← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakina mai fadi ne, an sanya Italian bed, closet ta jikin bango, dressing mirror da shelves na littafai. Fentin dakin light orange ne, sai daga bangon gado da aka sanya wasu irin wallpapers masu tsananin kyau. Daga can gefe akwai study table da aka shirya, da dan karamin firjin a gefe, can gefe kuma nan ne bathroom yake. An zuba duk wasu abubuwan bukata a ciki. Sauran dakunan ma duk haka suke, hatta da kayan ma duk iri daya ne, kala ce kawai ta banbanta. Na sake bin dakin da kallo ina jinjina kai cikin jinjina namijin kokarin da Yaya yayi. Daga karshe dai na shiga bandaki na dauro alwala, ina fitowa na tadda abin sallah a shimfide yana facing din alkibla, don haka na hau kai na tada kabbarar sallah. Ban tashi daga kai ba sai dana yi sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan.

Kayana da aka taho min dasu na samesu a tsakiyar daki, na fara daga su ina fiddo su daga cikin akwatunan. Cikina ihun yunwa yake yi tun karfinshi, tunda yau na fita daga girki nasan bani da halin cewa zan shiga kicin in dora abinda zan ci. Nayi tunanin fita domin in ga abinda aka girka, daga baya dai kawai naga bari in dakata in gani ko za'a kira ni. Na daga fridge din dakin naga babu komi a ciki sai ruwa, shima babu sanyi saboda firjin din ba a kunne yake ba. Naja tsaki na maida firjin din na rufe. Na koma naci gaba da daddaga kayan.

Ina cikin fito da kayan Janan ta kirani, ni sai lokacin ma na tuna babu wanda na kira, na daga wayar cikin dariya saboda nasan korafi ta kira ta min. Illa kuwa, ina dagawa ta fara, "haba baiwar Allah, dokin sabon gida har yasa kin fara mantawa da mutane ne?".

Nayi dariya nace "don mantuwa kam na manta dake, sai dai ba santin gida bane yasa na manta dake wallahi, gajiya ce da yunwa, gashi tunda muka sauka bamu zauna bane shi yasa".

Tace "to sannunku. Nima tun dazu naji Yaya yana fadawa Ummah kun isa lafiya, shine na zauna ina jiran a kirani sai kuma naji shiru, shine na biyo baya. Kun sauka lafiya?".

Nace "lafiya lau, ya su Ummah?".
Tace "lafiya. Ya gidan naku?".

Nan na mike kafa na fara labarta mata labari, har sai data fara cewa in dan saurara sannan na dakata ina dariya, "Allah don baki ga gidan bane Jan, ya hadu fiye da tunaninki. Bana tunanin duk shige-shigenki kin taba shiga gidan daya kai wannan wallahi".

Tace "ai in Allah ya yarda zamu zo ganin gida ni dasu Yaya kila satin sama, tunda Yaya ya gama ginin kusan shekara nawa yanzu, babu wanda ya taba zuwa sai dai su Yaya Auwal da naji suna fadin haduwar gidan".

Nace "haba? Dama ba'a taba zama a gidan nan ba?".

Tace "wa zai zauna? Shi kadai yake zaune a gidanshi. Anty Ameerah dama bata taba zama a gidan ba saboda lokacin da aka yi aurensu tana karatu, kuma yana cikin yin ginin ne, bayan ya gama kuwa taki komawa. Ita kuma Anty Raheemah dama bai taba cewa zai kawota nan ba, don't know why though!".

Na jinjina kai, "lallai yayi kokari ba kadan ba. Zama a gidannan kai kadai duk girma da fadinshi?".
Tace "to yanzu ba gaku nan ba? Dagewa zaki yi ki fara sauke mana yan digwi-digwi yadda zaki ga gidan ya cika nan da dan lokaci, sai ku daina ganin girmanshi".

Wani abu ya dan ratsa zuciya da tace haka, amma sai na dake, na saki wata sarkakkiyar dariya nace "ke fa baki da kunya wani lokacin Jan, duka-duka yaushe aka yi auren?".

Tace "tunda aka yi sati kuwa, ai lokaci yayi babe, yakamata zuwa yanzu ace koma menene ya gama shiga. Kin fara jin canje-canje a jikinki kuwa?".

Na sake fashewa da dariya, wani lokacin haka take kamar wata sintacciya. Ina shirin bata amsa, naji alamun shigowar kira, na duba naga 'Zhaujee', kamar yadda ya kawo min wayar da wannan sunan a jikin lambarshi yana tsalle, nace "you are nuts wallahi. Bari in dauki wayar Yaya ya kira, ki gaida su Ummah".

Ban jira ta gama fadin abinda ta dauko fada ba, na katse kiran tare da amsa na Yaya. Ina dagawa yace "ke da waye ne kuke yin waya tun dazu?".

Nace "Janan ce Yaya".
Yace "ok, ki fito mu ci abinci".
Nace "to". Na kashe wayar na tashi.
Wani tattausan silifas pink, na dauka a cikin kayana na saka. Na dauki turare na kara fesawa a jikina, na dauki wayar hannuna naja dakin na fita.

Suna zaune akan dinning table, da kwanukan abinci a gabansu na same su. Na musu sallama suka amsa, tare da jan kujera kusa da Yaya na zauna, ita kuma Raheemah tana kan wadda take fuskantar shi. Fuskar nan tasha make up har da na hauka.

Yaya yace mana "bismillah ko?".

Na ga Raheemah ta ja plate ta bude ta zuba abinci a ciki macaroni ne aka yi jallop, an zuba kifi da nama a ciki. Maimakon in ga ta mikawa Yaya wanda ta zuba, sai naga ta ja shi gabanta zata fara ci.
Na kalli Yaya naga yana fama da cokali da plate, sai na dan matsa, na karbi plate din hannunshi na zuba mishi abincin, na tsiyaya ruwa a cikin cup shima na ajiye mishi, sannan na fara zuba nawa nima. Ya kalleni cikin dan murmushi, tare da furta "jazakillah", a can kasan makoshinsa. Na maida mishi martanin murmushin.
Ina daga kaina, naci karo da idanun Raheemah tana watso min harara, ni kuwa na daga kafadata sama na fara cin abincin bayan nayi bismillah.

Ban wani ci da yawa ba, na ture kwanon gefe na ajiye. Ban taba cin girkin Raheemah ba tunda nake, don haka ban taba sanin yadda girkinta yake ba sai yau. Kodayake, zata iya yiwuwa yau din rana ce ta kufce mata abincinta yayi gishiri da yaji ya kuma dafe.

Na ci gaba da zama anan duk da cewa na gama, har suka gama cin nasu abincin. Yaya ya tashi ya wuce dakinshi, itama ta mike tayi nata dakin, ta bar kayan abincin anan, suka barni ina zare ido.
Da nima nawa dakin zan koma, sai na jiyo sautin karar talabijin a falon Yaya, don haka na karasa can. Baya cikin falon ma, na zauna tare da daukar remote na latso tashar mbc action na kunna, suna hasko film din Furious 7 kuwa, na gyara zama sosai don ina kaunar film din kwarai.

Ban yi nisa a kallon ba, sai ga Raheemah itama ta shigo. Tana zama, ta dauki remote ta canza tasha, na dan daga kai na kalleta kadan, sai kuma na dauke na maida kan tvn da take ta latse-latse da canza tasoshi. Idan tayi zaton magana zan mata akan haka, zata sha mamaki kam. Daga karshe ma sai na kunna wayata na bude wani document akan pregnancy issues ina dubawa.

Muka cigaba da zama a haka, babu mai ko tari sai sautin wakoki dake fita daga wata tasha data kunna. A haka Yaya Bilal ya fito ya same mu.

Ya umarceta data kashe kallon, yana so yayi magana damu. Nima sai na kashe wayata, na maida hankalina kan shi.

Yayi gyaran murya, ya fara da kara yi mana nasiha da kuma dokoki daya kafa. Yace babu yan aiki a gidanshi, daga maigadi, sai mai ban ruwan fulawa, sai kuwa wata mace da yace zata dinga zuwa tana tayamu da share-share da wanke-wanke, amma bai yarda da girkin yan aiki a gidanshi ba, mun fahimta? Muka ce mishi eh.
Sai kuwa zancen girki, ya tambayemu kwana nawa muke ganin zasu fi zama convenient a wajenmu? Ni dai nayi shiru ina jin suna muhawarar kwana daya ko biyu shi da Raheemag, har sai daya jiyo ya kalleni, Ya tambayeni ya nake gani? Nace ni duk yadda suka yanke daidai ne a wajena. Nan ma na kara karbar wata hararar dai, na nuna kamar ban gani ba. Daga karshe dai suka kare akan kwana biyu.
Yace tunda ita Ameerah bata da ranar dawowa, zamu cigaba da raba girkin a tsakaninmu har zuwa lokacin da zata dawo. Ya kara da cewa bai yarda da fada ba a gidanshi, babu fada kuma babu cece-kuce, yace duk wadda take da matsala game da wani abu, mu tunkari junanmu mu warwareta a tsakaninmu, ko kuma mu fada mishi, sai yasan yadda zai warware matsalar, muka ce to.

Daga nan muka cigaba da kallonmu har dare yayi, sannan na tashi na musu sallama na wuce dakina.
Kayan da ban gama gyarawa ba, na gyara. Na ciro kayan barci na ajiye akan gado, sannan na shiga wanka. Wanka nayi, na wanke bakina da mouth wash mai kamshin berries, na daura alwala na fita.

Yaya Bilal yana bakin gadona a zaune da wayata a hannunshi yana dannawa, ya daga kai ya kalleni lokacin dana fito. Har naja kujerar da aka ajiye a gaban dresser na zauna, idanunshi suna kaina.
Na kauda kaina kamar ban san yana yi ba, na dauki lotion na fara shafawa a jikina. Ta cikin mirror na sake tsintar idanunshi a kaina, wayar ma ya ajiyeta a gefe guda, ya karkato da hankalinshi kaina kacokam. Naji gabadaya na fara takura da kallon kurillar da yake yi min, a gaggauce na karasa shafa man, na mike tsaye da niyar dauko kayan barcina dana ajiye.
Babban tawul ne a jikina wanda ya sauka har kasan gwiwata, na karasa gaban gadon na janyo kayan, ganin har lokacin yana zaune yana kallona yasa na juya na koma bandaki na sanya kayan.

Wannan karon dana dawo, yana tsaye a bakin gadon, hannuwana saye cikin aljihun sweat pant dake jikinshi, idanunshi kyam akan kofar bandakin yana dan murmushi.

Yace "meye na wani guduwa bandaki kuma? Menene ake boye min ne, wanda ban riga na gani ba?".

Na kalleshi blankly kawai ban ce komi ba, na wuce kan gado kawai na ja bargo na rufa.
Ya matso ya janye bargon daga fuskata, "uh uh!! Shariyar menene ake min haka, baby na kamar baki gane ni ba?".
Chapter 65 · 0% Book details