← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 46

Sashe 41

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can 'bangaren su Hajjaty ma sun 'kira wayarsa amma dai amsar 'daya ce, not reachable, Yaya Khalil ya 'kira ya 'kara shima abun ya fara 'daure kansa, ba tare da ya sanar da kowa ba coz shima bai san specifically abun da Yaya Sadaukin zai yi a Bauchi ba tunda iya saninsu dai ba su da wasu ahalin a can sai dai in aiki ne ya kai shi.

*Ya Ishaq's POV*

Alhamdulillah, there's a little bit progress regarding his condition kuma yana coping yadda ya kamata sai dai deep down his heart is suffering, how he wish ko da sau 'daya ne ya kamata a ce ya 'kara kallonta, even once, amma tun da 'kaddara tai masa yankan 'kauna da ita ya amshi hakan tare da fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi saboda ko ka'dan a halin yanzu ba ya so ya 'kara sanya iyayensa a damuwa duk.da cewa they were behind the issue, da ba dan selfishness nasu ba da ba tabbacin zai rasa Zahrah, ga shi yanzu ya rasa ta rashi na har Abada in dai ba suna da rabon ganawa ba.

Haka yinin ranar ya shu'de ba tare da kowa yaji daga Yaya Sadauki ba, sosai hankalinsu ya tashi musamman Hajjaty da Alhaji Baba wana su ka'dai suka san ya bar Abuja, to babban abun da ya gama 'daure kanunsu bai wuce rashin samun wayarsa ba, hakan ba ta ta'ba faruwa ba, bai ta'ba aikata wani abu kwatankwacin hakan ba domin duk tafiyar da zai yi in ya kai masau'ki yakan 'kira ya sanar da su. Sai a lokacin suka fara tunanin me ma yaje yi a Bauchi? Rashin mai ba su amsa yasa suka fauwalawa ubangiji al'amarin don ganin ya zai 'kare tare da addu'ar Allah ya sa jikan nasu yana cikin aminci.

Ko da Zahrah ta fahimci halin da ake ciki sosai ta shiga wata matsananciyar damuwa har kanta ya fara ciwo, fatanta da addu'arta Allah yasa a wani mugun abu bane ya faru da shi duba da yadda gabanta ke tsananta fa'duwa tunda ta shi daga bacci. A haka ta sa su Hajjaty a gaba tana kwantar musu da hankali that Yaya Sadauki na lafiya may be yanayin aiki yasa bai 'kira ba, su masa uzuri ko yaya ne zuwa safiya in sha Allah zai 'kira, Allah sarki tsofi, da haka hankalinsu ya 'dan kwanta ka'dan.

*AUNTY MABRUKA*

Sosai kanta ya fara sarawa saboda damuwar da ta ma'kalawa kanta na rashin samun wayar mijin nata. Bayan ta yi sallar Maghrib ta samu ta 'dan kwanta kan praying mat 'din cikin ranta tana nema masa kariyar ubangiji a kowanne hali yake. Kamar an zabure ta ta mi'ke ta fito parlour ta kwanta tsawon wasu da'ki'ku kafin daga bisani kamar mai shafin iskoki ta kunna TV, da yake jiya shi yayi kallon 'karshe a NTA, hakan yasa tana kunnawa ta yo baya ba tare da sanin takamaimai dalilin jin son ganin tashar ba kasancewarta mace maras son hayaniya da wargi, sam ba ta damu da kutsa kanta rayuwar kowa ba hakan yasa ba ta tashi da son kallon labarai ba.

Kwacakom hankalinta na ga TVn har sadda suka tafi talle, bayan wasu mintoci kuma suka dawo, kamar an ce ta gyara kwanciyarta kuwa ta 'dan zunku'da, maimacin labaran rana aka fara, tana gani zuciyarta na tsananta bugu kamar za ta faso 'kirjinta ta fice, ba ta ankara ba haka ta ga abun da yayi sanadiyyar tashin hankalinta, idan har ba ta manta ba to babu shakka Bauchi mijim nata ya tafi. A matu'kar firgice ta tashi tsaye tana dafe saitin zuciyarta, kafin ka ce me wani irin jiri ya kwashe ta, nan ta fa'di 'kasa sumammiya.

*YAYA KHALIL*

Tashin hankali, wai ba a sa masa date, tunda ya shiga facebook nasa ya fara cin karo da wasu irin post wanda kusan dukkansu are relevant to each other, a lokaci 'daya zuciyarsa ta 'kara tsananin bugu haka kuma 'kwa'kwalwarsa ta tsaya cak da aiki, ba abunda yake fahimta tsawon wani lokaci, abun kamar tsafi 'kwa'kwalwarsa ta dawo aiki. A matu'kar razane yace
"What!" Sai kuma ya mi'ke tsaye yana 'kara zuba idanuwansa ga screen 'din wayarsa don 'karyata abun da idanuwansa suka hango masa. Bai kai ga cimma matsaya ba sai ga 'kira daga Alhaji Babba.

A matu'kar ru'de ya 'daga yana fatansa dai Allah yasa Alhaji Babba zai 'karya masa abunda ya gani ne.
"Assalamu Alaikum, an yini lafiya Alhajinmu?"
Sallamar kawai ya amsa masa, tun daga yanayin muryarsa Yaya Khalil ya rasa gaba'daya hope 'dinsa. Ba tare da ya bi takan gaisuwar da Yaya khalil ya masa ba yace.
"Kai Khalil, ina 'dan uwanka ne?"
kamar zai yi kuka yace
"Alhaji ai Sadauki ya tafi Bauchi 'dazun nan ma jirginsu ya tashi, sai dai kuma...."
ba tare da ya bar Yaya Khalil ya kai ga aya ba ya fara doka salati.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una..innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.."
haka Alhaji ke ta doka salati ba tare da ya katse kiran ba, a matu'kar firgice Yaya Khalil ya katse kiran don zuwa yanzu ya yadda da abubuwan da ya gani. Tsabar yadda zuciyarsa ta gama raunana ta kuma bushe 'kayau hawayen ma kasa zubo masa suka yi, tunani ya fara me ya kamata yayi yanzu? Tunawa da 'yar'uwarsa yayi hakan yasa ya figi motarsa sai gidan Yaya Sadaukin.

Sallama yake kwa'dawa but shiru, hakan yasa ya shige da sauri yana addu'ar Allah dai yasa news bai kai gareta ba, bulb ya kunna sai dai abun da idonsa ya gani yasa zuciyarsa bugawa tare da 'kara raunana. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa, a hanzarce ya nufi Aunty Mabruka da ke kwance 'kasa a halin rayuwa ko mutuwa. Ya ma rasa mai ya kamata yayi sai da ya hangi glass cup 'din da ke kan centre table yayi hanzarin 'daukowa ya shafa mata a fuska, wani irin gauron numfashi ta sau'ke tare da fa'din
"Shikenan..." ba ta kai ga 'karasawa ba jikinta ya 'kara saki.

A matu'kar tsorace ya 'kara 'daga hannunta, ganin ya sake yasa ya 'daga ta da sauri ya nufi mota da ita, ko da maigadi ya g haka tuni ya wangale get yana fatan Allaj yasa lafiya...musamman da ya san Yaya Khalil mutum mai barkwanci amma yau ko kallonsa bai ba, uwa uba kuma Hajiyar da yaga an fito da ita a hannu.

Da matsanancin gudu ya figi motar, bai tsaya ko'ina ba sai asibitin estate nasu, a matu'kar 'dimauce ya fito da ita a hannunsa, nan ya ma rasa ina ne mashiga sai dube-dube yake.
Dr. Mubarak da ya fito don wucewa gida ya ga Yaya khalil ri'ke da maras lafiya yasa ya kwa'da masa 'kira, a matu'kar 'dimauce ya waiwayo, da sauri Dr. Yayi wa nurses magana, kan kace me sai gasu sun turo stretcher har zuwa wurin da yake. Babu 'bata lokaci suka shige ciki da ita don bata taimakon gaggawa. Yaya khalil bai tsaya ba ya kira Numbern Humaira yace tayi maza ta taho asibiti za ta kula da mai jinya, idan ba ta same shi ba tayi wa Dr. Muba magana zai kaita. Da haka ya katse kiran yana bin wayarsa da kallo, sai a lokacin ya ga missed calls ba adadi, Daddy, Papa, da sauran uncles nasa duk sun 'kira ba adadi, sauran cousins nasa da su Aunty Madina duk sun 'kira bai ma sani ba, haka friends nasu ma 'kira babu adadi.

Ta riga ta tabbata, hakan yasa ya nufi cikin estate 'din don ganin halin da suke ciki. Abun mamaki har lokacin su Hajjaty da alama labari bai kai musu ba sai dai suna cikin matsanancin tashin hankali. Ajiyar zuciya ya sau'ke daga nan ya juya ba tare da ya ida shiga ba, karo suka ci da Ya Qasim wanda fuskarsa tayi ja alamar dai kuka yayi ga kuma tashin hankali 'karara a fuskarsa.
Rungume shi Yaya Qasim yayi tare da sakin wani irin kuka wanda duk wani mai sauraro ko mai gani yaji ko ya gani dole zuciyarsa ta raunana more especially da ya kasance namiji ne ke kukan, namijin ma irin Yaya Qasim da ya kasance mutum mai juriya da tawakkali.

Har lokacin Yaya khalil bai samu damar zubar da 'kwalla ba ko da kuwa 'digo 'daya ce, bai hana Yaya Qasim 'din kukan ba saboda shima kansa zuciyarsa ta gama raunana har hawayensa sun 'kafe, tsawon mintuna goma suka kwashe suna rungume da juna tukun Yata Qasim ya saki Yaya Khalil yana aika masa wani irin kallo da ke nuna bu'katar 'karin bayani.
"Da gaske shikenan mun rasa shi?, kace min ba haka bane Khalil!" Ya fa'da a matu'kar raunane.
Rasa wace irin amsa zai bashi yayi hakan yasa ya ke'be shi zai wuce. A matu'kar zafafe Yaya Qasim ya cakumo Yaya Khalil 'din.

"Ya za ka wuce ba ka bani amsa ba, ka fa'da min meye gaskiyar batun!" Ya fa'da cikin zafin rai "I can't afford to lose suck brother Khalil, ka ce abun da na gani ba haka bane!" Ya fada cikin raunin murya.
Ganin yana shirin tara jama'a shi kuma ba ya so a ji mutuwar sarki a bakinsa yasa ya bu'de baki murya 'kasa-'kasa yace
"It's all true Akhy, Yaya mun rasa 'dan'uwanmu da gaske....."
Ba tare da ya 'karasa ba ya zame jikinsa zai koma mota sai dai me? Ganin su Hajjaty da wasu daga family members 'din yasa ya 'dan tsaya yana kallonsu.

Muryar Hajjaty ce ta doki kunnensa
"Ban gane me kuke magana a kai ba Halilu,waye aka rasa kuma meyasa Qasim ke kuka? Me ya faru ku bani amsa!" Ta fa'da cikin sigar tsorata don ba shakka da za a gwada bugun zuciyarta a lokacin to tabbas ya tsananta.
Chapter 41 · 0% Book details