← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 95

Sashe 70

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

A takaice sai bayan la'asar sannan muka ci abincin rana yau. A falon shi na shimfida mana ledar cin abinci, muka zauna. Yaya yafi son cin abinci a kasa, sannan cin abincinshi yafi son su ci tare da wani ko kuma matar shi, saboda haka yanzu abincin safe kadai muke ci a kan dinning. Na dare tun kafin ya dawo daga wajen aiki nake kaiwa falonshi in shirya mishi, muci kayanmu. Ita kuma sai in shirya mata nata akan dinning din.

Bayan mun gama cin abincin, hana ni motsawa ko nan da can yayi. Muna nan har aka kira sallar magriba, sannan ya tafi masallaci. Sai lokacin na dauke kayan abincin na kai kicin. Akwai yar aiki da take zuwa kullum ta mana sharar falo, wanke-wanke da kuma goge-goge, tana dai yin sharar ranar girkina, amma sauran ni nake yin komi da kaina. Musamman ma gyaran dakin Yaya Bilal da falonshi. Ranar girkin Raheemah ma Yaya da kanshi ya umarceni akan in dinga gyara mishi, tunda ita ta gwammace ta mike kafa dai-daya akan kujera tana murza channels, ko kuma ta shura takalmi ta bar gidan yawon gidan makota, akan ta zauna ta gyara dakin mijinta. Ni kuwa ban nuna kyashi ko jin haushina ba, na cigaba da gyara mishi daki.

Dakinshi na koma nayi sallah, ina karatun Al-Kur'ani har aka kira isha'i nayi.
Yau Yaya bai shigo da wuri ba, sai wajen karfe tara ya dawo. Muna babban falo daga ni har Raheemah muna kallo, ko in ce tana kallo, ni a zaune kawai nake.
Ya dawo da ledoji a hannunshi, na tashi na tarbo shi. Dama yace kada in damu da yin girki yau. Na bude ledar naga tsire ne da balangu, yoghurt da roll cakes.

Na ajiye su anan, na shiga kicin na dauko plates nazo na zuba mana. Da ya cewa Raheemah ta sauko, sai ta turo baki gaba, cikin alamun mita tace "uhmmmm! Da yake ita yar gaban goshi ce, dama mana. Yanzu ni har na isa in ce ba zan yi girki ba, ka siyo abinda zamu ci ba tare da ka bata min rai ba?".

Na girgiza kai a hankali cike da takaicin matar. Aikin kenan fa kullum, sam bata da godiyar Allah. Baka taba yin wani abin arziki ba tare data gwasale ka ba, musamman Yaya. Yana iyaka bakin kokarinshi wajen ganin yayi adalci a tsakaninmu, amma bata taba gani ba. Yadda duk karshen wata yake bani dubu ashirin saboda hidimar zuwa da dawowa, musamman cin abinci a asibiti duk da na ce mishi bana bukatar su, amma ya ki, haka yake daukar ashirin dinnan ya bata, maimakon godiya sai ce mishi tayi, "wai ita yanzu shikenan sai ta albarkaci na zata dinga cin kudin hannunshi?", abin ya bani haushi ya kuma bani mamaki kwarai.

Yaya ya daga baki zai amsa ta, nayi saurin tarar numfashinshi, nace "anan zaka ci ne ko kuma zaka koma karamin falo?".
Yaya ya kalleni sosai, nima na kara kallonshi, da alama ya fahimci dalilina na tarar numfashinshi, yace "mu koma falona".
Nayi murmushi tare da kanne mishi ido daya, wanda yasa ya saki murmushin shima tare da mikewa tsaye. Na dauki plate din dana zuba mana namu a ciki,na wuce na kai falonshi, na dawo da niyar daukar yoghurt da cake din.

Tana tsaye a gaban Yayan kamar wadda take tsare shi daga shiga falon nashi, ihu take tun karfinta, wai ya maidata mahaukaciya, tana magana ya dinga shareta.
Yace "wai ke me yasa ba kya son zaman lafiya ne ko kadan Raheemah? Me ma aka yi daya janyo fada da daga murya anan?".
Tace "dama yaushe zaka gani tunda an rufe maka ido? Ni da ake wa rashin adalci ni nake gani, kuma wallahi ba zan yarda ba!".
Yace "sai ki dauki mataki...", ya zagayeta ya wuce. Nima na kwashe sauran kayan na bi bayanshi.

Falon shi kamar nan ne wajen shakatawarmu da hutawa, Raheemah bata cika shiga ba musamman ma ranar da ba girkinta bane, ni kuma ina kokarin kaucewa wajen ranar girkinta saboda shiga hakkinta. Ranar girkina kam acan nake yini musamman idan Yaya yana gida, mu yi ta hirarmu, ko wasanninmu, watarana kuma sai dai mu kwanta kawai, watarana kuma idan yana aiki in barshi yayi aikinshi ni kuma inyi busying kaina da wasu abubuwan.

Yanzu tashar CNN ya kunna yana kallo, ina gefenshi muna cin naman a hankali, lokaci zuwa lokaci zamu dan tattauna akan wani case da zamu ji an fada a tashar ko kuma wani abu. Har muka gama ci, na dauke kayan. Na dawo falon, nayi matashin kai da cinyarshi har dare yayi, ya kashe kayan kallon muka wuce dakinshi.

~~~

Da kyar ya bari muka yi sallama dashi wahsegari na tafi Kaduna. Da kasa ya kekashe akan cewa sai dai in bari mu tafi dashi ranar juma'ah, kamar zan mishi kuka haka na dinga rokonshi ina magiya, nace "idan ma na zauna me zan maka ne Yaya? Ba fa ni zanyi girki ba yau".
Da kyar dai, muka yi sallama ya tafi wajen aiki. Wajen karfe goma sha daya, muka bar garin Abuja.

Tuni gidan biki ya fara cika da yan biki. Gida ya cika ya tumbatsa Masha Allah. Bayan mun gaggaisa da mutane, wasu yan uwan nasu ba da basa cikin kasar ko kusa da gari, sai yanzu muka samu muka gaisa dasu.
Muka lume can kuryar dakin Yaya ni da amarya Janan muna hirar yaushe gamo. Tayi ta min shakiyanci, wai nayi fresh, meye sirrin, ko har an bani ajiya ne?.

Na kuwa danna mata harara, "wai don Allah meye matsalar ki ne? Kullum kiyi ta lakaba min abinda bani da?".

Ta kuwa kwashe da dariya, "to Malama, alamu ne suka nuna haka ba wani abu ba. Ki duba fa yadda kika wani ciko tubarkallah, kin kuma yi haske da abubuwa, idan ba ciki bane to menene?".

Na kada mata idanu, "kiwon Yayanki ne kawai!".
Ta saki ihun dariya, abinda ya janyo su Harira dake falo kenan suma suka fado, suka cigaba da shakiyancinsu. Dana gaji sai na janyo wayata, na dannawa Yaya kira na koma can gefe muka kwashi hirarmu ta masoya.

Washegari aka yi kamu anan cikin gidan. An dauko masu decoration da masu raba abinci, abokanmu da yawa sun zo, haka dangin ta dana Almu sunyi kara ba kadan ba. Gida ya dauki jama'a sosai. Har karfe goma na dare ranar muna kan kafafunmu a tsaye muna kokarin gyara gidan.

A dakin su muka yi parking, baki duk an kaisu dakunan dake cikin gidan, wasu kuma suna dakin Yaya da Ummah.
Ummah ta kawo mana damammiyar fura da kanta, da tasha nono ga sanyi sosai. Tun bayan aurenmu da Yaya, kamar an kara mata kaunata haka nake gani, tunda nazo take ta nan-nan dani, abincin da zan ci ma daga dakinta ake kawo min. Sai naji nima kimarta da mutuncinta sun karu a cikin idanuna.

Bayan munyi wanka don mu dan warware gajiya, muka sha furar data kawo mana, sannan fa kowa ya nemi makwanci. Lokacin karfe sha daya ta wuce. Naso in kira Yaya kafin in kwanta, tun da safe da muka yi waya dashi bamu kara yi ba, amma sanin suna tare da Raheemah yanzu yasa na daure zuciyata. Sai na rubuta sako mai cike da kalamun nuna kewa da kauna, na tura mishi. Cikin sakanni talatin da shigar sakon wayarshi, ya dawo min da amsa.

Nan muka kwashe kusan mintuna arba'in muna musayar kalaman soyayya, kafin muka yi sallama dashi.

Washegari aka yi mothers eve, sai ranar Anty Ameerah tazo. Anty Sarah ita tun jiya tazo, sai dai bata kwana a gidan ba, gidan Yayarta dake aure anan cikin Kaduna taje ta kwana.
Ana gama taro Anty Ameerah ta koma Zaria.

Sai ranar juma'ah Yaya yazo shi da Raheemah. Tunda suka zo bata ma zauna a gidan ba, ranar walima muka yi. Yau ma kamar jiya, ana tashi wajen karfe shida Anty Ameerah ta wuce, ita kuwa Raheemah da tunda suka zo kayanta ma a dakin Yaya ta ajiyesu, ta wuce can. Bata shiga cikinmu ba mu kawayen amarya, muma kuma bamu nemeta ba.

Washegari aka daura aure, muka kai amarya gidan aurenta dake can unguwar rimi. Gini ne na kin karawa, idan ka shiga kamar kada ka fita saboda haduwarshi.
Yanmatan sun ce babu inda zasu tafi sai anguna sun zo sun sayi baki, duk da da yamma ne aka kaita. Na gama shan dariyata nace bari inyi tagging dai nima.

Wajen karfe shida na yamma sai ga kiran wayar Yaya, na fito daga cikin hayaniyar hirar da suke yi, na amsa kiran.
"ki sameni a kofar gida", kawai yace ya kashe wayar.

Na bi wayar da kallo cikin mamaki, kafin na sake kiranshi, nace "muna fa gidan Janan yanzu haka".
Yace "ehh, nan din fa".

Cikin sanyin jiki na koma gidan. Su Anty Sarah da basu jima da zuwa ba, su ganin gida suka zo yi kafin su koma Zaria, ciki har da Anty Ameerah, suna cikin bedroom inda amarya take suna tasu kalar hirar suma.
Na matsa na radawa Janan zan tafi, tace "ina zan tafi yanzu bayan ba'a zo sayen bakin ba?" Nace mata "Yaya yake nema na, yace yana waje".

Ta zaro ido, nayi gaggawar kai mata dukan wasa a hannu kafin tayi tunanin fadin wani abu silly, nace "kada ki wani kawo min wata maganar banza anan, sallama ce kawai zamu yi saboda yau zasu koma Abuja shi da Raheemah".

Amma bata fasa ba, sai data yi commenting din dai. Na dauki jakata kawai na musu sallama akan cewa zan koma can gida, na fita.

Kamar yadda yace kuwa, yana kofar gidan. Na bude murfin motar na shiga, yayi murmushi tare da janyo ni jikinshi, mun dan jima a haka kafin ya dago ni yana kallona, yace "kai baby na, da alama ke ko kewata ma baki yi ba, ji yadda kika yi wani irin kyau kamar ba ke ba?".

Nace "a haka din?".
Yace "sosai ma!". Ya fara kokarin tada motar.
Ban tambayeshi inda zamu je ba, ya fita daga unguwar. Sai gamu a kofar wani gida a can cikin GRA. Na kalleshi cikin mamaki lokacin da naga yayi horn mai gadi ya bude mishi kofar ya shiga.
Chapter 70 · 0% Book details