← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali bikin yana ta matsowa, kwanaki kuma suna wucewa. Na samu da kyar da jibin goshi an barni inje wajen biki inyi kwana hudu, daga can in wuce Katsina in musu kwanaki biyu. Zan dawo Abuja inyi sati biyu ko uku, sai in je Gashua. Duk yadda naso akan ya barni inyi ziyarar gabadaya, ki yayi, dole na hakura musamman da naga yana nema ya rufe ido yace bikin ma na fasa zuwa.

Ranar Laraba zasu fara shagulgulan biki, don haka nayi niyar tafiya ranar talata. Idan aka gama biki assabar, Lahdi in wuce Katsina.

Ranar litinin, ana washegari zan tafi. Ranar babu aiki saboda ranar hutun ma'aikata ce.

Da yake girkina ne yau, bayan mun gama karyawan safe, na koma daki na. Na cire kayan barcin dake jikina, na fada bandaki nayi wanka, bayan na fito na tsaya a gaban mirror na shafa mai, yau ko hodar ban shafa ba sai dan wet lips kawai, na bude wardrobe ina laluben abinda zan sanya.
Daga karshe dai idanuna suka sauka akan wata rigar atamfa, cikin dinkin da Janan ta kai min ne, ban taba sanyata ba sai yau.
Na fiddota tana ta tashin kamshin turaren kayan dana sanya a cikin wardrobe din kafin in shirya kayana.

Rigar doguwa ce, hannuwanta kanana ne da suka tsaya a damtsen hannuna, daga saman kafadar rigar an yi wani irin yanka ta yadda duka fatar wajen take a waje, haka daga bayan rigar ma anyi wani irin show me, rabin bayana a waje yake, daga tsakiyar rigar kuma daga baya, anyi tsaga tun daga kasa har tsakiyar rigar, idan na daga kafa ina tafiya tun daga gwiwata har kafafuna a waje suke.
Ni kaina dana saka rigar sai dana tsaya ina kallon kaina kamar ba ni ba yadda rigar ta fito da duk wata kira ta jikina kamar sai da aka auna ni, abin ya bani mamaki ya kuma kayatar dani.

Na kalli waje ta tagar dakin, naga yadda hadari yake ta kara gangamowa, tunda safe a haka muka tashi. Yanzu garin yayi luf, ya kuma dan yi duhu. Na dan sauke ajiyar zuciya tare da daukar comb na taje gashin kaina, na dauki dankwalin na daura kawai, gashina kuma ya tsaya a tsakiyar bayana yana ta sheki.

Ina cikin fesa turare, da niyar ina gamawa zan wuce dakin Yaya da nasan yana can yana jirana, sai naji an turo kofar dakin.,

"Bab...!"

Maganar daya fara ta tsaya mishi a makoshi. Na juya cikin mamaki na kalleshi, yana tsaye a bakin kofar dakin, baki a dage yana kallona, with admiration.
Na saki murmushi a tausashe, ko bai fada ba, nasan kwalliya ta biya kudin sabulu.

Na danyi juyi a gabanshi kamar wata wadda take fashion parade, na sake juyawa ina kallonshi, "nayi ne?".

Ya girgiza kai kamar yana shaking wani abu daga kan nashi, ya maida kofar ya rufe tare da takowa zuwa inda nake a hankali, ya tsaya a gabana. Hannu yasa ya kamo habata, na daga kai ina kallon idanunshi da suke karewa ilahirin jikina kallo, "Subhanallah! Just Masha Allah, baby na ba zaki gane irin kyawun da kika yi bane wallahi. Fatabarakallahu ahsana khaliqeen!! Dama haka kike, amma shine baki taba yi min irin wannna kwalliyar ba baby!".

Na saki yar dariya, "to yanzu ba gashi ka gani ba?".

Ya sake ni tare da ja da baya yana kara kare min kallo, ni kuwa nayi humoring dinshi ta hanyar sake yin wani juyin, na kara wani. Ina juyowa, tun ma kafin in samu damar daga idanuna in kalleshi, in ga wani hali yake ciki, naji saukar lebenshi akan bakina.

Abin ya daukeni a ban shirya ba, na dan yi sak na yan sakanni kafin na biye mishi na kara kawata abin. Lokaci mai tsayi, kamar ba zai bari ba, kafin ya sakeni a hankali tare da sake dagowa ya kalleni. Hannuwanshi biyu yasa ya tallabo kumatuna, "baby...!", kadai ya iya furtawa cikin wata irin murya dana kasa tantance idan tashi ce, kafin ya sake lalubar bakina. Wannan karon hannunshi yasa cikin gashin kaina yana yamutsawa. Ban tantance ba naji an daga ni sama cimak, anyi kan gado dani.

Wani abu a tattare dashi yau ya banbanta da sauran lokutan da muka kasance tare, bai taba zurfafa wasanninmu irin na yau ba, ban taba jin intense abu irin na yau ba. Haka kawai naji zuciyata ta hau bugu, babu kakkautawa.
Daidai lokacin da naji an saki ruwan sama mai karfi, lokacin na jiyo ana jan wata certain addu'a, kafin in gama tantance ainihin abinda yake faruwa, wani irin zafi da ban taba jin kamar shi ba ya ratsa ni, na dan saki ihu, a lokaci daya yatsun hannuna suna lumewa cikin fatar bayanshi cikin azaba....

.......

(Ehhhemmm!!).

*☆⋆40⋆☆*

Karfe biyu ta gota lokacin dana farka daga barcin daya daukemu. Yaya yana gefena, kaina yana kan hannunshi daya, dayan kuma ya zagayo bayana dashi yadda na shige jikinshi sosai. Yanayin garin yayi sanyi mai dadi sosai, saboda ruwan da aka gama yi.
Nayi dabara na zame a hankali ba tare da nayi motsi mai karfi da zai tashe shi ba.
Zanin sallata dake ajiye a gefen gadon na dauka na daura, na shiga bandaki.
Duk da ciwon da nake ji a jikina, amma ba wani sosai dinnan bane da zai hana ni tafiya. Yaya Bilal was very gentle.
Na hada ruwan wanka, na shiga ciki nayi duk abinda ya kamata. Na dauro alwala na fito Zuwa yanzu kuma normal nake jina, duk gajiya, ciwon jiki da wani zafi ya tafi sai dan kadan wanda zan iya manejin shi.

Har yanzu yana kwance yana shakar barcinshi. Nayi zaton motsina zai tashe shi, amma har na gama dauke kayana da aka watsar dasu can gefen gado, na linke nashi, na dauko wasu kayan na sanya, bai ma san ina yi ba.
Na zauna a gefen gadon, na fara daddabar filon da yayi matashin kai dashi a hankali, ina kiran sunan shi.

A hankali ya fara motsi, ya bude kyawawan idanunshi suka dira a kaina. Murmushi ya saki mai taushi, "baby. meye haka nake gani?".

Nima na saki murmushin, "lokacin sallah ya wuce". Abinda nace mishi kenan, na mike tsaye.
Ya fara kokarin tashi zaune shi kuma, ina ganin haka na juya da sauri kamar zan kifa, na wuce inda na shimfida abin sallah na tada kabbara. Ina jin sautin dariyar daya saki a hankali yana wasu maganganu da kunnena bai jiyo ko menene ba, kafin ya shige bandaki na.

Kafin in gama sallah har ya fita zuwa masallaci.
Ina gamawa na yaye zanin gadon dake kai, na jefa shi cikin washing machine na shimfida wani, sannan na fita da hanzari domin in dora abincin rana. Duk da dai yanzu kowa yana dafa abincinshi na rana ne, na kanyi kokari a ranakun da muka samu hutu ko weekends in hada abincin gidan gabadaya.

Ina fitowa daga dakina, Raheemah ta fito daga nata dakin. Tayi tsaye hannu a kirji tana kallona ina kokarin rufe kofar dakina da mukulli, har na gama na wuce ta gefenta, sannu kawai nace mata wadda ban tsaya naji ta amsa bama na wuce.
Cikin sauri na hau yanke-yanken abubuwa, na fara sanwa.

Ina cikin yin girkin Yaya ya dawo, kai tsaye kicin din ya fado don ta karamar kofa ya shigo kamar yasan a kicin din zai sameni.
Ina tsaye ina kada miyar kubewa a cikin tukunya. Ya rungumoni ta baya, kanshi yana sauka a gefen wuyana. Na fara kokarin zamewa daga jikinshi, amma ko motsi bai yi ba.

Yace "bai kamata ace kina aiki ba yanzu, in fact kamata yayi ace yanzu kina kwance ne kina hutawa. Are you okay?".

Kunya ta rufo ni kamar kasa ta tsage in shige, nayi kasa da idanuna tare da daga kai.
Murmushi yayi, "ni fa kada ki fara min wani sadde-sadden kai, don ba zan laminci hakan ba. Zaki iya yin girkin? Idan ba zaki iya ba kinga ki barshi, bari in tura yanzu a siyo mana".

Nace "ni fa lafiyata lau, kuma zan iya yin girkin. Yanzu kawai kaje ka zauna, ko kaci gaba da wasu ayyukan naka, yanzu abincin zai sauka".
Maimakon ya sake ni, sai ma kara janyoni jikinshi da yayi, "na ki wayon".

Nace "Yaya...".
Kafin in karasa fadin abinda zan fada, muka ji anja wani irin tsaki, duk muka juya muka kalli Raheemah dake tsaye a bakin kofar kicin din.

Fuska a murtuke take kallon Yaya, "wallahi an dai fadi babu nauyi, girma kuma ya fadi. Ban da tsabar jaraba ma da masifa, da tsakiyar ranar Allah Ta'ala ma ba za'a daina jaraba ba? Mu dai bamu saba ganin wannan jarabar ba, idan ma ta wanke ta baka ka sha ne, to Allah ya tsare ka".

Ni baki a dage nake kallonta, me yasa matar nan ta saka min idanu ne a cikin rayuwata? Kada dai ace... ta san abinda ya faru yanzu? Na kalleta cikin zare idanu.
Yaya ma bai ce mata komi ba, sai ma kara nutsa kanshi da yayi a wuyana yana peppering wajen da kananun sumba, kamar bata wajen.

Ta sake doka wani tsakin, "wallahi an dai ji kunya, ya biyewa yarinya karama suna shirme a cikin gida!". Ta fita daga kicin din tana cigaba da mita da zazzaga masifa.
Na ture shi daga cikin jikina a hankali, wannan karon ya ja da baya ya tsaya yana kallona, cikin turo baki nace "don Allah ka tafi dakinka ka huta, yanzu zan kawo maka abincin".

Ya shafa sumar kanshi, "but ke ce yakamata ace kin huta baby ba ni ba!".
Abin nashi ya fara kokarin yin yawa, cikin sanyin murya nace "na fada maka lafiyata lau, don Allah ka tafi kawai".
Ya daga kafada, "shikenan, tunda kin dage. Amma ki tabbatar yau babu wani aiki da zaki kara yi, ina jiran ki a falona".
Sai daya manna min peck a goshi, sannan ya fita daga kicin din. Na sauke ajiyar zuciya a hankali, na juya naci gaba da ayyuka na.
Chapter 69 · 0% Book details