← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 46

Sashe 3

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama jerawa ta fice, few minutes ta dawo da wasu kulolin ta jera, ta zo fita Hajjaty ta dakatar da ita “Laraba, in kin fita ki ɗauko kayan zahra ki mayar da su can ɗaki na”
Cike da girmamawa Laraba ta amsa mata da faɗin “To Hajiya, yanzu ma”. Daga haka ta fice.

Tsawon wasu daƙiƙu, misalin 7:23pm suka yi sallama zuwa parlourn, saɓanin fitarsu ɗazu su biyu, wannan karan tare da wasu samari kyawawa guda huɗu, Daddy kuma baya cikinsu. Da sallama suka shigo fuska sake. Alhaji Baba zama yayi a kan kujerarsa su kuma suka zauna ƙasa kamar yadda Zahrah da Hajjaty ke zaune.

Cikin samarin ne ɗaya ya kalli Hajjaty fuska sake yace “Barka da dare Hajjaty”
Suma sauran suka gaishe ta, kamar yadda yanayin fuskarsu yake haka ta amsa musu tana murmushi “Lafiya ƙalau yaran nan” sai kuma ta haɗe gida kamar ba ita ce ke cikin fara'a daƙiƙu kaɗan da suka gabata ba.
“Duk nayi fushi da ku, tsawon jiya shiru shiru babu wanda ya leƙo cikinku, ƴar gaisuwar safiyar nan ma babu wanda ya leƙo saboda kun maida Ni mutuniyar banza” su dai kallon Hajjatyn kawai suke suna kwaɓe fuskokinsu ba tare da sun katse ta ba.
“Amma iyayen ku da ke da daraja ai kun shiga kun gaida su ko?”

Gaban Hajjatyn suka dawo tare da durƙusawa ƙasa, fuskar tausayi suka yi cikin haɗin baki suka ce “Haba tsohuwa mai ran ƙarfe, uwar gida sarautar mata a gidan tsoho mai ran ƙarfe, ki yi wa ƴan jikokin ki haƙuri ba zasu kara ba.”
Ɗan sakin fuakarta kaɗan tayi ta ce “Ai yau ba zan yi haƙuri ba, nasan da yarin kirkin nan Mahiru na nan da ban shaƙi takaicin ku ba, shi kafin ya gaida iyayensa sai yazo ya duba lafiya ta, Allah sarki mahiru.”

Ƙara kwaɓe fuska suka yi kamar zasu yi kuka, kamar haɗin baki kuma suka kama kunnuwansu suna faɗin “Ayi mana afuwa Hajjatyn mu”. Dariya sosai Hajjaty tayi, su dai da mamaki suke kallonta though sun San halinta, lokaci ɗaya in ta birkice kamar ba zata dawo dai-dai ba, sai kuma kuga ta dawo unexpected. Shiru Hajjatyn tayi tana kallonsu tana murmushi ta ce “Shikenan yaran kirki, kun ci albarkacin yau ina cikin farin ciki na haƙura” fuska sake ta yadda zaka fahimci ainihin farin cikin da suka yi da jin zancenta suka ce “Mun gode Hajjaty tamu abar ƙaunarmu”

Alhaji Baba da ke kallonsu sosai suka burge shi, yana ƙara alfahari da jikokinsa saboda ɗa'a da biyayya da suke da shi, sai kuma ya kai duban sa ga Zahrah wacce kanta ke ƙasa tun shigowar samarin, ganin she's uncomfortable yasa ya buɗe baki zai yi magana sai Muryar ɗaya daga cikin samarin ta katse masa hnazari.
“Hajjaty farin cikin menene wannan ya ƙwacemu daga fushinki mu taya ki celebrating?”
Kallonta ta mayar ga zaharh da ke gabanta, sai kuma ta jawo ta jikinta, su ma a lokacin idanuwansu ya kai kanta, sai dai sun yi mamakin ganin ƴar matashiyar budurwa tare da Hajjaty.

Hajjaty ta ɗago kan Zahrah tana dubanta, ba tare da t kallesu ba ta ce “Albarkacin jika ta daga gudan jini na Madina”
Da mamaki suka kalleta, in basu manta ba kullum sai Hajjaty tayi magana kan Madina da take cewa ɗiyarta ce auta da ta ɓata tsawon wasu shekaru. Ganin rashin fahimta shimfiɗe kan fuskarsu yasa Hajjaty tayi gyaran murya tana faɗin “Ɗiyar Madina ne yau Allah ya kawo ta cikin ahalin nan, Zahra'u” ɗagowa Zaharah tayi tana duban Hajjaty, har lokacin idonta bai kuskura ya kai kan samarin ba. “Kinga ga yayunki nan, ku kuma ga Zahrah ƙanwarku, gobe zaku ƙara saninta, in kun fita ma ku sanar da sauran ƴaƴan akwai taro gobe”.

A tsorace Zahrah ta dube su sai kuma ta sunkuyar da kai saboda kwarjin da suka yi mata, ga kuma kyau da Allah yayi musu kamar me. “Ina yinin ku” ta faɗa cikin rawar murya. Tare suka amsa da lafiya, mai surutun cikinsu ne ya ce “Sannu Zahrah, muna matuƙar farin ciki da dawowarki cikin ƴan uwanki, fatan zaki karɓe mu hannu bibbiyu, mu dai nan muna farin ciki da zuwanki, ɗago ki kalle mu matsayin ƴan uwa na farko da kika fara gani” ya Idasa cikin sigar zolaya.
Ɗagowa tayi ganin basu nuna wani ƙyama gare ta ba kamar yadda da tayi zato.

Cikin sakin fuska yace “Suna na Auwab..” “Ni kuma Aufa...” Ni kuma Tajuddeen” sai kuma Ni “Faruq” murmushi tayi tace “Na gane fuskokin ku, sunayenku masu daɗi” cike da zolaya Ya Auwab ya ce “Ke fa bamu san naki sunan ba”
“Zahrah” ta basu amsa tana murmushi. Ta matuƙar burge su, ga ta kyakkyawa son kowa, ko maƙiyi ba ya kushe ba, ita ma bata ɓangaren tunanin kirkinsu take tana addu'ar Allah dai yasa sauran family members ɗin su kasance haka.

Ƴar hira suka fara janta da shi saboda ta ɗan ƙara sakewa da su, ganin sun ware kansu yasa Hajjaty faɗin “Ku tashi kuyi dinner Ku bar min jika, daga zuwan ku kuna shirin ƙwace min ita!”
Ya Aufa ya ce “Kai Hajjaty ki bar mu mu gana da ƴar uwarmu mana”
Danƙwalo ta kai masa ta ce “Ungo nan!, kai Auwabu ka kiyaye Ni, ku tashi nan ayi dinner.”

Gabaɗayansu miƙewa suka yi zuwa dining ɗin kowa ya nemi wuri ya zauna, ita dai Zahrah sai rarraba ido take tana ganin ikon Allah, Hajjaty da kanta ta samar mata waje daga nan ta fara serving nasu, ta can ƙasan idon Zahrah ke dubanta tana kula da yadda take komai.
Tunda suka fara cin abincin shiru ya wanzu, ƙarar spoons da ke arangama da plates kawai kake ji. She's not comfortable eating with them shiyasa tana cin kaɗan ta dakata, tatar kallon Ya Taj tayi ganin shima ya ajiye spoon ya yago tissue ya goge baki yasa ita ma tayi kamar yadda yayi.

Hajjaty ta dube ta ta ce “Zahrah ya bakya ci” a hankali don bata son sauran suji bare su ce sai ta ci tace “Naci, har na ƙishi”
“kin sha abun shan ne?” Hajjaty ta ƙara tambayarta “A'a Hajjaty” Hajjaty da kanta ta tsiyaya mata zoɓon tasha.

Bayan sun gama ci nan aka ci gaba da hira, tuni Zahrah ta gama sakin jiki da su, meanwhile Ya Faruq ya tura musu saƙon Hajjaty na meeting gobe. Da misalin tara saura su Ya Taj suka yi sallama suka wuce, Hajjaty ma ta ce Zahrah ta taso su kwanta. Sai da suka yi wanka tare da alwala suka yi shafa'i da witri. Hajjaty na zaune kan sallayar ta ta ce ma Zahrah ta je ta kwanta, babu musu ta haye makeken gadon Hajjaty, ita kuma Hajjaty sai da ta gama laziminta ita ma ta nemi wurin bacci.

Safiya mai albarka Zahrah and Hajjaty.
Fatann rayuwar farin ciki tare da Abatcha family.

_Sallar Shafa'i da Witri salloli ne da manzon Allah (S.A.W) ya bayyana cewa: « gara a baka damar yin Shafa'i da Witri akan a baka duniya da duk abinda yake cikin ta» , shiyasa manzon Allah kullum yana yin Shafa'i da Witri koda yana halin tafiya yana yin su.
Karanta Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 425._

_Zaku samu cikakken bayani kan yadda ake yin ta a channel ɗina_

★★★★★★★★★★★★

_Me kuke tunani game da rayuwar wanan ahali?, me ake aikatawa a babban gidan nan ne?, shin kuna ganin rayuwar Zahrah ta samu Salama kenan?, ina Mama ne? Ko da gaske ta mutu?, Amsoshinku na ɗaure da alƙalamin Diamond Bhatool 💎, Diamond Bhatool 💎 taku ce!👍😍_

*Vote, comment, react and share Fisabilillah!*
*Vote, comment, react and share Fisabilillah!*
[13/10, 12:12 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎:
*Typing 📲*

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*

Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._

*Masu Neman labarin daga farko, kuyi following channel ɗina.**

*Chapter 2: People only managed to smile, nobody know how they're really hurting deep down*

*PAGE* 0️⃣3️⃣

_Sadaukarwa gare ku mutanen channel ɗina *Diamond Bhatool's library*, ina godiya da ƙaunar ku gare ni._
_Ban manta da ke ba Maryam Muhammad, ƙauna ta ta musamman, ina godiya ƙwarai

*1:00 midnight*
*Unknown location but a black wilderness*

Cikin ƙasurgumin baƙin dajin wanda tsabar duhunsa ko tafin hannayenka baka iya gani, duhun wannan daji ya wuce misali, ya wuce siffantawa ga tunanin mai karatu, amma zan iya cewa duhu ne da ba lallai bil'adama ya taɓa cin karo da kwatankwacinsa ba.

Cikin ƙankanin lokaci kuma kamar tsafi sai ga haske ya bayyana kamar safiya irin rana ta fara hudowa. Kamar ƙiftawar ido sai hasken ya ɗauke wurin ya koma kamar dai dare, amma akwai haske though bai wadata ba amma mutum kan iya ganin tafin hannunsa. Kamar daga sama kuma wani irin mummunan sauti maras daɗin amo da sauraro ya fara cika jejin, a hankali kuma sautin na ƙara kusantowa i zuwa tsakiyar wani fili wanda ke ɗauke da bishiyoyi biyu a jere, ƙatuwar bishiyar kuka ne sai kuma ta tsamiya a gefenta wacce ke da duhu kamar wani kurmi.

Tsawon wasu daƙiƙu wasu halittu da zasu kai kimanin Goma sha biyar suka bayyana, ko kaɗan basu da daɗin kallo, siffarsu tayi kama da ta goggon biri saboda gashin da ya lulluɓe fatarsu. Tsarin kama ma dai basu da maraba da goggon biri sai dai haƙwarensu zaƙo-zaƙo ne baƙaƙa da su har abun tsoro. Daga cikin waɗannan halittu wanda suke bisa tsari, wani yafi wani girma, haka wani ya fi wani. Babban cikinsu ne ya zauna can nesa da da sauran waɗanda suke hallare a wuri ɗaya, hakan zai ƙara tabbatar maka da cewa shi ɗin na musamman ne.
Chapter 3 · 0% Book details