← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 46

Sashe 6

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Bibalo jiki ya yi sauƙi sai dai muce Alhamdulillah, lafiya ta samu, surutan da take yi duk ta daina su, hakan yayi wa Baba Amarya daɗi sosai, sai dai babbar damuwarta shine rashin ganin Zahrah a gidan. Duk yadda tayi tunanin a nan iyayen Uwarta suke ta rasa don bata san wacce jaha suke ba. Tun tana neman a hankali har ranta ya fara ɓaci, ta kuma ƙudiri aniyar nemo Zahrah duk yadda take. Alwashin ta darr yake, ba zata taɓa bari Zahrah tayi rayuwa mai kyau ba, kamar yadda uwarta tayi wulaƙantacciyar rayuwa (a nata tunanin) ita ma Zahrah ita zata ɗanɗana. Bata ko tunanin illar hakan duk irin yadda Bibalo ta wahalta gashi kuma babu biyan buƙata.

Kawu ma dai nasa ɓangaren babu sauƙi, cikin kwana biyun nan mugayen mafarkai yake yi da Mama, mostly Kuma yana faɗawa mawuyacin hali ne tana taimaka masa, ya rasa ina wannan mafarki ya dosa, gashi kuma yanzu wata ƙaunarta ke kama shi, ya rasa yaya zai yi cikin kwana biyun nan, a halin yanzu babu abinda ya tsana sama da Baba Amarya, ko da ya shiga gidan ɗakin Mama ya fara nufa. To his suprise sai yaga ƙura alamar dai babu mai rayuwa ciki ga kuma yadda aka barwatsa komai na cikinsa.

Zuciyarsa ce ta buga, cikin ƙarfin hali ya nufi ɗakin Baba Amarya, a tare da Bibalo ya tarar da su suna cin taliyar murji da manja da kuma yaji, Baba Amarya na ganinsa ta miƙe da sauri ta zo gare shi. Kallon da ya jefe ta da shi yasa ta ɗan dakata. “Ina Madina ne?”
Sai da ta ɗan yi jim don har ga Allah ba zata ce tana iya tuna wace Madina ba har sai da ya tambaye ta a karo na biyu “Ina Madina ne?”
Cikin kame-kame ganin wannan sauyi tattare da Kawun yasa ta ce “Eh ah eh dama haka ne, eh ita da ƴar ta dama dama can sun shirya ne sai suka gudu don cin duniyarsu da tsinke....!”

Dakatar da Ita kawu yayi, shi kansa mamakin dalilin jin wannan zafi yake , a da shi kansa cin kashin da yake mata ko kare ba zai shinshina ba, amma yanzu duk wanda yaji zai faɗi magana kan ta, yana dai-dai ne da dakatar da shi ko ma waye. Juyawa yayi ya fice abunsa tare da barin gidan.

Cike da takaici Baba Amarya ta koma kusa da Bibalo ranta ɓace tace “In dai boka da Malam na nan, cikin su babu wanda ya dakatar da aikinsa, to nima ba zan gaji akan ƙudiri na ba. “Dole ka kasance a tafin Hannayena Idrisu.” ta furta a zahiri tana ɗaura kan Bibalo a kan cinyarta.

**********************

*ABATCHA ESTATE*
*FCT ABUJA*
*8:05am*

Sai da ta ƙara wanka kafin ta ɗauki wannan kayan da Hajjaty ta nuna mata, cikin wata Black expensive Abaya da ta ji stones wanda ke zuba ƙyalƙyali ta shirya, ba ta yi wata kwalliya ba coz farar powder da ke gaban Mirro ɗin ta shafa, sannan ta shafa wet leaves, ko kwalli bata saka ba ta yafa Black veil da ke haɗe da abayar ta yafa. “Masha Allah ” sosai suka karɓi farar fatarta sai ta fito a ainihin balarabiya amma fa mai jin Hausa 😂.

Hajjaty ma cikin wata atamafar ta ja da baƙa ta shirya, tayi kyau kamar ba ita ta haifi Daddy ba. Ganin ƙarfe 8:10 yasa Hajjaty ɗauko Mayafinta ta yafa “Yi maza ki fito Zahrau lokaci ya kusa cika”
Da “To” ta amsa tana ajiye turaren da ta ke fesawa tare da bin bayan Hajjaty da ke ƙoƙarin barin bedroom ɗin.

Basu ɓata lokaci ba kau tsaye suka nufi Family Hall da ke ɗan kusa sosai da ɓangaren Hajjaty. A wannan lokacin kuma da yawa sun iso, saboda su al'adar su babu African time Shiyasa in an saka lokacin taro da wuya ba'a fara shi yadda ya kamata ba.

*Shin kun sa cewa?:*
_1. Duk wanda ya tashi daga bacci ba'a so ya miƙe immediately as he wake up?, Ana so idan mutum ya farka daga bacci kada ya miƙe a lokacin, an fi so ya ɗan ci gaba da kwanciya na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya miƙe tsaye, hakan zai ƙara improving level of wellness na mutum musamman ta bangaren ƙwaƙwalwa da kuma tunani, psychologically one will be more stable_
_On the other hand miƙewa tsaye da zarar mutum ya tashi daga bacci kan haifar da matsalolin lafiya da dama, ciki yana jawo sauƙar jini (hypotension), yana kawo rashin dai-daiton tunani ta yadda zaka ga mutum a zabure kamar wani abun tsoro ya sako shi gaba. Hakan har ila yau kan iya haifar da matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwar ɗan Adam._
_So You guys should be more careful, in an tashi daga bacci a daina miƙewa tsaye a take, ayi ƙoƙarin jinkirtawa na wani lokaci ko don inganta lafiya._
_Haka nan tashi tsaye bayan dogon Zama, shima yana sanya jinin mutum sauƙa. Ba'a fiye son yin dogon Zama ba saboda gudun hakan, ku sani Sauƙar jini (hypotension) ya fi hawan jini illa, sannan yafi wahalar magancewa fiye da hawan jinin. A kula sosai da lafiya my esteem fans._

_2. Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi yakan fara kowanne aiki da bismillah_
_Manzon Allah ya kasance yakan ambaci sunan Allah a farkon kowanne abu da zai yi hatta a cin abinci, habibties kada a manta a ke yin bismillah kafin yin kowanne irin abu. Sannan ake yawaita godewa Allah bisa kowacce ni'ima komai ƙarancinta. Allah ya sa mu dace._

*Ku kasance da alkalami na don jin yadda zata kaya, masu cewa kansu ya kulle ku ƙara haƙuri ku ci gaba da bibiyar alƙalami na, komai zaku fahimta ne da sauƙi, ku tuna _A babban gida_ muke, so everything there supposed to be somehow complicated.*

*A karɓa da haƙuri my esteem fans, manage this!, ina ƙara Baku haƙuri in sha Allah komai zai daidaita. I've been busier than before that's why, Amma zan ƙoƙarta komai ya saitu. Make sure that you guys react! React!! React!!! & React har sai na gaji da ganin reactions. I love you guys😘, group members ayi comments Please sannan ayi sharing don Allah, much ƙauna 💕.*

[10/18, 5:24 AM] Diamond Bhatool:

*Typing 📲*

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*

Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._

*PAGE* 0️⃣5️⃣

_Dedicated to my superhero, father, mentor and role model in person of JS Yakubu, Allah ya ƙara maka lafiya baba._

_Masu neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu_



Gaban Zahrah ne ya buga suna kaiwa gaban makeken block ɗin da aka maƙala mishi signboard na Family Hall wanda ke ƙyalƙyali da dare kuma ya ke fitar da haske kala kala. Hajjaty da ke riƙe da hannunta ne ta fahimci hakan. Cike da kulawa ta ce “Kin ga Zahrau muje duka ƴan uwanki ne ba wani bare, kar ki ji tsoro kin ji?”
Kai ta gyaɗa sannan suka fara takawa izuwa steps ɗin da zai sada ka da hall ɗin. Suna tsayawa glass ɗin ya zuge nan suka shiga ciki.

Mutane ne sosai suka halarci taron, manya da yara, sai dai babu iyaye mata da alama iya mazan ne a ciki. Shigowar Hajjaty yasa hankalin su komawa ga saitin ƙofar, mamaki sosai ya cika su ganin wata baƙuwar fuska wacce ko makaho ya shafa ta zai sai jinin gidan ce, but to them abun ya ɗaure kanunsu. Ko da yake lokacin Alhaji Baba ne kaɗai bai shigo ba sai kuma Daddy yasa suka nemi wuri suka zauna. Few minutes sai ga Alhaji Baba tare da Daddy wanda ke riƙe da shi. Har wurin zamansa aka kai shi bayan ya zauna Daddy ma ya nemi nasa wurin ya zauna.

Babu alamar motsi cikin hall ɗin tun shigowar Alhaji Baba. Kowa yayi tsit yana sauraran me za'a ce, wadanda suka kula da shigowar Hajjaty ma suna jira a kammala su ji wacece wannan kyakkyawar yarinya da suka shigo tare.

Alhaji Babba wanda a kodayaushe in za'a yi wani taro yake fara magana kamar yadda ya kasance babba cikin Abatcha family. Microphone 🎤 ɗin ya ɗauka da fara magana.
“Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatouh”
Gabaɗaya Hall ɗin ya ɗauka da “Wa Alaikumussalam”
Nan ya ɗaura da faɗin “Iyayen mu masu daraja, ƴan uwa na da kuma ƴaƴan mu, barkan ku da wannan safiya mai Albarka” sai ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba
“Kamar yadda na gani akan fuskokin ku na ƙara tabbatar wa da kaina cewa kuna mamakin wannan unexpected meeting, so Kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara magana akan abinda ya tara mu. Sai dai kafin nan kamar yadda muka saba za'a bude taron da addu'a, Bismillah Qasim”

Wani kyakkyawan saurayi ne ya mike ya amshi microphone ɗin daga hannun Alhaji Babba, fuskar matashin sake wacce da ke nuna zallar kamala da kwarjini ya fara magana, khudhbatul hajah ya fara daga nan yayi addu'o'i sannan ya mikawa Alhaji Babba da ke zaune microphone daga nan ya koma mazauninsa.

Alhaji Babba ya ci gaba da magana “Masha Allah, Allah yayi Albarka Qasim, kai tsaye zan fara magana akan abinda ya tara mu. Idan baku manta ba wasu lokutan zaku ji ƴan uwana wato iyayenku suna magana akan ƴar uwarsu wacce ta ɓata tsawon wasu shekaru masu yawa” sai kuma yayi shiru. Nan hankalin kowa ya ƙara komawa jin me Alhaji Babban zai ce? An same ta ne ko kuma ta mutu ne? They're all earger to know.
“Alhamdulillah” Alhaji Baba ya ci gaba “Cikin ikon Allah Ubangiji ya nuna mana gudan jininta, sai dai ta ɗaya bangaren har yanzu dai ita Madina babu labarin ta, saboda haka a ƙara ƙaimi wurin Addu'a Allah ya bayyana ta.”
Chapter 6 · 0% Book details