← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 46

Sashe 10

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe idanuwansa yayi tare da buɗe su lokaci guda sai kuma ya kalli Ya Khalil, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Ok”
Da sauri Yaya Khalil ya ɗago ya dube shi jin amsar da ya bashi wondering if amsan da ya bashi yaji da kyau. Tunaninsa ya koma kwacakom ga bai ji da kyau bane. Ganin dai ba ƙara magana Yaya Sadauki zai yi ba yasa yaya Khalil faɗin “Man ka haƙura zamu koma Naija??” kamar ba zai kula shi ba sai ya ɗaga kansa alamar eh. Da sauri yaya Khalil ya miƙe ya rungume Yaya Sadauki, bai yi ƙoƙarin dakatar da shi ba coz he need it, he need someone to hug him ko zai sa damuwoyinsa raguwa. Cike da Farin ciki Yaya Khalil yake faɗin “Masha Allah, thank you so much, Allah ya ƙara maka lafiya.”
Cikin ransa ya amsa da “Amin” sai kuma ya janye Yaya Khalil ɗin da ke jikinsa zuwa gefe.
Lokaci guda kuma suka shirya, ko da Dr. Ya zo yayi discharging nasu ba su tsaya ba suka wuce bayan shawarwarin da Dr ɗin ya bawa yaya Khalil game da rashin lafiyar yaya Sadaukin.

******************

Ganin duk ƴan matan sun tafi yasa Hajjaty ƙwalla ƙiran Zahrah da ke kwance kan sofa. Da sauri ta miƙe tsaya tana faɗin “Ina zuwa Hajjaty ” a gefen Hajjatyn ta zauna, nan Hajjaty ta fara jan ta da taɗi, sosai suka sha hirarsu Hajjaty na ƙara kula da yanayin Zahrah tana mai ƙara fahimtar ta. Lokacin sallah da yayi Hajjaty ta saka Zahrah gaba suka gabatar da sallar su wanda su biyun suka daɗe a sujjada suna masu faɗawa Ubangiji damuwarsu wacce kusan duk kusan abu ɗaya ne suke roka wurin Ubangiji.

Bayan sun yi sallah suka yi lunch ɗin su, ko tashi daga dining area basu yi ba sai ga Nasreen ta shigo ɓangaren Hajjatyn.
Cike da son tsokalo Hajjatyn ta ce “Zahrah samu kiyi wanka tunda kin shirya mu tafi part ɗin mu.” Hajjaty da ke shirin miƙewa ta ce “Kya yi ki gama ai, ko uwarki Ruƙayya bata isa ta zo tace Zahrau tabi ta ba.” dariya Nasreen tayi ta ce “Mai da wuƙar Hajjatyn mu, ba da faɗa min ga na zo ba, na zo ne na ɗauki ƴar'uwa ta mu ɗan huta.”
A ɗan fusace Hajjaty ta ce “To ai sai ki ɗauakd ta ko! Ke Nasreen wallahi ki kiyaye Ni, har Ni zaki faɗawa yan'uwan taka? To ki ɗauke ta ku je maza.”
Ganin dai da gaske Hajjaty fushi tayi yasa Nasreen kwantar da murya hanmayenta biyu haɗe ta ce “Yi haƙuri masoyiyar kakata wacce babu kamarta, wasa nake kawai na zo na ɗebewa Zahrah kewa ne.”

Kamar ba Hajjaty ke masifa ba sai ta saki fuska yana washe baki “Kai amma naji daɗi sosai Nasreen, Shiyasa kullum nake ƙara yabon ƴaƴan Ruƙayya , Allah dai yayi Miki albarka. ”
Sai ta kalli Zahrah da ta miƙe itama tana kallonsu tace “Zahrau kuje bedroom ɗin ki ke da ɗiyar Albarka ko?”
Kai kawai Zahrah ta gyada tana mai sakin fuakarta tare da nufar yadda Nasreen ɗin ke kallonta tana murmushi ita ma.

Tare suka ƙare yinin nan sai wuraren 5:25 Nasreen ta ce zata wuce, “Zahrah kiyi wanka kafin na dawo”, “Ok” Zahrah ta bata amsa, daga nan Nasreen ta wuce zuwa part ɗinsu. A hanzarce tayi wanka ta saka kaya, ko kwalliya bata yi ba duk da kasancewar ta gwanar hakan. Wasu EXTRA Kaya ta kwaso ta fito, tana zuwa parlour suka yi kiciɓus da Hajiya Babba. “Eh an Damah Hajiya Zan kaiwa Zahrah ne Yaya Auwab zai raka ta tayi shopping ” kamar zata ce wani abu sai kuma kawai ta yi mata alama da hannunta da ta wuce. Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kafin ta fito da sauri. Ganin Zahrah ta yi wankan ya sa Nasreen miƙa mata kayan. “Ki saka wannan kafin gobe ki yo shopping,”baki Zahra ta buɗe zata yi godiya, kamar Nasreen ɗin ta san me zata ce ta dakatar da ita tana ɗaira index finger nata a kan baki “Dont say thanks, u deserve more.”

Haka Zahrah ta sanya kayan da suka matuƙar amsar jikinta, abun ba'a cewa komai tayi kyau sosai. Nasreen ce ta kalle ta tace “Wow! Kinga yadda kayan suka yi Miki kyau kuwa Zahrah? Abun ba'a magana fah!”
Murmushi Zahrah tayi tama faɗin “Lallai kam, babu wani kyau fah, you are just kidding ”
In a serious tone Nasreen ta ce “For sure Zaharah I'm telling the fact, kin yi kyau, kina da kyau ma zance” “Ok thank you dear, kema kin yi kyau ai”. Zahrah ta bata amsa cike da son kawar da zancen.

“Kin ga Zahrah, let's get going” Nasreen ta faɗa tana riƙe hannun Zahrah
“Ina ne zamu je haka Nasreen?” Zahrah ta tambaya. “Lallai ma Zahrah ” Nasreen ta bata amsa tana harararta. “Ba Hajjaty ta ce zan raka ki ki gaida mutanen gidan ba kuma na nuna Miki gidan ba” “Oh” Zahrah ta faɗa “Wallahi na shafa'a, mu wuce ko” daga haka suka fice har lokacin hannunsu riƙe da na juna suna tafe suna taɗinsu har suka fito daga part ɗin Hajjatyn.

Da Ya Aufa suka ci karo yana ƙoƙarin shiga ɓangaren Hajjaty, da sauri suka gyara masa hanya tare da gaida shi. Tsayawa yayi yana kallon su kamar wasu sababbin halittu, ganin irin kallon da yake yiwa Zahrah yasa duk ta ɗan rikice, gyaran murya Nasreen tayi tana faɗin “Ehm Yaya Aufa mun wuce ko” sai ta ja hannun zahrah suka yi gaba. A ɓangaren ya Aufa sosai ya yaba da kyau da kuma tsarin halitta irin na Zahrah, sai ya tsinci kansa da jin ƙaunarta,zuciyarsa ta ƙara masa ƙarfin guiwa da faɗin “Ƴaruwarka ce ai!” da haka ya ahige part ɗin Hajjatyn cikin sanyin jiki.

Su Zahra na wucewa suka nufi part ɗin Alhaji Babba wanda ya kasance haɗaɗɗe tun daga wajensa, yana da girma da kuma faɗin gaske, kai tsaye Nasreen ta ja hannun ta zuwa cikin part ɗin da ke ɗauke da sassa uku manya manya. A hankali Nasreen ta furta “Nan shine sashen mu Zahrah, ɓangaren Alhaji Babba kenan ai kin gano shi?” kai ta gyaɗa mata daga nan suka tunkari sashen Hajiya Babba, wato sashen sun Nasreen ɗin.

A parlourn suka tarar da Hajiya Babba kwance kan sofa ga kuma Fruits a ɗan basket ɗin da ke table ɗin gabanta. Sunkuyar da kai ƙasa Zahrah tayi ganin matar ita kuwa bata ma san ta shigo ba coz hankalinta na ga labaran da take kallo.
Ko da suka isa dai-dai tsakiyar parlourn sai Zahrah ta zauna ƙasan carpet ɗin, Nasreen ce tayi gyaran murya tace “Hajiya Babba!” a lokacin ta ɗago ido tana duban Nasreen ɗin, bata kai ga ɗauke idonta daga gare ta ba taji wata sassanyar murya mai taushin gaske na faɗin “Ina yini”.

A lokacin Hajiya Babba ta mayar da dubanta ga sashen da sautin ya fito, duk da cewa kanta a ƙasa ya ke amma hakan bai hana zuciyarta bugawa ba. Fuakarta babu yabo babu fallasa ta amsa da “Lafiya ƙalau ƴan mata, ya kwanan baƙunta.” Zahrah da kanta ke ƙasa ta fara magana yayin da zuciyar ta ke gudu da sauri da sauri wanda bata san dalilin hakan ba. “Alhamdulillah Mama”
Ɗan sakin fuska kaɗan Hajiya Babba tayi tace “Kar ki saka damuwa a ranki, ki ɗauke Ni tamkar Uwar da ta haife ki,ga Nasreen nan zata kasance a tare da ke, amma ki kula sosai!” daga haka tayi shiru. Zahrah ta ce “Na gode sosai, Allah ya ƙara girma” bata ji amsar Hajiya Babban ba amma cikin ranta tana ayyana wasu abubuwa, why take ta haɗe mata fuska ko bata farin ciki da zuwanta ne?, abu na gaba haka ta jinjina mulki irin na Hajiya Babbar har take tunanin anya ita ta haifi Nasreen?.

Muryar Nasreen ce ta dakatar mata da tunanin ta “Mu je gaba kada Maghrib tayi bamu gama zaga gidan ba.” miƙewa tayi ta kai dubanta ga Nasreen ɗin kafin su yi waje tare, Hajiya Babba dai da ido ta bisu har suka ɓace.

Ɓangaren Hajiya Karima suka yi, a nan kam Zaharah ta samu kyakkyawar tarba daga Hajiyar tsakiya. Sosai ta nuna farin cikinta da ganin Zahrah, haka mutanen da ta tarar ma a parlourn, Hibba, da Samha su ma suka yi ta zolayanta sai taji kamar kada su tafi.

Daga nan suka wuce part ɗin Ƙaramar Hajiya, babu laifi nan ma Zahrah ta samu Garba musamman daga Aunty Meerah dake tare da ƙaramar Hajiyar.

Sosai Nasreen taji daɗi ganin yadda suke nuna mata ƙauna, can dama su part ɗin su ba'a faɗa in fact duk kansu haɗe yake Shiyasa ko da ta shiga bata fuskanci wani kallo ko hali na nuna cewa su ɗin abokan zama ne ga mahaifiyarta ba. Hakan yayiwa Zahrah daɗi duk da cewa ta saka Ayar tambaya akan hali irin na Hajiya Babba ɗin.

Daga nan sai da suka yi tafiya mai ɗan tsayi har suka wuce wani ɗan cool down mai ɗauke da flowers masu Kyan gaske, though Zahrah bata tambaya ba amma Nasreen told her that cikin estate ɗin nan akwai kwatankwacin irin wannan wuri kusan guda Ashirin, and its all meant for refreshing minds. Sai dai ta faɗa mata cewa “Wannan kuma da kika gani ba kowa ke zuwa ba saboda na Yaya Sadauki ne! Ko baya gari babu mai gigin zuwa wurin saboda wurin zamansa ne.”
Sai da zuciyar Zahrah ta buga da jin sunan though this is the first time da ta ji sunan. Amma sai ta samu ƙarfin halin faɗin “Who is he?”
Nasreen ta bata amsa da faɗin “In mun koma I'll let you know who is Yaya Sadauki, zan faɗa Miki!”

_Masn son magana da ni kai tsaye ko suke buƙatar littafin daga farko, ga number na +2347061707238._
_React please, a taya Ni isar da saƙon ta hanyar sharing don Allah, ina ƙaunarku my. esteem fans, Allah ya bar mu tare. Diamond Bhatool taku ce 🤗_

*TALLA! TALLA!! TALLAH!!!*
Chapter 10 · 0% Book details