← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 46

Sashe 4

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin sauti mai rikitar da tunanin bil'adama ne ya fara fitowa yayin da waɗannan halittu suka miƙe tsaye suna jujjuyawa kamar wanda suka shiga filin rawa. Can kuma sai ga wata walƙiya mai mugun gaske da ta haska illahirin dajin. Lokaci ɗaya waɗannan halittu suka nutsu, wasu baƙaƙen kujeru da ba zaka iya tantance da ƙarfe ko roba aka yi su ba suka bayyana a bayan kowa, nan suka zauna damas yayin da wannan halitta ɗaya dake gefe wata narkekiyar kujera ta iso bayanta, ita ma zama tayi, nan dai halittun suka fara wani kuka wanda zamu iya siffanta shi da Yaren da suke yi. Can bayan wasu daƙiƙu shiru ya wanzu.

Kwatsam!, babu zato ba tsammani wannan shugaban da ba zamu iya tantance jinsinsa ba ya fara magana irin ta mutane, abun al'ajabi ma a wurin cikin harshen Hausa. Muryar dai irin ta mutane ce amma tana fitar da wani amo na musamman wanda ke bada sauti bibbiyu kamar dai echo.
“Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi! Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi! Jinjina ga Gutsirito dodon tsafi!!!”
A tare su ma suka amsa da “Jinjina! Jinjina!”.

Shiru suka yi sannan shugaban ya ɗaura da faɗin “Ba komai ya tara mu a wannan waje ba sai don wata muhimmiyar sanarwa da nake son kai wa gare ku a matsayi na ta uwargijiyarku!”
“Jinjina! Jinjina!!!” suka amsa mata cikin haɗin baki tare da ɗaga hannayensu masu ɗauke da Zara Zaran faratu masu kama da duwatsu baƙaƙe ƙirin da su.

“Akwai wata masifa da ke tunkaro wannan ƙungiya ta Devil Klans 👿, Wanda idan muka yi sake zamu iya rasa dama da ta rage mana, ƙarfin tsafi da muke da shi a duniya zai raunana, zamu rasa ikon mu! Kai mu kanmu in wannan masifa muka barta ta iso akwai tashin hankali! Don kuwa sauran ƙungiyoyi zasu yi ta kawo mana farmaki yayin da mu kuma bamu da ƙarfin kare kan mu, ku sani in dai bamu tsayar da ita ba to kowa zai yi galaba a kan Devil Klans 👿!”
Surutunsu ne sama sama ke ɗan tashi yayin da shugaba wacce ta ambaci kanta da uwargijiya tayi tsit tana jira ta ji daga gare su.

Ganin lokaci na ƙure musu gashi babu wanda ya faɗi wani abu yasa ta buga sandar da ke hannunta a ƙasa, wani irin sauti da sandar ta bayar tare da fidda tartsatsin wuta yasa dukkansu yin shiru. Magana ta fara tana faɗin “Ina jira daga gare ku, Ɓurum me zaka ce?” ta idasa tana nuna wanda ke a farko ta ɓangaren hagu.

Ƙasa yayi da kai sannan ya sauƙo tare da sujjada a gabanta kana ya ɗago, cike da girmamawa ya ce “Uwargijiya ki ƙara mana haske a kai, wace irin masifa ce haka ke tunkarar tawagar mu?”
Ba tare da ta kalle shi ba tana mai ɗaura jafarta kan ɗaya ta ce “Ɓurum yayi abunda ya dace! Dodon tsafi yana alfari da kai” ta faɗa tana ɗaura hannunta kan goshi.
“To bari nayi muku filla filla, ɗazu na gana da Shastuna Aminiya ta wacce ita ma shahararriya ce a duniyar tsafi shine take sanar da Ni cewa haske na ya fara disashewa! Idan nayi wasa kuma kungiyar mu na shirin halaka!.

A tsorace na koma gida bisa mayafin tsafi kai tsaye fada ta da ta kasance ta sirri na shiga, ina buɗe madubin tsafi a nan na tabbatar, akwai wasu haske guda biyu da ke shirin tunkaro mu, sai dai kuma duk hanyar da zan bi na gano jinsin waɗannan haske ya faskara, abun da dai na gano shine ɗaya na ƙarfafan ɗaya ne, kuma waɗannan ruhi biyu suna gab da ƙarasowa gaban mu, idan bamu dakatar da su ba kuma za'a samu matsala, ya kamata tun wuri mu toshe duk wata hanya da zata sada mu da su, mu rufe kowacce kafa da zata basu damar tunƙarar baƙin daji. Dodon tsafi na a tare da mu!” ta ƙarasa tana ɗaga murya wacce sautin ta ke fita kusan takwas takwas from every direction.

“Ye! Dodon tsafi na a tare da mu!”
Suka haɗa baki suna bata amsa. Cike da jarumta ɗaya daga cikinsu tace “Tabbas dole mu tsinkayo wannan ruhika guda biyu sannan mu datse gudirinsu ga Devil Klans 👿 cikin ikon Gutsirito dodon tsafi!, amma kafin nan, ya ke uwargijiya!” sai ya yi sujjada gabanta ya tashi “Ki bamu dama mu mu bincika daga nan sai a san yadda za'a ɓullowa al'amarin. Gobe in an fito meeting sai kowa ya faɗi ya yake tunanin zamu yi, in so samu ne ma a ce kowa yayi matsanancin bincike mu gano waɗannan ruhika biyu kafin mu ɗau mataki kan su!”

Cike da gamsuwa uwargija ta furta “Dodon tsafi ya ƙara kasancewa tare da kai Muƙal! Ka cika magajin Devil Klans 👿, Ka ƙara ƙaimi wajen ƙara gina kanka, dodon tsafi zai yi alfahari da kai!”

A haka dai suka kawo ƙarshen meeting ɗin nasu ba tare da wata kafaffiyar matsaya wacce zata ɓulle musu ba. Daga nan kuma wannan duhu ya ƙara mamaye dajin, tsawon daƙiƙu biyar sai ga haske, waɗannan halittu kuma babu su babu alamunsa, they'll disappear.

_wannan kenan!_

*Oxford University of London*

Zaune yake a katafaren room ɗin shi kaɗai, babu abun da kake ji a ɗakin sai sauƙar ajiyar zuciya da yake sakewa lokaci zuwa lokaci kamar karamin yaron da ya gama shan kuka.
Saraki kenan!, yayi nisa cikin tunani wanda ya manta cewa a duniyar ma yake.

Cikin ransa babu Abun da yake tunani sai irin badaƙalar da ke cikin gidan nasu,gidan da ya zame masa tamkar baƙin kurkuku, gidan da yake jin ina ma bai kasance ɗaya daga ciki ba.
“Shin me yasa ƙaddara ta tazo da haka?, me yasa rayuwa ta ta kasance haka?, na gaji! Na gaji da wannan rayuwar, ina son samarwa Kai na cikakken ƴanci ko ma yaya ne! Ina so nima nayi rayuwa ba tare da wani ciwo ko nauyi a zuciya ta ba.”

Khalil da ke tsaye kansa ne ya jijjiga kansa cike da tausayawa ɗan'uwansa kuma amininsa, how he wish yana da yadda zai yi ya samar masa mafita, but babu!. Cike da kulawa ya durƙusa gabansa ya kamo hannayensa biyu ya haɗa da nasa. Cikin raunatacciyar murya ya ce
“Sadauki! Ya kamata a ce zuwa yanzu ka cire wasu damuwoyin cikin ranka, kowa da kake gani da yadda Ubangiji ke jarabtarsa, ka ƙara haƙuri, addu'a ita ce kawai makaminmu mu, ba kai kaɗai abun ya shafa ba Sadauki, mu ma nan duka family ya shafe mu, amma addu'ar da ake fadi kullum dole dai ita ɗin ce zamu riƙe, Allah ya kawo mana sauƙi cikin wannan rayuwa ya kuma sanya salama da nutsuwa cikin ahalinmu”

Runtse idanunsa da suka yi masa jajir kamar gauta yayi, zuciyarsa na wani irin tafasa, cikin rauni da kuma damuwa ya furta “Amin Dude, ina tsoron wata rana wani abun ne ya faru da tsofaffi da yaran da basu ji ba basu gani ba! Ina tsoron wani abu ya faru da su, Khalil in wani abu ya faru da su ba zan taɓa yafewa kaina ba, Ni ne sila Khalil! Mine sila!...” sai kuma ya dafe kansa da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya dafe ƙirjinsa da ke masa nauyi da zafi kamar an ɗaura masa karfen da ya shekara cikin razanannnen garwashi.

Da sauri Khalil ya miƙe, a zabure ya fara jijjiga shi sai dai attack ɗin da ya samu ɗin ya hana shi komawa daidai!, rungume shi Khalil yayi yana ƙara jijjiga shi, ya ma rasa me ya kamata yayi a daidai wannan lokaci. Hawaye ne suka fara zubo masa kamar ƙaramin yaro, har a lokacin kuma bai daina jijjiga Sadaukin ba wanda babu alamar numfashi ma a tattare da shi
“Don Allah Dude Ka tashi, ka tashi don Allah, kar ka bari baƙin cikinsu ya kashe ka su basu da asara, don Allah ka tashi ka tashi!”

Ganin dai Sadaukin ya ƙi yin ko da motsi yasa ya ƙara shiga wani matsanancin yanayin. Ya rasa ina zai sa kansa ciki ma, ƙarar shigowar saƙo yasa ya tuna da waya, da sauri ya sa hannunsa ya janyo wayar sannan ya shiga nemo numbern Doctor ɗin Sadauki da ke London. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cikin harshe Larabci ya sanar da shi halin da suke ciki shi da patient ɗinsa. Bai tsaya bashi amsa ba ya katse ƙiran.

A haka Ya Khalil ke jijjiga Sadaukin har tsawon mintuna goma. Ƙarar doorbell yasa ya zame shi daga jikinsa da sauri ya nufi ƙofar, yana buɗewa ko jiran ganin waye bai yi ba ya koma wurin ɗan'uwansa. Cike da tausayawa Dr. Arƙam wanda ya kasance balarabe ke kallon Ya Khalil ɗin ganin yadda duk ya firgice lokaci ɗaya, ɗaya ɓari na zuciyarsa kuma na ƙara jinjina ƙarfin so da kuma alaƙar jini da ke ɗawainiya da matasan biyu.

Murmushi kawai yayi shima yana mai tunawa da nasa ɓangaren rayuwar sai kuma ya shiga cikin ɗakin da sauri, First Aid kit nasa ya ajiye sannan ya nufi Sadauki da ke kwance kamar gawa. Shi kansa Dr. Arƙam ya gama sarewa da al'amarin patient ɗin nasa, zuciyarsa tayi rauni gani yake kamar zai rasa wannan patient ɗin da tunda ya fara aiki bai taɓa jin so da ƙaunar da yake yi masa ya taɓa bawa wani ba.

Da sauri ya fara fitar da kayan bada agajin gaggawa, CPR yayi ya kai sau biyar amma numfashin Sadauki bai dawo ba, nan shima zuciyarsa ta sare, hope ɗinsa kenan, tunanin me zai ƙara yi yayi amma ya kasa tunawa ga kuma Ya Khalil da ya tsare shi da ido yana jiran yaga ɗan'uwansa na numfashi. Haka dai Dr. Arƙam ya ci gaba da yi masa CPR ɗin amma shiru, tsoron da Dr. Ke ɓoyewa ne ya bayyana har hawaye na silalowa daga idanuwansa.
Chapter 4 · 0% Book details