← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 46

Sashe 17

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin shiru yasa ya fito jiki sanyaye, har lokacin kuma Hajiya Babba na zaune yana karatunta. Jiki mace ya tsugunna ya ma rasa me zai ce mata. In a cool voice ya ce “I'm so sorry Hajiya, I don't mean it to happen, ban ji daɗin abubuwan da Mommah tayi miki ba, kullum ina ƙara nuna mata hanya amma ta kasa fahimta, don Allah ki yi haƙuri, sannan kada ki biye maganar Ammie da Mami ki ce zaki hana aure na da Mabruka, Allah meant it to happen, kada ki hana don Allah.”

Murmushin su na manya tayi kana ta shafi fuskarsa tace
“Kada ka damu son, ban isa na ja da hukuncin Alhaji Baba ba, sannan batun Sughrah ban taɓa ɗaukarsa da muhimmanci ba saboda na san ba yin kanta ba ne, fata na ka taya ta da addu'a Allah yasa ta gane da wuri.”

Dattaku irin na Hajiya Babba kullum ƙara burge shi yake, murmushi yayi sannan ya ce “Bari na je na duba ta, addu'a In Sha Allah muna kan taya ta.”
Daga haka ya wuce yana ƙara godewa Allah da ya sa abun da ya faru babu wani yaro duk suna school, Mabruka kuwa yana kyautata zaton ta wuce court abunta.

Abun da ya tarar a can ai ya dama wadda ya gabata, duk irin huɗubar da suke wa Mommah cikin kunnensa ne, duk shaiɗancin su bai taɓa zaton za su yi mata irin wannan huɗubar ba duba da yadda suke nuna cewa suna tare da ita, ya za a yi su ɗaura ta kan ta kashe aurenta akan abunda ta san ba Mai sauyuwa bane?.

Makewa yayi ya wuce tare da gyara murya, tuni suka miƙe suna yi wa Mommah sallama, shi dai da kallo ya bi su yana musu addu'ar shiriya cikin ransa kuma yana ayyana barin Mommah ta yanke ne ya dace da ita, In ta zaɓi kashe aurenta fine, zata koyi darasi ne ai.

Rungume shi tayi tana kuka kamar wata yarinya
“Son kana ganin irin cin mutuncin da aka min gaban idon ka ko? Ko tausayi na ma baka yi ko?”
Hankalinsa ne ya tashi don baya son kuka musamman na ɗiya mace, macen ma wacce tayi silar zuwan sa duniya. Sanyaya murya yayi kana ya ƙara hugging nata tightly, he so much love her, yana son mahaifiyarsa ko yaya take, amma kuma ɗabi'unta kawai yake so ta gyara.

“Ba haka bane Mommah, ina jin zafin abun da ke faruwa indeed na ma Fi ki jin zafi amma ke har yau kin kasa fahimtar cewa masu zuga ki kina aikata ire-iren abubuwan nan wallahi ba son ki suke ba illa iyaka son su ga mutuncin ki ya zube.”

Ba tare da ta yadda ba sai dai kawai tana tsoron wannan damar ta kuɓuce mata yasa ta ce
“Is alright sit down let's talk.” ba musu ya zauna gefenta kamar yadda ta umarce shi.
“Na ji wata magana da Alhaji Baba yayi ɗazu amma ina so ka tabbatar min ba haka bane”

Tsaf ya fahimci a kan me take magana amma sai ya kame ya ce
“Me kenan Mommah?”

“He Said that zai haɗa auren ka da yarinyar nan da tayi kwantai har take bin maza don na tabbata abun da ya faru ma shirin ta ne”
Kamar zai yi kuka yake kallon Mommah. Tabbas wanda yayi nisa ba ya jin kira amma sai ya kame ya ce

“Yea haka ne Mommah, akwai matsala ne?”

“Tambaya ta ma kake akwt matsala Haidar?” ta faɗa a ɗan zafafe.

Ba tare da ya ce komai ba ya riƙo hannunta ya haɗa da nasa.

“Mommah Please understand, ba Wai Alhaji Baba ne ke da laifi ba, hakan da yayi adalci ne, ki ƙiyasta a ce Nainarh ce haka ta faru da ita kuma kawai sharri aka mata, kina tunanin zata samu wadda zai aure ta ne? No Mommah kada ki ce zaki ja da wannan hukunci, Ni na riga nayi accepting ma kawai kema ki share, and Zan faɗa miki wani abu da baki sani ba wallahi Mommah mutanen da ke ɗaura ki hanya ba mutanen kirki bane, kuma ki sani abinda ya faru ma suna daga cikin waɗanda suka shirya shi, ki yi tunani a kai.”

Cikin rasa Madafa ta ƙara duban yaya Sadauki sannan tace “Ba wai bana son ka yi auren nan bane, yarinyar da aka Baka ne, ɗiyar Hajiya Babba fa, matar da ke ƙwace duk wani abu da zan mallaka, kai kanka ƙoƙarin raba Ni take da kai son, Ina ga in ka auri ɗiyar ta, get something here son, in ma zaka yi auren ka auri ɗiyar masu ƙauna ta mana, ga ƴaƴan Hajiya Baraka da Saudatu amma sai ƴaƴan Hajiya Babba?”

“Mommah, ki fahimci wani abu, Hajiya Babba ba ta nufin ki da sharri ke ce ba ki fahimce ta ba saboda huɗubar da ake miki, Mommah don Allah ki gane gaskiya ki gane masu son ki tun kafin ki yi nadama lokacin da babu amfani.”

Ita fa duk iri wahalar da ta bashi na yin doguwar magana bata gamsu ba da saboda ta riga da ta yi nisa. Cikin ransa yake mata addu'ar Allah ya sa ta fahimci gaskiya.

Daga haka ya miƙe yace bari ya je ya bawa Alhaji Baba haƙuri, Bata Hana shi ba duk da bata so hakan ba, sai ta amsa da to amma ya dawo Please za ta gyara masa Bedroom ɗinsa. Shi har mamaki yau ta bashi, wai yau shi ne yake samun irin wannan kulawar daga Mommah? Lallai ta yi laushi kam.

Shi kam murmushi yayi sannan ya nufi kofa zuwa ɓangaren Hajjaty ya bar ta parlourn tana saƙawa da warwarewa.

_Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, yanzu muka fara wasan fata na dai zaku bani haɗin kai mu kammala tare da ku ta hanyar reacting, commenting da Kuma sharing. Na gode_

*Comment, react and share fisabilillah*

[12/27, 8:06 PM] Diamond Bhatool:

*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_

_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 1️⃣3️⃣

_Not edited_

                                  ﷽

Hajjaty ce sai Zahrah a parlourn, Alhaji Baba Kuwa yana can Bedroom ɗinsa tun da ya baro part din Hajiya Babba ya dawo bai ƙara leƙowa. Saƙawa da warwarewa kawai yake game da family crisis da ke samu.

“Assalamu alaikum”
Zahrah ta amsa masa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴaƴan yatsunta. Lura da yadda ta suƙure da shigowarsa sai yaji babu daɗi amma hakan bai sa ya saki ransa ba sai ma ƙara haɗesa da yayi.

Ita ta fara gaishe shi kanta ƙasa, bata ma yi tunanin zai amsa mata da ta tuna da korarta da jiya yayi. Jin ya amsa yasa ta ɗan turo baki wanda caraf a kan idon sa ne, bai ce uffan ba ya zauna gefenta Hajjaty sannan suka gaisa.

“Ai na ɗauka ka tafi yawon naka da naga shiru baka zo ka yi breakfast ba.”

Harara ya bankawa Zahrah ai ba shiri ta miƙe, cikin ransa yace “Wannan da ganinta zata yi rashin kunya sai dai kuma tana da shegen tsoro da alama”.
Ganin ta bar wajen yasa yace
“Ina nan, ban samu bacci bane jiya shi yasa ban fito da wuri ba.”

“Ayya, baka karya ba ma kenan?”

“Uhm”

“Bari Zahrah tazo ta haɗa naka wani abu Mai sauƙi...” bata kai ga kiran Zahrahn ba ya yamutsa fuska yana faɗin
“Haba Hajjaty yarinyar nan ne za ta min girki ai sai dai jagwalgwale, ki bar shi na ci lunch kawai.”

Baki riƙe Hajjaty ta ce
“Sannu Sadauki, to bari ka ji, girki jiya zan iya cewa ita tayi tunda gurasar ka ma ita tayi ta haɗa maka, Zahrah! Zahrah”

“Na'am, ga Ni nan zuwa. Ga Ni Hajjaty”

“Zaki ɗan haɗawa Yayanku abun karyawa ne mai ɗan sauƙi”

“Tooo Yaya me za a yi?”

“Something simple” ya faɗa a saman laɓɓansa. Nan Zahrah ta wuce kitchen don Samar Masa breakfast shi kuma ta bar shi suna ɗan taɓa hira da Hajjaty wacce duk rabin hirar nasiha da jan hankali take masa.

Within 10minutes Zahrah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da good flask da kuma thermoflask, tana gama ajiye masa a dining table dawo parlourn looking at his innocent face tace
“I'm done yaya.”

Shiru can kuma ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba yace
“You wait for me there ko Ni zan yi serving Kai na?”

Kai ta jijjiga sannan ta koma dining area Tana jiran zuwansa. Ya share kusan 3minutes kafin ya zo ya zauna. Serving nasa fried potatoes with egg tayi sannan ta fara ƙokarin zuba bread ɗin da ta soya da ƙwai cikin wani bowl. Hannu ya ɗaga mata hakan yasa ta tsaya tana jiran umarni.

“Have You taken yours?” ba ƙaramin mamaki taji ba jin tambayarsa amma sai tayi ƙoƙarin ɓoye hakan ta girgiza kai.

“Oya serve yourself now!”

Babu yadda ta iya ta zuba nata sai dai ta kasa ci saboda kunyarsa da kuma nauyinsa da take ji but can ɓangarensa hankali kwance ya ci abun sa yana korawa da shayin da ta haɗa masa.

Bayan ya gama ya goge bakinsa da tissue sannan ya ɗan kai dubansa ga ɓangaren da take. Ganin ba a sake take ba yasa ya murmusa kana yace

“Why Are You not eating?, Ain't you hungry?”

“Ina....Ina ci fa Yaya.” ta faɗa a rarrabe. Wani iri yake ji idan ta ƙira shi da Yaya, ji yake kamar yadda take faɗa ba kamar yadda sauran family members ɗin ke faɗi ba ne.

“Alright, ajiye zamu yi magana In na tashi sai ki ƙarasa.”

Ƙirjin ta ne ya bada sautin dimm jin maganar sa. Da sauri ta ture bowl ɗin gefe kana ta sauƙar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta, hakan kuma ya zama mata ɗabi'a matsawar zata magantu da wani babba.

“Me yasa jiya kika min dariya?”

Shiru tayi tana zaro idanuwanta.

“Bana so ina ina magana ana shiru musamman magana mai muhimmanci.”

Cikin sanyin murya tace

“A'a ba da kai nake ba Yaya, Ina tuna Bibalo ne fa...”
Chapter 17 · 0% Book details