← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 46

Sashe 27

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai dama haka so yake? Haka so yake dama? Idan haka so yake baya yi wa wasu mutanen adalci a rayuwa duba da yadda yake kai su ga rasa jin daɗi, da yawa sun rasa nutsuwarsu saboda so, wasu sukan rasa hankalin su su koma tamkar mahaukata, wasu sukan rasa dukiyarsu da muƙamin su saboda so, wasu kuma iyalinsu da abokai kan juya musu baya dalilin so, so so! Wasu kuma sukan rasa wani sashe daga jikinsu, wani so kan zama sanadiyyar makancewarsa, wani kuma sanadiyyar kurumcewarsa, wani sanadiyyar rasa ɗanɗanon bakinsa wani kuma kan rasa rayuwar sa gaba ɗaya. Tabbas so cuta ce ga duk wanda bai yi dace ba ko kuma ɗaya daga cikin abubuwan nan suka same shi silar sa.

Miƙewa Yaya Ishaq yayi da ƙyar saboda yadda yake ganin dishi-dishi, wayarsa ce ta nuna buƙatar agaji yayin da sautin ringing ɗin ya karaɗe ɗakin, waƙar Saleem Smart ne dai-dai wurin da yake cewa.
Haka so yake dama, ya maida kai bawa.......

Sauraran waƙar ya ci gaba da yi har ƙiran ya yanke.

_Flash back_

Masu karatu za su ce tun da Yaya Ishaq ya tafi bai ƙara neman Zahrah ba tsawon waɗannan shekaru! Abun da ya faru shine, bayan tafiyarsa karatu bai taɓa mancewa da Zahrah ba tsawon wannan lokaci, kullum cikin tunani da kewarta yake ga shi ba shi da wani abu nata da zai ɗebe masa kewa sai pictures ɗin ta guda uku.

Bayan ya kammala karatu kuma Daddynsa tare da Mom ɗinsa suka yi residing a can saboda hare-haren da ake kaiwa mahaifin nasa, ya kuma kafa masa dokar babu shi babu Nigeria har sai In tare za su je, shi kuma ba shi da ranar zuwa.

A haka soyayyar Zahrah ta ci gaba da kama zuciyarsa har ta kai ga ta yi masa kamun da ba zai iya cire kansa ba, tun yana ɓoyewa har abun ya fara yawa har da su kwanciya jinya.

Wannan karon ma ganin in har ba su bar shi ya zo ya ga angel ɗin sa ba za a samu matsala saboda likitan da je kula da shi ya sanar da su lallai in ba a Masa abun da yake so ba zai iya rasa ransa.

Hakan ya sa babu shiri Daddynsa yayi booking Musu flight suka diro Nigeria duka kuma sauƙa gidansa da ke GRA, a ranar ya so ya tafi don ganin Angel ɗin sa amma suka ba shi haƙuri ya bari sai washe gari.
Wannan shi ne taƙaitaccen bayanin abun da ya faru bayan tafiyar ya Ishaq.

_To the story...._

*SADAUKI'S POV*

Tunda Alhaji Baba ya gama magana ya sulale ya bar parlourn ba tare da sun kula ba, kai tsaye part ɗin su ya wuce don ya kwanta in b haka ba yada zuciyarsa ke wani irin mahaukacin bugu da sauri da sauri ba lallai gangar jikinsa ta iya ɗaukar sa ba, the amazing part of it is that Sam ba ya so ko kaɗan iyayensa su fahimci cewar kawai sadaukarwa ce yake son yi musamman Alhaji Babba, wanda duk cikin gidan babu mai ƙaunarsa kwatankwacin yadda yake kai har mahaifin da ya haife shi, idan har ya fahimci baya so to tabbas auren nan sunan sa an fasa.

Ko wankan da ya saba yau bai yi ba, kan Bed ɗin sa ya faɗa yana dafe saitin heart ɗin sa, ba zai ce ba ya son auren ba sai dai kuma yana jin wani iri, yana ji kamar akwai wata zuciyar da ta fi buƙatar aurensa fiye da Mabruka, yana jin anya ya yi wa wannan zuciya adalci?.

“Who's that person?” ya tambayi kansa. Tashin mafita ga kuma tunani da ya sa shi gaba kamar ya haukatar da shi yasa ya miƙe a daddafe ya shiga toilet tare da ɗauro alwala. Nan ya yi ta jera nafilfilu ba adadi yana kai kukansa ga mai sama tare da neman ya masa zaɓi mafi alkhairi.

*MAMI*

Da yake duk matan babu wanda ya san da dawowar Abba ko da ya shigo a main parlour ya sauƙa, lokacin kuma dukka matan na zaune a parlourn kowacce ta hakimce sai hura hanci take.

Small Mom dama can ita ta iya kula da miji da sauri ta miƙe tana masa sannu da dawowa, shi ma ya amsa, ganin dai Mami ko alamar furta A ba ta da shi yasa ya jijjiga kansa yana mata addu'ar shiriya.

“Baraka!” Abba ya ƙira sunanta
Ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta mayar da kanta.
“Kina gani na amma ko sannun da dawowa babu? Kina ganin hakan daidai ne?”
“Haba Abban Faruq, ya za a yi ka titsiye Ni gaban wannan matar hakan daidai ne?”

“Ka ga Alhaji na, ka ƙyale ta kada ta ɓata maka ranarka while you look so happy I can see, mu je ka watsa ruwa ka ci abinci.”

“To ƴar'iska! A gaba na kike karuwancin naki ko? Hehehehe! Sai ki faɗa min wane dare ne jamage bai gani ba!”

Small Mom ba ta bi ta kanta ba ta ja hannun mijinta ta bar Mami sai harare harare take tana magana ita ɗaya kamar mahaukaciya.

Ba ta bar parlourn ba kuma sai da ta suka fito. Nan taji Abban na faɗawa Small Mom cewa an saka bikin Sadauki da Mabruka, sosai ta yi murna yayin da Mami ta miƙe tsaye a zafafe tace
“Ba zai yiwu ba! Dole na tarwatsa auren nan don Sadauki ba shi da matar da ta wuce Kausar”

Kallon ba ki da hankali Abba ya cilla mata sannan yace
“Dama can ke ba hankali gare ki ba Baraka, sai ki tarwatsa auren, nace bismillah ki tarwatsa auren in kin cika ƴar halak” rai ɓace kuma ya wuce zuwa turakarsa da ke jikin main parlourn.

Da harara Mami ta bi shi tana faɗin
“Zan kuwa tabbatar maka Ni na cika Baraka Abban Faruq!”
Cike da mamaki Small Mom ke kallonta sannan ta miƙe tsaye tana faɗin
“To iyayen haddasa, a dai sano hassada ga mai rabi taki ce! Mtsss” daga haka ta bi bayan Abba. Ita kuwa Mami kamar mahaukaciya ta fice ta nufi part ɗin ta tana tunanin ta ya za ta yi ta tarwatsa wannan aure!

*Ammie*

Wani lukutin bala'i, Part ɗin Papa ma dai haka aka gwabza bala'i don Ammie rasa nutsuwarta ta yi bayan jin bayani daga bakin Papa, ita dai Mimie fatan alkairi tayi musu tana nuna tsantsar farin cikin ta, tun da Papa ya ga yadda ta yi reacting tare da ficewa a hasale ya sa Ayar tambaya kan ta.

Haka ta faru a sauran sassan gidan kuma ko ina shigen abun da ke faruwa, sauran matan da ba su ƙulli kowacce da sharri ba taya su murna tare da musu fatan alheri.

*Hajiya Babba*

A lokacin da Alhaji Babba ya shigo gidan fuska sake ya tadda su a main parlourn gidan ne saɓanin sauran sassan gidan, a nan hirarsu suke gaba-dayan su, yaran kuma na wasan su.

Shigowarsa yasa yaran suka nutsu, ƙananan cikin su suka rungume shi suna oyoyooo Alhaji. Da farin ciki ga amsa musu sannan ya yi wa kansa mazauni a parlourn, nan duk matansa suka masa sannu da dawowa.

Hajiya Babba ya kalla yace
“Ina Mabruka ne?”
Hajiya Amina da ta kasance uwar ɗakin ta tace
“Tana ciki, Meerah, maza kira Auntynku ki ce mata Alhaji na kiranta.”
Da gudu ta zuwa parlourn Hajiya Amina don kiranta.

Kallonsa suka yi ganin yadda fuskarsa ke nuna farin ciki Hajiya Karima ta ce
“Babbansu yau dai alamun kana cikin farin ciki” ta ƙarasa cikin sigar zolaya.
Murmushi yayi yana faɗin
“Ba shakka, ina cikin farin ciki maras musaltuwa.....” katsewa yayi sakamakon shigowar Mabruka parlourn wacce ta tsugunna gabansa kan ta ƙasa.
“Sannu da dawowa Alhaji, An yini lafiya?”
Fuska sake ya amsa mata da
“Lafiya ƙalau Mabruka, ya aikin?”
“Alhamdulillah” ta ba shi amsa. Shiru parlourn ya ɗauka na wani lokacin kafin Alhaji Babba ya gyara zamansa tare da gyaran murya.

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
_Yanzu ma aka fara! Yanzu ma aka fara, kuna jin wata lukurar Masifa kuwa people? Gaskiya akwai ban tausayi sosai musamman ga love birds ɗin nan, fatan mu Allah ya sa abun ya zo da sauƙi._

*Masoya littafin A babban Gida musamman followers ɗin ~DBRC~ waɗanda ke ƙarfafa min guiwa da reacting wadda ke nuna zallar soyayyar su gare Ni da alƙalami na ina godiya, alkhairin Ubangiji ya kai gare ku a duk yadda kuke, tabbas ina ƙaunar ku ƙauna ta gaskiya kuma saboda Allah.*
*Sannan waɗanda ke min comments daga wasu groups ɗin da kuma na musamman masu min ta PC Allah ya saka muku da alkhairi, kar ku manta ko yaushe ƙofar gyara a buɗe take Habibties, zaku iya samu na kai tsaye ta +2347061707238 ina godiya sosai*
*Love You all.*

[1/11, 7:14 PM] Diamond Bhatool:

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_

_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 2️⃣1️⃣

_For those willing to be updated about this book should kindly follow my channel, a can kaɗai nake update yanzu._

                                  ﷽

“Hajiya Ruƙayya, Hajiya Karima da kuma Hajiya Amina.”
“Sai kuma ke Mabruka na tara ku ne a nan ba don komai ba sai don na sanar da ku abun farin ciki da ya tunkaro mu.”
Gaban Mabruka ne ya bada wani irin sauti mai karfin gaske wanda har fuskarta sai da ta bayyana hakan. Babu wanda yace komai hakan ya ba wa Alhaji Babba damar cigaba da jawabinsa.

“A matsayin ku na iyaye ga yarinya ina fatan za ku yi farin ciki da abun da zan faɗa, ke kuma Mabruka” ya nuna ta da hannunsa wanda har lokacin kanta ke duƙe.
“Ina fatan za ki biyayya a kan wannan hukunci.” nan gabanta ya ƙara bugawa

“A yau Alhaji Baba ya yanke auren Mabruka da kuma Sadauki cikin makonni biyu masu zuwa in Sha Allah, sai ku fara shirye-shiryen bikin, zan tura muku kuɗi ta a account ɗin Ruƙayya, In da buƙatar ƙari sai ku min magana.
Chapter 27 · 0% Book details