← Book details A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 46

Sashe 13

A Babban Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar shi ya fitar sannan ya kara a kunne alamar dai kira yayi, can kuma ya sauke tare da kallon gefensa. Tun kafin ya ƙaraso Alhaji Baba da ke tsaye ya ƙarasa gare shi tare da rungume shi.

“Nayi kewarka sosai”
Ya faɗa can kasan maƙoshi.
Sake shi Alhaji Baba yayi jin Muryar ya Khalil yana faɗin.
“Tare da Ni fa muke tafe.”
Shi wallahi tsabagen farin cikin ganin Sadaukin sa yasa ya manta ma da cewa tare da Khalil suke. Murmushi irin na manya yayi yana faɗin “mu samu mu wuce gida ku huta ko?”

Kai suka gyada, nan ya Qasim da ke tsaye yana kallon su gwanin ban sha'awa ya wuce zuwa wurin da motar su tayi parking, nan yaya Khalil ya shiga front seat, su kuma Alhaji Baba da Sadauki sa suka zauna gidan baya.

Kai tsaye estste ɗin su suka nufa, bisa umarnin Alhaji Baba suka tsaya a ɓangaren su. Bayan sun daidaita parking suka dunguma baki dayansu.

Babu kowa a parlourn hakan yasa duka baje kan kujerun da ke parlourn yaya Khalil na korafin wai ya gaji Alhaji Baba da ya Qasim sai dariya suke masa. Hayaniyarsu yasa Hajjaty fitowa da sauri don tabbatarwa kanta cewa su din ne.

Ganin da gaske su ɗin ne yasa ta ƙarasa wurin nasu tana sakin kukan farin ciki na ganin shalelen jikanta. Da sauri duka suka juyo suna kallon ta. Cike da zolaya yaya Khalil ya ce “Ya da kuka kuka Hajjaty, gaskiya zan sa ɗan'uwa na gaba mu koma tunda baki farin ciki da zuwan mu”

Dariya dukkansu suka yi banda Hajjaty dake hararar Ya Khalil ɗin sannan ta ƙaraso gefensa ta zauna tana faɗin “To ja'iri ku koma mana”

Yaya Khalil ya ce “Ai don ina tausayin halin da zaki shiga ne In na ɗauke miki shi da kin ga aiki da cikawa ”
Ya idasa yana mata gwalo.

Danƙwalon sa tayi tana faɗin “ kaga Ni ban Don kai na fito ba” sai kuma ta mayar da kallonta ga ɓangaren da Yaya Sadauki ke zaune fuska babu yabo babu fallasa
“Ga don wanda na fito ”.

Nan suka kwashe da dariya bako dayansu , daga nan kuma aka fara gaisawa. Sai a lokacin Hajjaty ta tuna da Zahrah da ke kunshe can a Bedroom dinta.
“Zahra'u Zahra'u” dim dim zuciyarsa ta buga jin bakon sunan da Hajjaty ta ambata sai kuma ya waske yana tunanin ko sabuwar mai aiki ce.

Ɓangaren Zahrah ta ji shigowar su har ta mike zata fito sai kuma ta gargadi kanta ta koma yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Ko da Hajjaty taji karar rufe kofar sai kawai tace “Ki kawo ma su Yayanku abun sha ko?”

Ta gefen ido yake kallon mai fitowa daga wannan dakin, haka kawai yaji gabansa na faduwa da fitowar ta sai kuma yake ji a ranar yana biɗar kallon wannan sabuwar mai aiki. Tunanin sa ya katse nr jin kalaman Hajjaty na Yayanku, sai kuma zuciyarsa ta fara raya masa ko dai cikin ƴan matan gidan ne.

Tunanin sa ya katse ne yayin da sallamarta wurin ta rike dodon kunnuwansu. Zuciyarsa ne ta bada Wani sauyi Na daban sai dai a zahiri ba zaka fahimci hakan ba saboda hankalinsa kwacakom ya mika shi ga wayar da yake dannawa.

A ɓangaren yaya Khalil shi ma abun da ya faru kenan, sallamarta yasa yayi saurin ɗagowa don ganin wacece, shi dai iya tsawon rayuwarsa bai taɓa jin makamanciyar wannan Muryar ba a fadin estste ɗin su.

Kan ta ƙasa ta ƙaraso tana ajiye babban jug ɗin da ta zuba zoɓon da ta yi dazu. A sanyaye ta furta
“Sannun ku da hanya, ina yini”

Baki sake yaya Khalil ke kallonta yayin da zuciyarsa ke tunanin wacece wannan, sai dai kamarta da ya gani ya sa ya tabbatarwa kansa cewa jininsu ce. Ɓangaren yaya Sadauki ma haka abun take, sai dai shi babu wanda zai san cewa kallonta yake yi.

Yaya Khalil ne yayi ƙarfin halin amsa mata da “Yauwa sannu, lafiya kalau.”
Without minding his response ta fara zuba zoɓon a cups Tana Mika musu. Sai da ta sakawa kowa har su Hajjaty da Alhaji Baba kafin tayi yunkurin zuba nasa taji Muryar yaya Khalil yana fadin
“Ki ɗaukowa man drink coz ba lallai ya iya shan wannan ba.”

Da “To” ta amsa tare da ajiye cup din hannunta tana kokarin juyawa muryarsa ta daki kunnenta “No bar shi, serve me wannan ɗin.”
Ba iya Zahrah ba Kowa na parlourn kallon mamaki yake masa don iya saninsu dai baya son home made drinks shi kuwa ganin haka yasa ya kara maida hankalinsa ga wayarsa sai dai shi ma he's eager to know who is this lady don ya tabbatarwa kansa cewa ba mai aiki bace ganin yadda take zubi da famoly members don musamman Hajjaty, zai iya cewa photocopyn ta ne.

Kai kasa Zahrah ta juyo sannan ta dauki cup ta zuba tare da mika masa, tsawon wasu daƙiƙu tana shirin kara ce masa ga shi ya miƙo kyakkyawan hannunsa ya amshi cup din. Tana shirin komawa Hajjaty ta dakatar da ita
“Ina kuma zaki je Zahrah?”
“Zan koma ne ina karatu ne” ta bata amsa kai tsaye.

Alhaji Baba ya ɗago ya kalli Zahrah kafin ya ce “Dawo ki zauna ƴa ta gari, ga ƴan uwanki sun zo kuma shine zaki koma ciki”

Yaya Khalil who's tired of hearing ƴan uwanki ya ce “Hajjaty Ni ban ma gane Zahrahr taki ba, sai wani sunkuyar da kai take kamar mu ɗin sirkanta ne.”

Dariya suka yi baki dayansu, Ita dai Zahrah ta kosa ne amma haka ta dawo ta samu wuri a kasa ta zauna yayin da duk wani motsin ta yake kan idonsa.

Murmushi Hajjaty tayi sai kuma ta hade rai alamar she wanna say something important.
“Yanzu Halilu wai baka san Zahrah'u na ba kake nufi?, Dama shi wancan kam ba a magana” kai yaya Khalil ya gyada yana maida kallonsa ga Zahrah wacce ke zaune ƙasa.
“Da gaske Hajjaty ban san ta ba”

“Gaskiya ne, ba lallai ku san ta ba dama”
Ya Qasim ya faɗa yana kallon su duka biyun sai kuma ya ce
“To Hajjaty sai ki musu bayani amma ya kamata a ci tararsu.”

“Haba Yaya na Allah (kamar yadda suke kiransa su biyun) ka sa baki Hajjaty ta sassauta mana.”

Dariya Hajjaty tayi sannan ta ce “Ai babu sassauci tunda baku san shalelen jikanya ta ba, yau babu ku a girki na, kai wanda yayi muku ma ba zan baku ba, Qasim In ka tashi tafiya zan baka Gurasa ka wuce da ita.”

Da sauri kuwa yaya Qasim ya amsa da to.
Ba shiri Yaya Khalil ya sauko har kasa yana faɗin “Haba Hajjaty, ai babu wannan magana, ke Zahrah je ki jera mana gurasar a dining”

Mikewa Zahrah tayi tana nufin zuwa ta jera ta tsinkayi muryarsa da tun shigowar ta bata ji ya ce komai ba tun bayan cewa ta saka mishi zoɓon. Cikin ranta tana kara tabbatar da zancen Nasreen.

“Idan kin jera, ki ajiye sauran a kitchen anjima zan sa ki haɗa min shi” daga haka kuma ya make kamar ba shi yayi maganar ba, ita kam Zahrah kadan ne ma ya hana ta dariya saboda yadda taga yayi maganar yana wani shan kamshi kuma ya make kamar ba shi ba.
“He's damn amazing” ta faɗa cikin ranta.

Hajjaty ne ta dakatar da ita da faɗin “Koma Zahrah, ai hukunci na yanke musu” Zahrah sai ta koma ta zauna tare da daura kanta a cinyar Hajjatyn tana jiran ganin karshen wannan drama ta su Hajjaty.
Cikin ranta kuma tana yaba yadda suke mu'amalarsu da juna, abun ya matuƙar burge ta ya kuma kara karfafa mata guiwa kan ƙudirinta.

*React and comment please, yau fa In ba a gwangwaje Ni da reactions ba zan daina update gaba-daya sai kuma kun ji Ni, ah to , Ina matuƙar son ku my esteem fans da yawa da yawa din nan 💔🦋*

[12/24, 6:57 PM] Diamond Bhatool:

*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

https://www.facebook.com/profile.php?id=61570606515077

*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_

_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 1️⃣0️⃣

_Not edited_

                                  ﷽

Hajjaty ta ce “Babu abun da ya shalle nikam, ba dai Wai ba ku San Zahrah'u na ba ku ka ce?” hmm” sai Kuma ta yi shiru.
Yaya Khalil da ya kosa da son sanin wace ce wannan Zahrahr ya sa ya ɗan kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce “To Hajjaty ki faɗa Mana please”
Sosai Zahrah ta so darawa sai da babu dama musamman yadda wannan sarkin izza ya haɗe girar sama da ƙasa dhi ala Dole bai son raini.

Gyara murya Alhaji Baba ya yi sannan ya ce “To ni bari na yi magana tunda ita ba faɗa muku za ta yi ba...”
Kafin ya ƙarasa Yaya Khalil ya katse shi da “Yauwa Tsoho Mai ran ƙarfe, Allah ya ja kwana.”
Cikin ran sa ya amsa da Amin sannan ya ce “Idan ba ku mance ba akwai yarinyar mu Madina wacce ba zan ce ɗayanku ya San ta ba sabisa rasa ta da muka yi” sai ya ɗan ja numfashi ya ce “A taƙaitace dai wannan Zahrahr ɗiyarta ce, Amma ita a halin yanzu ba a San yadda ta ke ba”

Murmushi Yaya Khalil yayi yayin da Master Kuma ya dake kamar bai ji me ake magana a Kai ba Amma can ƙasan ransa ya tausayawa yarinyar ga Kuma su Hajjaty da ke tsananin kewar ɗiyarsu musamman da ta kasance tilon ya mace. Kallonsa ya Kai ga wurin da ta ke ita kuma lokacin ta sa hannu ta goge hawaye. Lokaci ɗaya tausayin yarinyar ya lulluɓe shi and he's eager to know how all these happened.
Chapter 13 · 0% Book details