← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 46

Sashe 2

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba kunya sai tsoron Allah haka ya miƙawa khalil ɗin wayar shi kuma ya wuce can cikin ɗakinsa tare da zubewa kan gadonsa.

******************************

*ABATCHA ESTATE*

Jerin motoci ne kusan biyar waɗanda dukkansu suka kasance na kallo suka Turo hancinsu zuwa katafaren estate ɗin, makeken gate ɗin guards suka buɗe, nan suka samu damar shigewa ciki. A mai flat wato ɓangaren tsoffin gidan suka yi parking motocin, nan suka fara fitowa.

Cikin waɗanda suka fara fitowa ne ɗayan su ya buɗewa Alhaji Baba ƙofar motar ya fito. Masha Allah, kyakkyawan dattijon ya tako da taimakon ɗaya daga cikin mutanen wanda ke tsantsar kama da shi. Haka sauran suka biyo bayansu zuwa cikin gidan.

Babu kowa a katafaren parlourn wanda ya kasance mai faɗi da yalwa sosai, Wanda ke riƙe da Alhaji Baba ne ya zaunar da shi kan kujerar sannan ya nufi wani ɗaki wanda ya ƙara tabbatar da cewa ɗakin Hajjaty ne. Ganinta zaune kan sallaya alamar dai sallar maghrib ta idar ya sa ya ƙarasa gunta yana risinar da kai ƙasa.
“Sannu da gida Hajjaty”
Ɗagowa Hajjaty tayi tana murmushi ta ce “A'ah Muhammad kun dawo kenan!” fuska sake shima ya amsa mata da faɗin “Eh Hajjaty mun iso kuwa yanzu”
“To bari na sa Laraba ta kawo muku abinci sai ku ci ko”
Ba tare da ya Musa ba suka fito tare da Hajjaty, sauran suma dake zaune ƙass suka miƙa gaisuwarsu ga Hajjaty, fuska sake ta amsa tare da ƙwalla ƙiran Laraba. Abinci ta jera musu kan dogon table da ke ɗauke da aƙalla kujeru hamsin sai kuma ta koma. Ganin lokacin Isha yayi yasa suka wuce masallaci kawai. Suna dawowa kuma suka baje abincin suka fara ciki.

Sai da suka kammala kafin Dattijo ɗazu (Daddy) yayi gyaran murya ya ce “To! Ɗazu fitarku wani baƙon al'amari ya faru har ya kai ga Hajjaty ta suma” sai kuma yayi shiru.
Zuciyar Abba har ta fara bugu don tunaninsa ko wani abu ya faru da matarsa ne da take da shegen jarabar tsiya.
“Akwai wata baƙuwa da ta kusa sati tana jele estate ɗinnan sai dai bata samu damar shiga ba sai yau. Kar na ɓata muku lokaci dai wannan yarinya kana ganinta ka ga jinin gidan nan, suna mugun kama da ƴar uwarmu ƙwaya ɗaya wacce ta ɓata shekarun baya.”

Zuciyarsu ce ta buga a tare kowa fuskarsa ta sauya musamman Alhaji Babba wanda duk cikinsu ya fi yin sabo da ƴar uwartasa kafin ɓatanta.
“Yanzu dai babu wani ɓata lokaci ko jan magana, ina ga za'a iya ƙiranta yanzu a ji daga bakinta daga ina take idan har ta tabbata jinin mu ce sai a haɗa taro gobe in Allah ya kaimu”
Kowa yayi na'am da maganar Daddy shi yasa Hajjaty da ɗauki da kuma anxiety suka lulluɓe ta ta ƙwalla ƙiran Laraba, nan ta sanar da ita tana son ganin baƙuwar ne ta ƙira ta.

*Me kuke tunani game da wannan labari mai cike da cakwakiya, ƴan uwantaka, munafurci, soyayya da kuma saran ɓoye (na billyn Abdul)*

*_Yanayin yadda naga kun amshi littafi na biyu ta hanyar yi min sharhi shi zai sa na ci gaba da muku typing babu ƙosawa, mutane na na channel kuma idan bana ganin reactions zan daina kawo muku shi baki ɗaya, sannan kada a mance ake taya Ni sharing zuwa wasu groups ɗin, wannan ma salon ƙauna ne, ina so saƙon ya kai inda ya kamata, ku sani DIAMOND BHATOOL taku ce!🤗😍😘_*

[12/10, 7:56 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎:
*_Typing 📲_*

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*

Wattpad: @diamond_bhatook
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._

*Chapter 1: Zahrah settled down at Abatcha estate*

*PAGE* 0️⃣2️⃣

_Sadaukarwa gare ku masoyan asali, boyayyu da kuma wanda suka bayyana a zahiri, Allah ya bar ƙauna Ameen_

*Masu Neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

*Join my WhatsApp group 1*
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66

*Join my WhatsApp group 2*
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB



Hajjaty da kanta ta ƙwalla ƙiran Laraba da ke kitchen, nan ta faɗa mata saƙon da zata isarwa Zahrah, ko da ta faɗa mata ta ja ƙofar ta rufe mata, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata yayin da wani irin fargaba da tsoro suka lulluɓe ta. Cike da ƙarfin hali ta miƙe tare da goge hawayen sannan ta nufi ƙofa.

Taron jama'ar da ta gani wanda mafi akasarinsu maza ne kuma da gani manya ne yasa ta ɗan dakata tana dafe ƙirjinta. Kanta ta sunkuyar ƙasa sakamakon jin Muryar Hajjaty tana faɗin “Ƙaraso nan yarinya”. Babu musu ta nufi wajensu zuciyarta ba bugawa da sauri da sauri, Dukkansu kowa idonsa a kanta yake hakan yasa har ƙafarta ta fara harɗewa kamar zata faɗi, a tare zukatansu suka buga sai dai maganar Alhaji Baba yasa duk hankaulansu dawowa gare su.

Hajjaty ne ta nuna mata gefenta sai dai ko da ta ƙaraso sai ta zame ƙasa ta zauna a kan carpet dai-dai ƙafar Hajjaty. Cikin murya mai ɗauke da zallar izza da nutsuwa Alhaji Baba yayi sallama suka amsa masa. Gyaran murya yayi yace.
“To ba komai ya tara mu nan ba sai batun da na riska bayan dawowa ta daga tafiya. Ɗan dakatawa yayi tare da mayar da dubansa ga Zahrah wacce kanta ke ƙasa a takure.
“Baiwar Allah kin zo cikin wannan ahali da abun al'ajabi sai dai mu nan bamu san ke wacece ba, idan babu damuwa muna son sani.” Ya idasa yana ƙara kallon Zahrah da yake ji kamar ya rungume ta saboda tsantsar kamanninta da ɓatacciyar yarinyar su.

Ba tare da Zahrah ta ɗago ba ta goge hawayen da suka zubo mata tare da jan hanci, “Da farko suna na Zahrah Abdulkarim Kuru, na zo ne tun daga jahar Bauchi saboda saduwa da ku. Ni ɗin a taƙaice ba kowa bace ga wannan ahali face jika!”
Gabansu ne ya faɗi jin furucinta, sai dai ita Zahrah murmushi kawai ta yi tunawa da baƙar ranar da aka rasa Mama.
“Eh Ni ɗiyar Madina ce, tabbas ita ce mahaifiya ta, tabbacin hakan kuwa shine kamanni na da ita, ban kwaso komai na mahaifi na ba sai yatsu.”
Nan dai ta fara basu labarin ɓatan Mama Wanda a ainihi guduwa tayi kamar yadda tayi mata bayani a kwanakin baya, guduwarta zuwa wurin Abbanta, auren su, haihuwarta, mummunan kisan da aka yi wa Abba, daga nan ta hau bada labaron auren Mama da kawu, wanda ya kasance dan uwa ga Abba, irin zaman auren da suka yi, har zuwa ɓatan Mama. Tuni jikinsu yayi sanyi gabaɗayansu. Hajjaty kuka take shaɓe-shaɓe tare da rungume Zahrar a ƙirjinta kamar wacce za'a ƙwace ta daga gare ta.
“Ni dama na sani, Madina ta na raye, gashi Allah yayi haɗuwarmu da tsatsonta kafin ita, amma wannan miji nata Allah yayi mugu wallahi sai ya san ya taɓo ƴar asali!”
Hanci ta fyace ta cigaba “Garba, Umaru, Usmanu, Gadanga, Muhammadu da kai Yusufu don Allah a ƙara ƙaimi wurin sanar da jama'a da kuma jami'ai har Allah yasa Madina ta dawo gare ni”.

Kowa jimami yake yi kuma jikin kow yayi sanyi sai dai ganin halin da Hajjaty ke shirin saka kanta yasa suka ɗan kawar da damuwarsu duk da cewa yanayinsu dama saisaitacce ne tunda sun samu tabbacin Madinar na raye.
Daddy wanda duk cikinsu yafi zafi ya ce “Tabbas wannan miji na Madina ya cutar da ruhikanmu, Wallahi sai ya san ya taɓo jinin ABATCHA, sai ya san ya taɓo ƴar Babban gida!”
Dafa shi Alhaji Baba yayi shima yana ƙoƙarin kawar da tasa damuwar
“Ya isa haka Umaru, ka kwantar da hankalinka yanzu abu mai muhimmanci shine kau haɗa kai ku bada himma a nemo Madina, shi kuma mijin daga baya ma san yadda zamu yi da shi.

Shawarar da Alhaji Baba ya basu kowa yayi na'am da ita, nan Alhaji Babba ya murmusa ya ce “Yaki yarinyar kirki, zo jikin babban uba ko?” cike da matsananciyar kunyarsu ta taho garesa, rungume ta yayi sannan ya sumbaci kanta kafin ya ce “Photocopyn Madina, Allah yayi Miki albarka Zahra'u.” da “Amin” Zahrar ta amsa kafin ta nufi sauran jama'ar da ke Parlourn suma ta kwashi albarka. Kasancewar lokacin sallah ya ƙarato daga nan aka rufe ɗan ƙaramin zaman da Addu'a, nan mazan suka fice zuwa mosque da ke cikin estate ɗin.

Ko da suka fita Hajjaty da fara'a ta ƙara rungume Zahrar, tsawon wasu daƙiƙu kafin ta sake ta tana tsura mata ido. Cikin ranta tana ƙara tausayawa rayuwar da ahalinta da Kuma bar soyuwarta Madina tayi, sai kawai ta yi murmushi cike da son kawar da damuwarta ta ce “Muje can ɗaki na kiyi Salla Zahrah, idan Laraba ta zo ta kwaso Miki kayanki” Kan Zahrah ƙasa ta ce “To Mama” Hararar wasa Hajjaty tayi mata tana riƙe da hannunta tace “ki ƙira ni Hajjaty kamar yadda kowa cikin estate ɗin nan ke kira na, kinji?”
“Eh Hajjaty ” ta bata amsa har lokacin bata sake ba.

Sallarta ta maghrib ta gabatar shimfiɗa ɗaya da Hajjaty, zuciyarsu tana ƙara kusantuwa da juna, bayan sunyi Sallar Hajjaty ta fara ɗauke Zahrah da zance, tun tana bata amsa a kunyace har dai ta sake suna Hira, ko da Alhaji Baba ya dawo, babban Parlourn sa suka wuce kamar yadda Hajjaty ke yi koyaushe. A nan dai Zahra ta saki jiki da ƴan kakannin nata da suka fara mantar da ita duniyar ta hanyar ɗumbun kulawa da so da suke nuna mata cikin sa'o'i ƙalilan.

Wannan kenan.

Lokacin Isha da yayi ne Alhaji Baba ya fita daga gidan zuwa Masjid tare da rakiyar Daddy. Su Zahra a nan suka yi sallar su kowa ya nuna godiyar sa ga Ubangiji, nan suka yi addu'a Allah ya bayyana Mama. Ko sallayar basu naɗe ba Maid ɗin Hajjaty, Laraba, ta shigo hannunta ɗauke da wani dogon tray wanda ke shaƙe da kuloli shaƙe da. Kuma jugs.
Chapter 2 · 0% Book details