← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 95

Sashe 43

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na dauki system dina na fara aiki akan project din da nake to har zuwa lokacin da Janan ta kira ni, sannan na dakatar da aikin na dauki wayar. Bayan mun gaisa ta watso min tambayar lafiya ta lau dai ko? Na kada idanu kamar ina ganinta, "ehh, ga wanda ya kwana ya wuni cikin tashin hankali da damuwa da rashin barci har da karin ciwon kai, lafiyata lau Jan. Ina fata kinyi kin tashi kin kuwa wuni cikin koshin lafiyata?".

Janan tayi yar dariya, "ai daga ji ma babu tambaya lafiyarki lau, ba sai kin janyo min wani dogon bayani ba. Ya karatu, ina fata dai kinyi ko?".
Na dan saci kallon tulin jotters da textbooks dana fiddo dazu wadanda suke jiran in daga su, tare da sauke ajiyar zuciya lokacin dana tuna akwai fa sauran gingimemen aiki a gabana. Nace "ban fara ba wallahi, amma anjima da yardar Allah zan fara tunda dama revising ne kawai zan yi".
Tace "hummm, nima hakan take. Allah dai ya bamu sa'a". Nace "ameen".

Tayi shiru, hesitating, banyi kokarin katseta ba ko tambayar lafiya, nasan tunda naji haka akwai magana da take son muyi, wadda kuma bata wuce ta mutum daya. Sai da tayi radin kanta tace "me zai hana ba zaki saurari Yaya ba don Allah? Ko sau daya ne Janan, ya cancanci wannan damar daga gareki".

Nayi shiru ina sauraronta, sai data dire aya sannan nace a hankali, "dalilin kenan da yasa kika kira ni dama? Saboda Yaya?".

Itama ta danyi shiru kafin tace "wai me yasa kike cewa haka ne Na'ilah? Ke kinsan cewa tsakanina dake ai babu wannan abin, wallahi jin ki nake kamar yar uwata ta jini, sai dai shima Yayan ina jin shi a cikin jinin jikina. I just want what's best for you Na'ilah, shine kawai!".

Na san duk abinda ta fada hakan take, idan kuma da kunya da kara, bai kamata in watsawa dan uwanta kasa a ido ba, sai dai bana tunanin zan taba iya wannan abu da Janan take kokarin sanyowa, ba zan iya yin wannan karar ba.
Nayi kasa da murya, cikin tsananin son yi bayanin da zata fahimta, wanda kuma ba zata kullace ni ba, nace "Janan... Ke kinsan abinda yake damuna, kin kuma fi kowa sanin yadda nake kin wannan akidar, don haka don Allah don Annabi Jan, ki taimake mu ki daina sako wannan maganar. Kince you just want what is best for me, barin wannan maganar shine mafi a'ala a gareni, don haka don Allah mu daina yin ta kawai. Don Allah kice min kin fahimce ni?".

Tace "na fahimce ki, sai dai Na'ilah, wannan fa ba karamar magana bace ko kuma maganar wasa da zaki ce a barta kamar bata taba faruwa ba. Yaya ma ba zai taba kyaleki ba in gaya miki gaskiya, shirun da kika ga yayi kawai ya baki iska ne ki hada tunaninki waje daya. Ina ga da kin hakura kun yi magana, kiji abinda zai ce mikin".

Na fara gajiya da maganar wannan, tun jiya muke nanatata kamar cin kwan makauniya, cikin nuna alamun gajiya da maganar nace "kamar yadda nace miki, kawai mu bar maganar nan. Babu wani abu da zamu tattauna tsakanina da Yaya Bilal, ke kin sani. Ba zan taba mika wuyana a sare shi ba alhalin ina cikin hankalin kaina, haba Janan, idan har kin tabbatar kina so na kuma kina kaunata, bai ma kamata ace kina nema kiyi convincing dina ba koda wasa".

Itama cikin nuna alamun gajiyawa tace "whatever Na'ilah, ni dai iyaka shawarar da naga zan iya baki kenan. A gani na idan kuka yi maganar, kika yi mishi bayani, zai iya ba zuciyarshi hakuri ya nemi daidai dashi wadda zata iya zama dashi da matan shi tunda ke kin ce baki iyawa. A ganina kenan. Sauran kuma, Yana gareki. Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, sai mun hadu a asibiti gobe!". Ta katse wayar.
Na bi wayar da kallo. Daga jin yadda muryarta ta dan daga, ranta ne ya fara baci. Ban yi kokarin sake kiranta ba, na maida wayar na ajiye. Bana tunanin wani abu zai iya canza min kudirina, ciki kuwa har da fushin Janan.
Na fahimci kaunar da take yiwa dan uwanta ce ta haddasa hakan, sai dai me yasa ni ba zasu fahimceni ba? Me yasa ba zata yi kokarin fahimtar dalilina ba??!.
Nayi kokari na kauda tunanina daga kan wannan magana na ci gaba da abinda nake yi.

Sai bayan la'asar sannan na fita karatu. Har aka kira magriba ina can, sai masallaci naje nayi salla. Akan hanya na tsaya na sayi doughnut da yoghurt, na koma class. Sai wajen karfe goma na koma daki. Ina komawa ko kayan jikina ban iya cirewa ba na zube akan katifa saboda barcin daya cika min ido.

*

Washegari kuwa garas na tashi, bayan nayi sallah na fara duk wasu al'adu dana saba kafin in fita zuwa asibiti. Jikina a dan sanyaye yake saboda nerves din jarabawa, kodayake nasan kusan kowa ma haka yake ji, an riga an saba. Na shirya a nutse, ban dora abin karyawa ba saboda azumin sitta shawwal da nake yi, zuwa gobe zan gama gabadaya in Allah ya yarda.

Akan hanyata ta zuwa venue din da zamu yi jarabawar, wayata ta fara pinging alamun shigowar message. Ina dubawa naji gabana yana dukan uku-uku, Yaya ne. Kin dagawa nayi, ina tsoron in daga in karanta abinda zai hana ni sukuni bayan ina da muhimmmiyar jarabawa a gabana.
A kalla kafin in karasa venue din, ya kara turo wasu sakonnin kamar guda uku haka. Na tsaya na bada ajiyar wayar wajen securities bayan na kasheta, sannan na shiga ciki.

Seat dina yana kusa dana Janan ne, yadda muka rabu da ita jiya nayi tunanin ko kallon arziki ba zan samu daga gareta ba, sai ta bani mamaki data haskeni da murmushin man nata, ta dan matsa kadan yadda zata bani waje sosai tana cewa "sai yanzu? Wato kema kin koyi makara ko?".
Na dan saki murmushi a tausashe, duk da yanayin da nake ciki, sai naji raina ya dan yi sanyi, na zauna kusa da ita, "ai kin san zama da madaukin kanwa...".

Tayi yar dariya, "idan ma dani kike, bani na goga miki ba, can zaki je ki nemo wanda ya goga miki yarinya!". Muka yi musayar murmushi.
Ba abin mamaki bane ga halayyar Janan, sanyin zuciya irin nata da kawar da kai har kullum shine abinda ya tsananta tsayin abotarmu da ita. Ina girmamata saboda hakan.

Muka fara revising ya junanmu gami da tambayoyi game da abubuwan da muka karanta, har zuwa lokacin da masu tsaron jarabawar suka shigo. Da misalin karfe tara kenan.
Jarabawar ta daukemu awanni biyu da rabi cur, kusan tare muka gama ni da Janan amma ta riga ni fita. Na mika takardar bakina dauke da addu'o'i iri-iri, idan nayi rashin sa'a jarabawar nan ta dawo min ban san ya zamu karge da Baba ba.

A bakin kofar wajen na sameta tana jirana, na amshi wayar hannuna, muka jera ni da ita hannu da hannu har zuwa cikin hostel. Allah ya taimaka yau sun daga mana shiga cikin asibiti har sai zuwa gobe. Muna ta tattaunawa game da jarabawar har muka shiga hostel din.
Muna shiga ta cire uniform din jikinta, nima na cire nawa. Na ciro mata rigar shan iska, doguwa mai wadataccen fadi, nima na saka shigenta, muka kwanta akan katifata, sai a lokacin na bata labarin Anty Sailu fa tana asibiti, ta jinjina lamarin tare da cewa zata kira ta mata sannu.

Ba karamin dadi naji ba da bata kara tado min zancen Yaya Bilal ba. Again, nan ma ta bani mamaki. Janan ba irin mutanen nan bane masu saurin sakin abu ba, idan ta sako abu a gaba ko kuma wata magana, bata saki don wasa har sai ta cimma nasara. Shi yasa yanzun nake ta kaffa-kaffa da ita, ban san ko me take tunani ba a cikin ranta.

Sai da muka yi sallar azuhur bayan mun koma mun kwanta, sannan na bi bayan sakonnin da Yaya ya turo min dazu, hannuna har rawa yake yi.
Na farkon cewa yayi; _'Hey, you okay?'_

Na biyun kuma: _'Nasan cewa ba ta haka ya kamata in tunkare ki ba, nayi kuskure. Should've thought about it more kafin in tunkare ki ta wannan hanyar, saboda haka ne nake baki hakuri!'._

Sai kuma, _'Baby, na san cewa kina ji a cikin ranki kamar ban kyauta miki ba, ko kuma wasa nake miki da hankali. Ina tabbatar miki da cewa ba haka bane, please let me explain myself!.'_

Akwai kuma wanda na kula ya sake turowa nan da mintuna sha biyar da suka wuce: _'Please baby, da gaske ba zan iya cigaba da zama a haka ba. Nayi kokarin ganin cewa na baki cikakken lokaci domin ki samu kiyi tunani akanmu, I know it's sudden. But that's it! I can't do this anymore.. Let me see you again, please? I promise zan miki bayanin duk abinda kike son ji, kinji baby na?!'_

Ina gama karanta wannan naji wani abu mai zafi ya daki zuciyata, idanuna suka fara min zafi alamun kwalla ta fara taruwa. Na lumshe idanuna tare da kwantar da kaina akan pillow. Yaya Bilal ya riga ya bata rawar shi da tsalle, koda yake tun daga farko dama bashi da wani chance a wajena, amma me yasa raina yake kuna idan na tuna cewa zamu rabu dashi har abada?! Me yasa nake jin kamar ina gab da rasa wani muhimmin bigire na jikina ba? Ko dai zan bi shawarar Janan ne, inyi rethinking wannan bakon al'amari?.
Nayi gaggawar girgiza kaina, inaa! Ba zai yiwu ba!.
Chapter 43 · 0% Book details