Janan tafi minti biyar tana ihu da shewa, har sai dana kai ga kauda wayar daga kunnena kafin ta kai ga kassara min ji na ina zaman lafiya. Sai data gama ihun murnar, sannan kuma ta hau zuba hamdala, "kai Alhamdulillahi, Allah na gode maka! Yau ina zan kai farinciki a cikin rayuwata?! Finally, Allah ya raba mu da bakar kaska, zamu huta dai. Gari ya waye dukan duhu na yayewa!!". Ta karasa maganar da take yi cikin sautin wakar gari ya waye.

Hakan yasa na saki dariyar da ban shirya ba. Na dawo gida daga wajen aiki. Duk da cewa ba yau na saba dawowa na tarar da gidan babu kowa ba, sai dai wannan karon da banbanci. Wannan karon nasan cewa komin dare babu wadda zai dawo, zan ci gaba da kasancewa ni daya, ban sani hakan ko abin murna da farinciki bane a gareni ko kuwa na jajantawa?

Janan itama tayi dariyar, "Malama kada ki fuske mana, nasan ran nan naki yau fari tas kamar likkafani".
Nace "ke fa baki da kirki wani lokacin wallahi, likkafani seriously?".
Ta kwashe da dariya. Ina tunanin yau dai ba za'a samu yin hira mai ma'ana da ita ba, don haka nace mata taje taci gaba da abinda take yi kawai.

Tace "shine don wulakanci ranar nan kika ce wai baki da ciki?".
Nace "waya fada miki ina da ciki ne?".
"Dalla can, an gaya miki zancen duniya yana buya ne? Zancen cikinki ai ya gama zagaye gari da dangi yanzu, har yaron goye yasan da maganar".

Na girgiza kai kawaI, na manta ba'a maganar sirri da Yaya, musamman wadda ta danganci wannan.
Nace "to naji, je ki cigaba da soyawa maigidanki cin-cin, nima abinci zan zo in dafa mishi".

Ina jin tana guna-gunin wai kada in mata gorin miji fa, na kashe wayar kawai ina dariya.

☆⋆50⋆☆
Finale

Watanni goma sha uku kenan bayan haka, na samu kaina tsaye a kofar gidan a can cikin unguwar Tudun Wada cikin Zaria. Gida ne kadaran-kadahan, amma zaka fi saka shi cikin jerin gidajen ya-ku bayi. Gabadaya gine-ginen unguwarma haka take, kwata, bumps, ramuka da bola sunyi yawa a wajen.
Chapter 89 · 0% Book details