← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 46

Sashe 28

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta ɗago jajayen idanuwanta ta dubi Alhaji Babba ta furta “Allah ya Ƙara girma Alhaji.” daga haka kuma ta bar parlourn da gudu har tana shirin faɗuwa sakamakon karo da Humaira da suka yi. Da kallon mamaki Humaira ta bi ta wondering why is Aunty Mabruka acting so strange, Nan ita ma gaban ta ya ba da wani irin sauti, daga nan ta ƙaraso, a lokacin su Hajiya Babba duk sun tashi, iya su Meerah ne zaune. Fuska ɗaure Humaira ta kalli Meerah tace
“Meerah me ya samu Mabruka?”
Meerah ta amsa mata da
“Albishir Aunty Humaira! Saura sati biyu bikin Aunty Mabruka da Yaya Sadauki.”

Gaban Humaira ne ya ba da wani irin sauti, bata tsaya idasa jin zancen Meerah ba ta wuce Bedroom ɗin Hajiya Babba da sauri yayin da numfashin ta ke kokawa don ya bar gangar jikinta.
Da taimakon Allah ta idasa shiga, yanayin yadda ta tura kofar ne ma ya sa Hajiya Babba juyowa don ganin waye. Yanayin da ta ga Humaira ya ɗaga mata hankali amma sai ta dake tana bin ta da kallo har ta iso wurin da take. Kanta ta ɗaura kan cinyar Hajiya Babba tare da fashewa da wani irin azababben kuka.

Cike da kulawa Hajiya Babba ke shafa bayanta ba tare da ta ce mata komai ba, sai da ta yi kukan ta ta fara sauƙe ajiyar zuciya tukun Hajiya Babba ta ɗago ta yayin da fuskar su ke kallon ta juna.
“Lafiya Humaira?” kamar jira dama take taji an tambaye ta sai ta ƙara fashewa da wani kukan, ba tare da ta yi shiru ba ta fara magana wacce ba a gane me take faɗi.
“Kin ga calm down Humaira, faɗa min me ke damun ki Please!” Hajiya Babba ta faɗa cikin wata raunananniyar murya
Ɗagowa Humaira ta yi tace
“Hajiya nima wallahi ina ƙaunarsa, kuma wallahi In ba a aura min shi ba zuciya ta bugawa za ta yi na mutu.”.

Tashin hankali, a gigice Hajiya Babba ta ce
“Ba za ki mutu ba Humaira, a kan waye kike magana? Ko waye dole ya aure ki tunda kina son sa, tell me who's that person da har kika mace kan sa”

“Hajiya Yaya Sadauki!...”
Bata bari ta ƙarasa ba ta tura ta gefe tana bin ta da wani irin kallo.
“Lallai Humaira ba ki da hankali ma, mijin ƴar'uwar taki kike so? Abun hauka ne aka ce miki?”

A raunane Humaira tace
“Haba Hajiya, Ni na ɗaura wa zuciyar tawa son sa ne? Allah ne fa ya halicci zuciya ta da son sa, na girma da son sa sai yanzu kawai za a raba Ni da shi? Ba a min adalci ba kuwa” raunin da Muryar ta tayi yasa ta dakata ta juya za ta fice daga ɗakin tana kuka.

“Wait, come here Humaira!” Hajiya Babba ta dakatar da ita, ba musu ta koma bakin Bed ɗin ta Zauna.

“Humaira haƙuri za ki yi kawai, Alhaji Baba ne ya yanke wannan hukunci. Da a ce ma ita Mabrukan akwai wani tsayayye a wajen ta za a iya dakatar da auren amma babu.”
“Hajiya Aunty Mabruka ba ta son Yaya Sadauki, she never get even a single feeling for him, in fact tsawon rayuwa ta da ita ban taɓa jin ko sau ɗaya ta yaba kowa ba sai Captain Hisham wanda tun ba yau ba suke tare, meyasa kuke son raba ta da farin cikin ta? Hajiya don Allah kar ki bari na rasa Yaya Sadauki, idan hakan ta faru I'm useless, ba Zan amfanu ba don ƙarshe ma dai I'll lost my life and....”

Da hannunta ta toshe bakin Humaira tana jijjiga kanta
“A'a Humaira, U won't lost your life saboda namiji, ba za ki mutu ba Humaira, ki yi haƙuri kin ji, zan duba naga yaya abun zai kasance, go and sleep now.” ba tare da ta ce komai ba ta fice sai sauƙe ajiyar zuciya take. Nan ta bar Hajiya Babba cikin kogin damuwa musamman da abun ya kwaɓe mata amma to Allah we belong, sai ta ƙara roƙon sa da ya kawo agaji.

*MORNING*
*Zahrah's POV*

A hankali ta fara motsa yatsun kafafuwanta wanda take jin kamar an ɗaure mata su, can kuma ta fara kiciniyar buɗe idanuwanta da suka yi mata wani irin nauyi, da ƙyar ta iya buɗe su tana mai bin parlourn da kallo sam jikinta babu Kwari ko kaɗan, a haka ta fara ƙoƙarin miƙewa tana tunanin what makes her so dull today. Nan ta fara tariyo daren jiya, da sauri ta koma shagab ta kwanta tana ƙara rintse idon ta.
“Ya Allah!”
Ƙoƙarin miƙewa ta ƙara yi har sau uku tana komawa saboda yada jikinta yayi laushi, da ƙyar ta miƙe ta nufi toilet tana mai bin jikin gini. Bayan ta yi alwala ta yi sallar ta wacce a zaune ma ta yi ta tana mai roƙon Ubangiji da ya kawo wa rayuwar ta ɗauki. Alhamdulillah sai ta ji zuciyar ta ta ɗan yi sanyi ba wai don ta daina jin yadda zuciyar ke zafi ba, sai dai ta ji ƙarfin guiwar coping ma wannan bada moment ɗin da ya zo mata a ba zata.

Bata fita parlourn ba sai da Hajjaty tazo duba ta nan ta tarar da ita jikinta zafi kau, hankalin Hajjaty ta tashi matuƙa da sauri ta fita ta kwaso drugs da kuma abinci ta dawo. Sosai ta ba wa Zahrah kulawar da ta ɗan ƙara ɗauke hankalin Zahrah daga tuna wannan abu. Yinin ranar dai kusan tare suka yi.

Can wajen yamma Yaya Sadauki ya shigo Part ɗin, ko da ya tambayi Laraba nan ta kora masa bayanin ai Zahrah ce ba ta da lafiya Hajjatyn take wurin ta. Nan take zuciyarsa ta bada wani irin sauti, da sasaarfa ya ƙarasa zuwa room ɗin Zahrah, handle ɗin ya murɗa ya yi wa kansa iso.
Bayan sun gaisa da Hajjaty ya maida dubansa ga Zahrah, gaban sa ne ya faɗi saboda yadda ta rame kamar wacce ta shekara tana jinya.
“Hajjaty why ba a Kai ta asibiti ba? Bari na kai ta asibiti yanzu, look how she's been wasted!” ya faɗa a ɗan kiɗime yana kai hannunsa zai ɗauki Zahrah wacce take bacci.

“A'a ai ka bar shi ma Sadauki an, ta riga ta ji sauƙi” Hajjaty ta dakatar da shi. Noo ba zai iya ba, ba zai bar amanar sa a haka ba, dole ya kula da ita. Kamar bai ji Hajjatyn ba ya sunkuci Zahrah yayi waje da ita sai cikin mota, daidai lokacin da motar Ammir ta wuce ta wurin. Bai ma kula da su ba ya tayar da motar sai wani private hospital na Indians da ke kusa da estate ɗin. Abunku da ƙwararrun likitoci tuni suka karɓi Zahrah hannu biyu aka fara duba ta.

Har wajen ƙarfe 8:00 na dare ba su bari ya shiga kallonta ba don kuwa gwaje-gwaje sun kai shida aka mata. Can bayan sun kammala physician ɗin ya ce da Yaya Sadauki su je zai yi magana da shi, he's eager to know what's wrong with Zahrah ai da sauri ya bi bayan doctor ɗin. Bayan sun gaisa ya fara masa jawabi.

“Maras lafiyar da ka kawo yanzu haka bacci take don tana da buƙatar hutu sosai, zuwa gobe za mu sallame ta.” ya faa cikin harshen Ingilishi.
“To me yake damunta?” yaya Sadauki ya tambaya.
“Honestly speaking Mr. Kuna gab da rasa ta matsawar ba za ku ba ta kulawar da ya dace ba, at this her age ta Yi ƙanƙanta da samun heart attack, to be sincere with you in ba a ba ta kulawa to condition ɗin will worsen, thank God ma an yi diagnosing early.”

Cike da mamaki da kuma damuwa Yaya Sadauki ke kallon Dr ɗin, har sai da ya gama jawabin yace
“Ok Dr. Yanzu dai takamaiman shi me yake kawo Heart attack ɗin?”
Dr ya gyara zaman glass ɗin sa ya fara magana, bayan ya gama masa bayani nan Yaya Sadauki ya fice fuskarsa ɗauke da damuwa. Wayarsa ce tayi ringing da ba zai ma ɗaga ba sai kuma ya duba, ganin Dude ɗin sa yasa ya ɗaga, bai ce komai ba sai kuma can yace
“BHAAT SPECIALIST”
Can ya Kuma cewa “Ok”.

Reception ya koma ya zauna har Yaya Khalil yazo. Da yake su tsarin asibitin babu patient relatives, ba a zuwa dubiya saboda suna rendering care yadda ya kamata ga patient. Da ƙyar dai aka bar su suka shiga da sharaɗin kada su yi motsin da zai tayar da patient ɗin. Fitowar su kowa fuskarsa ta sauya wanda hakan ta yiwu yana da alaƙa da yadda suka ganta, daga nan suka wuce tare. Da suka isa sai da suka samar da Hajjaty tukun hankalin ta ya ɗan kwanta, da cewa ma tayi sai dai a kai ta taga Zahrah, da suka mata bayanin tsarin asibitin yasa ta haƙura.

Daga nan kuma Yaya Sadauki ya wuce Part ɗin su don yana bukatar hutawa, wanka ya yi ya Saka wasu soft pyjamas blue colour, kamar kullum yayi shafa'i da witr sannan ya nufi Bed ɗinsa, bayam ya Yi addu'a ya ja Blanket yana mai lumshe idanunsa. Tunani yake me yayi causing wannan sickness na Zahrah, he later concluded it as dalilin rashin Mama ne. Hakan ya sa ya ƙuduri aniyar da safe zai ƙara tunkarar abokin aikinsa Inspector Wada Usman kan batun.

Ba ita ta farka ba sai wuraren 3:00am, a hankali ta fara bin ɗakin da take da kallo, hannun ta ta ɗaga sai taji igiya like a jiki, da sauri ta mayar da duban ta ga hannun, zaro ido tayi ganin cannula ce ga Kuma wani ƙatoton I.V fluid da aka maƙala mata. Sai a lokacin ta fahimci cewa a asibiti take, gabanta ne ya faɗi don bata san ya aka yi ta zo asibiti ba, shikenan asirin ta ya tonu?
Chapter 28 · 0% Book details