← Book details A Zato Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 95

Sashe 45

A Zato Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "ban sani ba. Ni zo ki raka ni waje inje in sayo wani abu in ci".
Ba musu na tashi na bi bayanta, da yake karfe sha biyu da rabi ta kusa, lokacin tafiya sallah yayi. Muka yiwa Aisha sallama muka fita, nace mata "ai nayi zaton kina azumi ne yau".
Tace "a'ah". Ganin tana amsa min magana dai-daya yasa nayi shiru nima.

Tace "wannan likitan da kike biyewa, son shi kike yi ne?".
Na dan yamutsa fuska, "wace irin magana ce kike yi haka? Wani irin so kuma?".
Tace "to sai wani yage mishi baki kike yi kina dariya, me hakan yake nufi?".

Na girgiza kai, "don Allah kada mu ja maganar nan tayi tsayi. Ni babu wani son shi da nake yi".
Tace "to sai ki daina bashi fuska, a haka kina leading dinshi ne kawai ba wani abu ba!".
Na daga baki hangamgam, nace "to wai ke meye matsalarki ne? Idan na kula shi ko naki kula shi, meye damuwarki?".
Har ta daga baki zata yi magana, sai kuma ta fasa, tace "oho dai, ke kika sani!".
Muka yi shiru muka cigaba da tafiya, can kuma tace "ya labarin su Sailu?".
Muka karkata hirar zuwa can, wanda hakan ba karamin dadi yayi min ba.

Mun je ta sayi abinda zata ci, muka biya ta masallaci nayi sallah sannan muka koma ward. Acan taci abincin, muka cigaba da ayyukanmu har lokacin tashin mu yayi.
Janan ta riga ni tafiya saboda lokacin da aka tashi, wani yaro nake yiwa dressing. Faduwa yayi garin wasa da keke. Don haka ta wuce saboda a cewarta, zata biya kasuwa ta sayi wasu kayan bukatu kafin ta wuce gida.
Sai wajen karfe biyar da kwata na gama, na yiwa mutanen wajen sai da safe, na fita.

Sai dai cak! Naja na tsaya lokacin da nayi arba da abinda ban taba tunanin zan gani a daidai wannan lokacin ba. Yaya Bilal ne a tsaye kyam, tsayuwar sojoji, ya zube hannuwanshi duka biyu a cikin aljihun wandon kaftani dake jikinshi.
Kamar wanda aka ce mishi ya dago kanshi, karaf muka hada idanu dashi.

Abu na farko daya fara zo min a cikin raina, shine in fyalla da gudu. Sai dai da nayi tunani, sai naga meye na gudunshi to? Hakan ba wata mas'ala bace. Shawara ta biyu ita ce in tafi in raba ta gefenshi kawai in wuce, in nuna kamar ban san shi ba. Sai dai matsalar itace, kafafuna sun kasa motsawa balle har suyi tafiya. Don haka naci gaba da tsayuwa anan inda nake, ina kallon Yaya Bilal.

Ganin bani da niyar yunkurin yin wani abu, yasa ya tako cikin wani nutsattsen taku ya tunkaroni. Sai lokacin naji kafata ta motsa, na fara ja da baya, amma bai daina tunkarata ba. Da dai naga ya kusa cimma ni, sai na juya na sake fecewa a karo na biyu.

Can A&E na tafi, na shige can wani lungu da mutane basu cika bi ba na labe kamar wata munafuka. Na kwashe fiye da mintuna ashirin a wajen, zuwa lokacin nasan idan ma nema ne Yaya ya gaji ya kara gaba, don haka na fito daga maboyata.
Sai dana karewa wajen dana ganshi dazu kallo na tabbatar da cewa baya nan, sannan na daga kafa da sauri kamar wadda aka cilla daga jikin mashi, na dauki hanyar komawa hostel.

Sai dai da yake kwata-kwata yau sa'a ba a sashe na take ba, sai dana fara hango gate din hostel, har ina kara daga kafa, kawai sai ganin mutum nayi a gabana kamar wanda ya diro daga sama. Nayi tsalle nayi gefe daya a tsorace ina rafka salati, kafin in daga kaina in sauke su akan dodon nawa. Shi din dai da nake ta gudu.
Na sake juyawa da nufin ranta ana kare, ya sake shiga gabana, juyawar da nayi da sauri, da niyar bi ta wata hanyar, sai naji ni shame-shame a jikin bango. Shi kuwa yayi babakere a gabana, ya tsare gaba da baya, ta yadda babu yadda za ayi in tsere, sai dai idan bangaje shi zanyi. Ko kuma in ratsa ta jikin bangon dana jingina.

*☆⋆25⋆☆*

Ga duk wata diya mace da take jin ta cika 'ya, mai cikar halitta da kamala, wadda zata shiga ko'ina ne a fadin duniyar nan kanta a tsaye, ta kuma amsa cikakken suna na 'ya mace, to ta cancanci gwarzon namiji kamar Yaya Bilal.
Irin mazajen nan ne da ake kira mazajen duniya. Wadanda Allah yayi wa ilhama da kuma rufin asiri ta kowane fanni.

Tun bayan rasuwar mahaifinsu, a lokacin yana ajinshi na shida a makarantar firamare, yayin da babbar yayarsu Yaya Sa'a take aji na biyar a sakandire, Jameel kuma yana primary three, duk da kankantarshi, Bilal bai yi kasa a gwiwa ba wajen zagewa tun karfinshi wajen ganin cewa ya tallafa musu. Wannan duniya da muke ciki ta riga ta zama abinda ta zama. Mutane basu san kowa ba daga kansu sai iyalansu, wasu ma iyalan nasu sai na kurkusa kawai. Mahaifinsu mutum ne mai rufin asiri daidai gwargwado, bayan rasuwarshi kuma sai rayuwa take nema ta zamar musu wata aba mai tsananin wahala.
Ummansu ta fara sana'o'i na hannu iri-iri domin ta samu ta tallafi ci da shan 'ya'yanta da karatunsu. To shima Bilal bai zauna ba, kananun sana'o'i na hannu babu wanda bai kama ya taba ba, kanikanci, dinki ne, bude karamar tired, da dai duk wata hanya daya san zata sada shi da samun halaliyarshi.

Duk da cewa yan uwa na iyaka bakin kokarinsu, sai dai kamar yadda nace, wannan zamani da muke ciki yanzu ya zama naka sai na naka. Koda suka fara abin daga farko kamar abin arziki, sai suka zo suka watsar. Shi kuwa yau a duniya, babu wani abu da yafi saurin zubar da mutunci da kima irin yawan bani. Ko iyaye gajiya suke yi balle kuma wadanda alaka ce kawai da bata kai ta kawo ba ta hada. Don haka suka kama kansu, idan an kawo musu abin amfani ko na tallafi, su karba suyi godiya, idan basu dashi, suyi kama-kama su rufawa kansu asiri.
Wannan gida da suke zaune, shi kadai mahaifinsu ya bar musu a matsayin gado, su ukun da kawunsu daya kasance kanin mahaifin nasu. Sai kuwa wata karamar gona da aka sayar da ita lokacin da Yaya Sa'a zata zana jarabawar fita daga babbar makarantar sakandire.
A cikin wannan lokacin ne mahaifinsu Janan ya fara neman Ummansu, lokacin matarshi bata jima da rasuwa ba. Kuma abokin mahaifinsu ne kafin ya rasu. Aka daura aure ta tare a Kaduna abinta.

Nan ya hade Bilal da Jameel din ya saka su a makaranta tare da sauran 'ya'yanshi suka cigaba, ita kuma Yaya Sa'a ya shige gaba, aka daura mata aure da wanda yake nemanta a lokacin bayan ta gama sakandire, taci gaba da karatunta a gidanta.
Bayan ya gama secondary, ya taho nan ABU Zaria yayi degree dinshi akan mass comm. Allah ya taimakeshi da taimakon Baban yara, ya gama degree dinshi da offer dinshi ta aikin jarida a hannu. Ya fara aikin a gidan jaridar Daily Trust da kafar dama, cikin dan kankanin lokaci ya samu karin matsayi, nan da nan yayi kaurin suna. Ya saye gidansu da suka gada a wajen kawunsu, itama Yaya Sa'a ya sayi nata ya bata kudinta. Yaje aka warewa Jameel nashi, ya tada gini abinshi. A cikin dan lokacin aka yi aurensu da Ameerah. Sun jima suna soyayya da ita, tun yana karatu a abu.

Har gashi a matsayin da yake tsaye a yau. Magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ilimi na musulunci da zamani ya gogar dashi. Yana fara aikinshi da Daily Trust, ya cigaba da neman kwalin masters dinshi ta online, bayan wannan bai dakata anan ba, yayi kwasa-kwasai da dama da suka kara mishi experience akan aikinshi, da kuma taimakonsu ne da taimakon Allah yake akan matsayin da yake yanzu a wajen aikinshi, Deputy Manager din Daily Trust.

Yana da wani irin hali na son yan uwanshi, zumunci da kyautatawa iyayenshi. Shi yasa har a kullum, Allah yake ta kara mishi budi da haske a cikin al'amuranshi. Allah ya wadata shi da haliita, zubi da kira irin na maza. Idan ka kalleshi sau daya, ba zaka so ka kauda kai ba. Irin halittar jikinshi halitta ce irin one in a million dinnan, kafin ka samu mai irinta sai ka dade. Sai kuwa alamun hutu da kasancewa cikin ni'ima ta rayuwa da suke kokarin boye yawan shekarunshi a duniya, wanda idan ba fada maka aka yi ba, mawuyaci ne ka iya cankar shekarun nashi kai tsaye.

Ta kowane fanni dai, Yaya Bilal irin mazan nan ne da idan mace ta samu irinsu, zata ce Allah ya karbi addu'arta, ya bata miji na kerewa sa'a. Idan kyawun ne, yana dashi, dukiya da rufin asirin ma dai Allah ya bashi, kyawun hali, kamala da nagarta, duk yana dasu. Duk dai wani abu da ake bukata a da namiji, miji na gari, kuma uban 'ya'ya na kwarai, idan aka zo kan Yaya Bilal dole a diga aya. Sai dai me yasa ni nake kokarin guje mishi tun karfina?!.

A yanzu daya zagaye ni ta ko'ina, duk inda na waiga babu abinda nake gani sai faffadan kirjinshi sai kuwa fuskarshi da sai na daga kai sannan zan iya ganin zagayayyun lebunan bakinshi, ni kuwa banyi wannan gigin ba. Kaina a kasa yake, ina kallon yatsun kafata kamar duk duniya babu wani abu daya kaisu kyawu.
Tattausan kamshin turaren da yake yi a karan kanshi, seems very inviting. Ji nake kamar wani maganadisu ne yake kokarin janyo ni zuwa jikinshi, domin inyi ta shakar kamshin kamar ba zan daina ba, kada ma kuma ayi maganar wannan managarcin kirjin nashi. Da na fara dago da kaina naga zan sauke idanuna akan shi, sai inyi saurin kara dunkufar da kan nawa kasa sosai.

Gashi a bakin hanya muke, mutane suna ta wucewa wanda duk da cewa kaina a kasa yake, amma na tabbatar kallonmu suke yi. Nan da nan nayi narai-narai, idanuna suka kawo kwalla.
Chapter 45 · 0% Book details