← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 95

Sashe 88

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kawai naji gabana ya fara faduwa kamar ana buga ganga, muna tsayawa a kofar falon kuwa naji kaina yana wata irin juyawa kamar zan fadi.
Samuel wanda yake ban ruwan fulawowi da gyaran garden ya bazamo daga bayan gidan hannu rike da tsintsiya, da alamu shara yake ya taho gaisuwar ban gajiya.
Hakan ne ya dakatar damu daga bude kofar falon, muka tsaya suna gaisawa da Yaya. Bayan ya mana sannu da zuwa, ya juya.

Idanuna suka sauka akan matakalar dake manne da kofar wasu irin abubuwa kamar har da danko da lema, babu mamaki wani abu ne ya zuba a wajen. Da sauri na kira sunanshi, ya juyo yana kallona.
Nace mishi "don Allah dan sa tsintsiya ka share wajen nan, kamar yayi datti".
Babu musu ya matso tare da sanya tsintsiya ya fara shara wajen, "to Haji...".

Bai gama rufe baki ba aka turo kofar falon da sauri kamar za'a ballata, Raheemah ta fito a sukwane kamar wata sabuwar kamu tana ihun "kada ka share! Kada ka share!!".

Amma ina! Aikin gama ya gama, tuni ya gama sharewa.

Ta ja tayi turus, muna kallon-kallo. Mu na mamakin abinda ya sanyata yin haka, ita kuma fuska cike da alamun tsoro.
Yaya yace "lafiya?".
Ta kalleshi a dan firgice, kafin ta girgiza kai da sauri, "me? A'ah, babu komi. Dama turaren wuta ne na zuba a wajen".

Yaya ya karya kanshi gefe guda yana kallonta, kafin ya tabe baki, "well, to ina ma amfanin sanya turaren wuta a waje? Muje ko?".

Ya tura kai zuwa cikin falon na bi bayanshi. Strangely, babu wannan faduwar gaban da nayi ta ji dazu. Har Yaya ya gama shigo da kayanmu Raheemah na inda muka barota a tsaye. Sai da na kai akwatina daki na dawo daukar jaka sannan na ga ta shigo falon jiki a sanyaye.
A dan lokutan da muka yi bamu hadu ba, babu abinda ya canza daga jikinta. Ta sha kwalliyarta cikin wani tsadadden paper Swiss lace, daya daga cikin wanda Yaya ya dinka mana na sallah. Babu laifi kuma, sun matukar karbarta.
Kai tsaye dakinta ta wuce da sauri, kamar zata fadi, ni da Yaya muka bita da kallo cike da mamakin wannan halayya. Wa zai yi zaton irin tarbar da zamu samu kenan a yadda take ta faman dokin mu dawo dinnan?.
Yaya ya taimaka min na gama kai kayana daki, shi dama daga brief case dinshi babu abinda ya riko. Daga nan ya wuce dakinshi, ni kuma na fada bandaki don in watsa ruwa ko na warware gajiyar jikina.

Bayan na fito falo na sake fita. Ina zama, Yaya ya fito daga nashi falon sanye da jallabiya baka. Yadda fatar jikinshi tayi wani kyau, da yadda rigar ta bi jikinshi ta lafe kamar second skin, yasa ban san sanda na saki baki ina kallonshi ba har da karkace kai gefe guda. Yadda sajen fuskarshi ya kwanta mishi sosai...
Ban san ya iso kusa dani ba, sai dana ji iskan daya hura min ya sauka a fuskata, na lumshe ido ina murmushi yayin daya zauna a gefena da yake akan two seat nake.
Yace "wannan kallon fa baby? Na nawa ne kuma?".

Na kyalkyale da dariya ina jingina da jikinshi, "yanzu don na kalleka har sai na wani biya?".
Yace "ehh mana!".
Na daga kai na kalleshi, "halalin nawa?".
Shima ya kalleni, tare da sanya hannu yana dan jan hancina, "zakin baki ne zaki yi mun yanzu?". Na sake yin wata dariyar ina kara kwanciya a jikinshi.

Raheemah ta fito daga dakinta, ba kamar dazu da take a hargitse ba, yanzu ta warware duk da daga gani zaka fahimci cewa murmushin dake kan fuskarta bai kai can ciki ba. Lullube yake da damuwa.
Bakinta washe da murmushi kamar zai tsage biyu, "marhabun lale sannunku da zuwa. Ya hanya? Kun sauka lafiya?".

Bata nuna alamun tado zancen abinda ya faru dazu ba, don haka babu wanda ta tayar mata a cikinmu. Muka ce "lafiya lau".
Tace "abincin ku yana kan dinning, ko nan zan kawo muku?".
Yaya yace "sai na dawo daga masallaci".

Ta kalleni, "ke fa Na'ilah?".
Da fari kallonta nayi cike da mamaki da kuma alamun tambaya, banyi tunanin dani take ba. Da sauri na girgiza mata kai, "a'ah, nima sai anjima".

Ta zauna akan kujera dake gab data Yaya, ta fara tambayarshi abinda ya wakana yayin zuwanmu umrah, nan suka cigaba da hirarsu.
Ni kuwa kallo kawai nake binta dashi, mamakina ya kasa boyuwa. Shi kanshi Yayan nasan ba karamin kokari yayi ba wajen boye nashi. Bansan abinda ya tsirar da wannan sabuwar halayyar tata ba, koma dai menene nasan raina baya gaya min da dadi. Nasan hakan baya rasa nasaba da yadda na saba da halayyarta ta mita da tankawa duk wani abu daya dangance ni.

Ana kiran sallah duk muka mike, Yaya ya wuce masallaci, mu kuma muka wuce dakinmu.
Bayan nayi sallah na kunce tsarabar da nayi, na dauki turaren kaya, na miski da ruwan zam-zam na leka har dakin Raheemah na mika mata. Ta amsa da fara'arta tana godiya. Na jima a kofar dakinta bayan ta amshi kayan ta rufe kofarta ina kallon kofar, kafin na juya na koma dakina.

Abinci ma a tsaitsaye na ci shi saboda cikine a cike yake. Dambun kifi dana nama Anty Sarah ta hado ni dashi cike da wasu manyan plastic rubbers. Shi nake ta ci tunda muka iso abina.
Muna gama cin abincin na musu sallama na wuce dakina, nasan yau dai Raheemah ce take a turaka. Kayan jikina kawai na cire na saka na barci na kwanta. Ina kwanciya kuwa barci ya daukeni, ban tashi ba sai da asubahi da Yaya ya shigo ya tashe ni sallah.

Da wuri na shirya shiga asibiti. Jakata dam da kananun turaruka da robobin zam-zam na tsaraba. Ina kan dinning ina hada ruwan shayi, Yaya da Raheemah suka fito. Hannunta daya rike da jakar shi ta wajen aiki, dayan kuma ya sarkafo daya hannunshi. Na kauda kaina gefe ina kokarin danne wani abu mai daci da yake kokarin taso min. Idan nace bana jin irin haka a duk lokacin da naga wata daga cikin matan Yaya tayi kusanci dashi, kamar haka, kai koda bai kai haka ba, to nayi karya. Ina ji, sai dai karfin zuciya da tsananin iya danne zuciyar tawa ne yasa nake iya kauda kaina gefe guda.

Nan suka ja kujera suka zauna. Bayan mun gaisa, Ameerah ta zubawa Yaya nashi abincin. Ni kam ina gama ci, na dauki jakata na musu sai anjima. Sai dai tun kafin in kai ga tashi tsaye Yaya ya tsayar dani. Yace "bari in gama sai in sauke ki".
Ban ce komi ba, na koma na zauna. Again, nayi zaton zata yi magana ko wani abu, nan ma ta bani mamaki da naji tayi shiru. Bai ma dauki wani lokaci ba ya gama cin abincin, nan muka mike muka fita.

A asibiti bayan na gama gaisawa da duk wasu wadanda muke gaisuwar mutunci, ganin babu aiki sosai yau a ward din yasa na yiwa ofishin Dr. Anita tsinke. Bayan mun gaisa da ita a mutunce kuma cike da girmamawa, na yi mata bayanin duk wasu signs da nake gani a jikina. Bayan tayi min wasu tambayoyi da kuma gwaje-gwaje, ciki sati biyar ya bayyana.

Ba karamin mamakinta ta nuna ba, cikin jijjiga kai tace "Allah kenan! Wannan abin mamaki da me yayi kama? A yanayin yadda kike dinnan, ban taba zaton zaki iya daukar ciki a cikin shekaru biyu masu zuwa ba wallahi. Kai congratulations!".

Nayi murmushi ina jina kamar ina yawo a sararin samaniya. Duk da cewa nayi zargin haka, amma na kasa yarda da abinda naji yanzu gaskiya ne.
Tace "sai dai you'll have to be extra careful gaskiya, saboda cikin jikinki yana bukatar kulawa da takatsantsan. Kin fahimce ni?".
Na gyada mata kai. Nan ta zauna ta kafa min dokoki, irin ayyukan daya kamata in dinga yi, da wadanda yakamata in guda, irin abubuwan daya kamata in dinga ci, da dai sauransu. Nan na mata sallama na wuce pharmacy na sayi magungunan data rubuta min. Throughout jin jikina nake kamar ba nawa ba. Da an dan motsa kadan, sai in kai hannuna saman cikina ina shafawa.
Lokacin tashi yana yi, na koma gida.

Bayan na ci abinci na cire uniform dina, na zauna a gefen gado ina tunanin ta yadda zan sanarwa da Yaya maganar wannan cikin. A haka har barci ya dauke ni, sai wajen karfe hudu na tashi.
Nayi sallah na fita waje don samawa cikina abinda zan ci. Babu kowa a falon, sai dai daga jin sautin muryoyin dake fitowa daga dakin Raheemah, nasan baki tayi.
Na bude fridge na ciro fresh fruits da yoghurt na koma dakina. Har Yaya ya dawo ban fita ba.

*

Fiye da kwana uku kenan, amma na rasa ta yadda zan isar da sakon cikinnan wajen Yaya, na kuma rasa dalilin da yasa na kasa din.

Safiyar ranar juma'ah, na gama shirin tafiya wajen aiki. Na fita falo da dan saurina ganin cewa naso in makara yau.
Yaya na zaune akan kujera yana latsa wayarshi, babu alamun Raheemah wadda take yin girki yau, babu alamun kayan kari.
Na dan yi turus, kafin na karasa kusa da Yaya na zauna tare da gaida shi.
Ya amsa yana bina da kallo, nasan yadda na murmure da wata irin kiba dana fara yi ne yake kallo yana mamaki. Bai kai ga amsawa ba Raheemah ta fado wajen kamar an jefota. Tun kayan barcin jiya ne a jikinta bata cire ba. Kanta babu dankwali, gashin kanta ya cure waje guda.

Taje gaban Yaya tayi tsaye har da kama kugu, duk muka bita da kallon mamaki.
Cike da tsiwa da alamun dibar albarka tace "Bilal!".

Ba Yaya kadai ba, ni kaina sai dana bude baki na bita da kallon mamaki. Bana tunanin ko Ummanmu tana ambatar sunanshi haka balle ayi maganar Yayye ko kannenshi, ayi zancen matar aurenshi. Nasan kila dai abokanshi na kiranshi haka.

Ya kalleta a dage, "lafiya?".

"Lafiyar kenan, lafiya ce ta kawo haka. Sakina zaka yi!". Ta furta hakan cikin saurin murya da mazarin jiki kamar wadda take shaking.
Chapter 88 · 0% Book details