← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 95

Sashe 59

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan dakin da aka jera min ba karamin kyau suka yi ba, babu abinda zan ce da Baba da yan'uwanmu sai dai fatan gamawa da duniya lafiya.
Bayan mun gama hutawa, munyi sallah, Janan dasu Harira suka daukemu zuwa tour din gidan. Dakuna hudu ne da babban falo, sai kicin da main toilet, sauran dakunan ma duk suna da nasu bandakunan, inda biyu daga cikin dakunan aka shake su da jeren kayana. Gado, mirror, closet, da dai sauran tarkacen kayan daki. Haka ma falon, ya sha saitin kujeru masu kyau, babbar plasma, dinning table, har da wajen hutawa daga can gefe. Aka shimfida tattausan rug carpet, aka watsa tuntuna da sofa kwara daya jal, sai katoton vase na fulawa.
Kicin kuwa ba'a ma yin magana, duk wasu kaya da ake bukata a cikin kicin an zuba min su, dangin su electronics da sauran kaya na nunawa sa'a. Ban taba tunanin haka gidan aurena zai kasance ba, a yadda Baba yake, nayi tunanin kila gado ma sai an kai ruwa rana zai sai min, dana gayawa Anty Halima haka dariya tayi ta min, wai bani da saiti.

Komi na gida dai yayi Alhamdulillah, sai godiyar Allah kawai. Daga nan kuma suka ja ni zuwa daya dakin na kusa da nawa, shi babu komi a ciki sai tattausan carpet da aka shimfida, katifa, da desktop table da kofofi. Daga gani babu tambaya nan ne dakin maigida Bilal. Nan suka nuna min akwatunan da aka kawo min, Janan tace "Yaya Sa'a ce zai fi a barsu anan kawai, in kin zo kiga kayanki tunda idan ma an kaisu can din hidimar kai da kawowa ce za'a sha". Na gyada mata kai cikin nuna fahimta.

Akwatuna ne irin na zallar leather dinnan, maroon, dai-daya har guda goma, kowanne shake da kaya. Tun daga na sawa, atamfa ce, laces, materials, yadika masu kyau da armashi, you name it. Kayan kwalliya kuwa kamar za'a bude shago. Harira da suke bude kayan, ta kalleni tana murmushin tsokana, "sai fa kin dage, mijinki mai dan banzan son kwalliya ne, ke kuwa naga alamu kwalliyar ba'a kanki ma take ba, kamar sauran taron matan can nashi daya ajiye dai. Idan kina so kiyi zarra, sai kin koyi amfani da kayan kwalliyar nan".

Nace mata "to waye yace miki so nake inyi zarra a gidannan?".
Tace "duh, lokacin da zaki fara shirin yin zarrar waya sani? Kawai ina baki head-ups ne idan lokacin yazo". Duk suka kwashe da dariya, ni kuma na bisu da harara.

Suka ci gaba da bude akwatunan, dangin jakunkuna, takalma tun daga vincci, gucci, chanels, LV, babu wanda babu. Turaruka, gyale, hijabai, babu abinda babu. Kada ma fannin fashion ear rings da sarkoki su ji labari. Kayan yawansu har yayi yawa, I was very overwhelmed. Yayin da masu ba idanu abinci suke ta zubo addu'o'i, idanuna cike suke taf da kwalla da hawaye, sai fakar idanu nayi na goge su.

Daga nan muka koma dakina, wasu kuma suka tsaya a falo. Aka fara shigo da tarin abinci kala-kala, muka zauna muka ci. Zuwa lokacin da muka gama cin abincin, aka fita da kwanukan abincin, karfe hudu tayi. Lokacin yawancin wadanda suka zo duk sun tafi, ya rage daga ni sai su Janan kawai dasu Maryam da zasu koma Katsina gobe.

Anty Halima ta sanya ni nayi wanka, na sanya riga da zani na atamfa, ruwan goro mai zanen manyan furanni, aka dora min babban gyale a kaina, na saka takalmi flat, muka tafi sashen Raheemah, a cewarsu kai amanar amarya.

Suna zaune a falonta ita da gang dinta, har ma da uwarsu. Taci daurin dankwalinta irin wanda ta saba yi na yan duniya, 'ya'ya sun zagayeta ana ta hira da shewa babu ko kunya.
Muka yi sallama muka shiga falon. Suka yi tsit, kamar ba su bane masu neman tada falon da hayaniya ba.
Babu wanda yayi mana masauku, suka nemi kujera suka zauna, ni kuma aka zaunar dani a kasan carpet. Kaina yana kasa cikin gyalena, naji su Anty Halima suna gaidasu. Babu wanda ya amsa, sai sautin "hummm" da "uhummmm" daya dinga tashi.

Basu daddara ba dai, Anty Halima tace musu "ga amanar diyarmu mun kawo muku, muna fata za'a rike mana ita cikin aminci da amana".

Sai da suka shaki iska, sannan naji muryar Adi, "to ku kunji fa, maciya amanan wai sun kawo muku amana".
Salame ta cafe, "Kaji ma wani rainin wayau fa anan wajen, Momcy. Sai da suka gama shuke-shuken munafurcinsu da kitsa rashin mutunci sannan wai suke kawo amana. Amanar me kuma? Ko roki a maida muku yar ku yadda kuka kawo ta mana, in one piece!".
Momcyn tasu kuma ta kara da, "ku ne ma kuka zauna wani yi musu karin bayani. Ku bari idanunsu su gane musu mana, kishi da ahalin gidanmu ba karamin aiki bane, kuma duk wanda yace zai ja da gidan iko, to ba jikinshi kadai ba, na uwatai ma da ubanai sai sunji labari!". Suka kuwa kwashi ihu har da sowa jin abinda tace.

Ganin abin yana wuce gona da iri, Anty Halima tace "to Allah ya baku hakuri, Allah ya gani mun sauke hakkin dake kanmu. Ku tashi mu tafi".

Sai lokacin Raheemar ta sanya baki, ta tashi tsaye tana wani jijjiga jiki, "hakkin banza dana wofi! Ku har wani hakki kuka sani? Wato dama munafurcin zuwa nan gidan da take yi, tsaface-tsaface take zuwa tana binne mana a gida. Sai da tayi yadda tayi ta tsaface min miji. To wallahi bari kuji, karyarku ta sha karya. Idan kuna cin kasa ku kiyayi ta shuri. An shigo gidan kudi ana ta bude daddaudan baki da ya sha miyar kuka, ana murna an auri mai kudi. To murnar ku zata koma ciki, gwanda ma tun kafin a maida muku diyarku a nakasce, ku dauketa cikin salama ku maidata inda ta fito, idan kuma ba haka ba... tammm!!".

Anty Halima tace "a'uzubillahi, mai kike fada ne haka? Allah ya tsaremuda aikata wannan danyen aiki. Mu ahalinmu babu masu aikata wannan danyen aiki, bamu taba ba, kuma ba zamu taba ba in Allah ya yarda".
Nan fa suka yo mana caaa! Da ihu kamar zasu cinyemu danyu. Nan dai muka samu muka bar musu falon, muka barsu suna barazanar sai sun koya mana hankali gabadayanmu.

Muna fita Anty Halima ta kama baki, tace "ikon Allah, Allah sarki mai halitta. Mutane ku sanya kanku cikin uku babu gaira babu dalili? Yanzu banda duniya ta zama abinda ta zama, me zai sako uwa cikin lamarin auren diyanta, har ka ganta ta taka kafa taje gidan surukai tayi dororo?".

Janan tace "Ai baki ga komi ba Anty Halima, idan har kina tare da mutanen nan, babu abinda zai dinga baki mamaki kuwa".
Hauwa tace "aikuwa dai Girma ya Fadi wallahi, ba'a ji dadin rayuwa ba. Ai in an girma sai asan an girma, a barwa yara yarinta".

Daga nan muka shiga wajen Anty Sarah. Nan kam tarba muka samu ta mutunci, aka gaisa a mutunce, aka bada amana suka karba, daga nan muka koma sashen na.

Muna shiga na yaye gyalen kaina na haye can kuryar gado na lafe. Abinda ya faru a sashen Raheemah, ta tabbatar min daga cewa lallai sai na kara daure damara a cikin wannan gidan. Ina cikin wannan sake-sake su Janan suka shigo, dole na mike zaune muka kafa sansanin hira dasu.

Da dare ina daki na jiyo shigowar Yaya Bilal nan sashen, ina ji suna gaisawa dasu Anty Halima da suke falo suna hira. Na zauna a gefen gado sosai, ina jiran ya shigo ciki inji da kalar wadda yazo. Ba'a jima ba na ji hayaniyar gaisuwar ta ragu, sai hirarsu da suka cigaba da yi da kuma karar tv, wato fita yayi babu ko leke? Na kuta tare da komawa na kwanta abina.

Ba'a jima ba suka leko, wasu suka mana sai da safe suka koma daya dakin suka kwanta, wasun kuma kamar su Janan, suka kwanta tare dani anan dakin.

#F.W.A

*☆⋆35⋆☆*

Washegari muka karya da abinci mai rai da lafiya wanda aka kawo daga gidan Anty Sarah. Bayan mun ci munyi nak, muka yi wanka muka shirya.
Ina gaban mirror ina shafa man lebe a bakina, Maryam ta leko kanta dakin, "Yaya Na'ilah motar da zata maida mu tazo".
Na kalli agogo naga karfe goma, naji jikina yayi sanyi sosai. A sanyayen nace "tun yanzu? Nayi zaton zaku kai ko gobene".
Tace "haba, daga kawo amarya kuma? Mu daya kamata mu kauce tun jiya, mu ba ango damar cin amarcin sa?".

Na mike tsaye ina harararta, "yarinyar nan kin baci da yawa wallahi, baki da kunya yanzu".
Tayi dariya tare da maida murfin kofar ta fita bayan tace "kiyi sauri ki fito ke dai muyi sallama".

Na saka kaya a gaggauce na fita falon, ganin Anty Halima da kaya a gaba nayi turus, nace "kema yau zaki tafi?".
Tace "ehh mana, ko zaman daki kike so in zauna in miki?", duk suka kwashe da dariya.

Nayi narai-narai da ido kamar zanyi kuka, nace "yanzu ba zaku dan kara kwana bane?".

Huleirah tace "nop, not happening. Gwanda mu tafi tun ana ganin girma da mutumcinmu. Ko kuwa so kike angon ya kai ga korar mu ne?".
Na jefa mata harara, "dallah can yi mana shiru, waye ya sako bakinki anan?". Suka sake kwashewa da dariya.

Na shiga inda akwatuna suke, na cicciro kaya na fita na kai mika musu, Anty Halima tayi kir tace babu abinda zata amsa, "ce miki aka yi kyauta ake yi da kayan lefe ne? Mijinki kawo miki yayi don ki mishi kwalliya dasu ba wani abu ba".
Nace "to ai sanya albarkarku ne nake nema, don Allah ki amsa Anty".
Da kyar ta amsa, sannan suma su Maryam suka amshi tarkacen kayan kwalliyar dana basu, suna zuba godiya da sanya albarka.

Da yake a hannuna akwai kudin da Janan ta bani tace Yaya yace inyi hidimar biki dasu bayan an daura aure, babu abinda nayi dasu ma sai jikin jaka dana saka su. Na dauko na basu dubu dai-daya, Anty Halima kuma na bata biyar.

Tace "a'ah, har da kari? Kai Allah dai ya sanya albarka. Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki da zuriya dayyiba".
Chapter 59 · 0% Book details